*A RASHIN SANI*...
*Page 23*
Dr Ahmed dasauri yafito jallabiyya ce kadai jikin sa kusan karo yakai ma Ummi dake kokarin Shigowa "subhanallah! lafiya Ahmed meke faruwa ne?" Wani Abu ne yafaru Asibiti Ummi" bai tsaya jin Abinda zata fada ba ya fita daga gidan binshi tayi da kallo yadda yarikice "dubi yadda ya rikece sai kace nike Asibiti ko mahaifin sa" tab'e baki tayi tare da shigewa ciki' Dasauri Dr Ahmed ya shiga motar sa Ya nufi Asibiti ko gyararen parking baiyi ba ya nufi ciki iske Inna Uwani yayi kusada Zainab yayi ta tafito taki fitowa sai kukan datake ta yi, "Mommy fito daga nan" noke kai tayi "aaaa Aunty duka.." ai ita tace kifito ita taba ni sako tace inzo in fad'a miki".. dakyar Dr Ahmed yasamu Zainab ta fito daga gun tana d'angyasa Kafa babu inda ya zame da ita sai wani Imagancy room ya kwantar da ita tare da yimata Alluran rage radadi hade dana bacci nan da nan bacci ya d'auke Zainab tanayi tana ajiyar zuciya domin ba karamin Azaba ta d'add'ana na..cikin tausayi Dr Ahmed ke kallon ta tare matsanancin haushin surraya Abinda zaiyi mata kawai yake hararowa kallon Inna Uwani yayi "Inna ki kula da ita zan dawo yanzu" "Toh yallabai Insha Allahu "... fita yayi a fusace ya shiga mota...har saida yazo kofar gidan su sannan ya fiddo wayar sa zai kira ta
"Wai kai Alhaji Labaran Kullum kana nanike dani ko gajiya bakayi kamar dai baka da matan Aure ne A gida ni Gaskiya kam nafara gajiya da irin wannan jarabar taka Nikam..tsoho ne A kalla Zai kai 65 Years jawo ta yayi "Haba sury Baby Kinsan ke d'in ce kullum qara sugar kike bana gajiya dake ne karkimin rowar kanki mana duk Abinda kikeso zan baki.." tab'e baki tayi wayar ta ce taji tayi tsuwwa special ringtone din tasami shi taji dasauri ta diro daga bisa gadon ta d'auki wayar "Hello Baby." Ganinan kofar gidanku"..haka kawai yafada ya datse wayar..dasauri Surry ta zura rigar ta Alh labaran yana kallon ta.. d'aukar jakar zatayi dasauri ya riko ta "surry ina kike niyyar tafiya ne?" Hararar shi tayi "Mijina ya kirani" bani da Lokacin kowa yanzu in ba nashi Next time".. daga haka ta dauki jakar ta da mayafin ta ko kallon shi bata sake yi ba, tsaki yaja tare da dauko wayar shi ya kira wadda zata huce mishi haushi..Surayya motar ta tashiga dake harabar hotel din a guje ta fita..
****
Zaune take a palour sai kace ba yar gayun maiji da kanta ba tagumi take ga tarin Abinci gabanta Amma ko kallon shi batayi wani photon kato wadda ke ciki ta qura ma ido hawaye ke zuba Amma bata su take ba,, shigowa yayi girgiza kai yayi tare da nufo ta har yatsaya kusa da ita bata sani dafa kafadar ta yayi "Maryamu".. juyowa tayi Fuskar ta shabe shabe da hawaye Fadawa tayi kirjin sa "Malam Ina kewar Zainab jikina har yanzu yaki bani Zainab ta mutu inajin Zainab tana raye" kara rungume ta jikin sa yayi "haba Maryamu wace irin Nasiha ce Baffah bai miki kinki jingina da komai ne ki fawwala ma Al'amarin sa, in lokacin Zainab yayi Zaki hana Ubangiji karbar ran ta ne, haba Maryamu meyasa kike jayyya da ubangiji ne"?"Bana jayyya da ubangiji Malam kasani Zainab itace daya tal gareni Ina tunanin zata haifamin zuriar da zasu ninkata ya goge tabon dake tare dani yanzu babu Zainab shikenan kai Matar ka komin daren dadewa zata iya haifa maka wasu yaran zaka kuma Auren wasu su haifa maka yara nifa nifa matsanancin kuka tasa tare da barin wajen da gudu..dasauri yabi bayan ta yana kiran ta...
***
Kallon Agogon hannun sa yayi tsaki tare kara kallon gate d'in gidan karar mota yaji waigowa yayi yaga tafito dauke fuskar sa yayi yana karajin wata tsanar ta, "Baby sorry...kana ta jira na ko na d'an fita ne ban San zak..." dakatar da ita yayi da hannu "ke wace irin muguwa ce Azzaluma ni ba jahili ne marar ilimi kamar ki ba Amma duk ranan da kika kuskure ki kara zuwa Asibiti kikayi ma Mommy haka wallahi tallahi zaki san tanada gata ba Kadan ba".. daga hakan ya shiga mota yabar ta tsaye gun tamkar gunki sai dataji Kurar mota sannan ta dawo hayyacin ta kuka tasa tamkar wadda mahaifin ta yarasu..ta nufi cikin gida dasauri ta tarbe ta "Lafiya Auta meyafaru shalele waya tabaki ne A gari nan".. Mommy Ahmed ne".. tsaki tayi "wai ke don uban ki baki hakura da Ahmed d'in nan ga masu son ki nan da yawa wadda sukafishi komai da Komai, "wallahi Mommy Shi nakeso inbaka haka zaki rasani kuma sai fadi kike kina son farin ciki na har yanzu Ahmed yaki dawowa karkarshin iko na yaki nuna mun kauna sai tsana kawai.." dafa kafadar ta tayi "Kiyi hakuri kinji Shalele tsaya ki gani".. dauko waya tayi tasa handsfree "Hello Hajiya".. "Kinga Hajiya Aysha ba wannan zance na kiraki ba Kisameni A gida gobe kawai"... Angama ranki yadade..." daga hakan ta kashe wayar ta kallon Surayya tayi karki damu kamar anyi Auren ki da Ahmed Angama"..
Yauwa Mommy na I love you"
Luv you too baby Farin cikin ki ai shine nawa"...*After one week*
Zainab ta warware sosai saboda kula da ita da Dr Ahmed ya dingayi sosai bashi nesa da ita har ta warware baki daya sanye take da wasu Pakistan riga da wando duk sune kayan ta da Dr Ahmed ke siyo mata yasan Zane baizai d'auro gareta ba Inna Uwani tayi mata kitso guda biyu ta raba mata shi ya safko har kafadar ta guje guje suke da Nadiya (Kawarta wadda take kira da diyalle)Dr Ahmed yana binsu yana musu video Sunata nishadin su, Zainab ce ta rugo da gudu ta biyo ta wata hanya duk dr Ahmed yana biye da ita,.... ZAINAB! yaji ankira sunan ta itakam tsayawa tayi cak! Dr Ahmed dasauri yakai idon sa ga mutum da ya ambaci sunan nan........
Lazy writer 😥
Saboda karatowar Ramadan..insha Allahu zanyi kokarin kamallah indai kukabani kwarin gwiwa dayin comments har sau 2 zan iya muku post Nagode
YOU ARE READING
A RASHIN SANI..
Mystery / ThrillerA rashin sani da jin rashin maganar iyayenta ta zabeshi A matsayin masoyin gaskiya, A rashin sani sanadiyar shi tayi rayuwa A gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya mai tabin hankali, A rashin wadda ta fifita ashe dan fashi ne..