*A RASHIN SANI*...
*Page 22*
*SURRAYYA*
Surrayya D'iyar wani hamshakin dan siyasa ce wadda gwammanati ke damawa dashi,Matar sa daya Hajiya Kulsum Mace mai masifar kishi, tuni ta mallake mijin ta Alhaji Hamza Naira sai Abinda tace yakeyi duk matar da yayi ba ta zama sai Hajiya kulsum ta koreta,..yaran 6 shida Surayya itace Auta..rayuwar gidan su surayya irin ta yan boko da wayewa ta ratsa su kowa yancin kan sa yake ba ruwan kowa da shigar harkar kowa Had'uwar Surayya da Ahmed kuwa sun hade a a gidan wani abokin Ahmed da matar shi ta haihu sunje gani Jariri ita kuma matar qawar ta ce itama taje ganin jaririi tunda ta kyalla ido taganshi taji duniya babu namijin da takeso kamar shi, bayan tafiyar su Ahmed tambayar Abokin nasa kawai tayi waye shi wajen sa Abokin sa ne yafada mata tare da bata dan takaikacen tarihin sa, tunda ga nan surayya ta fara bibiyar Ahmed, Amma shi ko kulata baiyi daganan ta billo ta b'angaren mahaifiyar shi Abu nema yasamu Ummi ta ja Surayya a jikin ta, surayya tunda ta lura da Ummi nada son abun duniya kuwa ta dinga yi mata hidima kamar bataso har da Abba, tunda ya nuna ma Ummi bacin rai batakara nufo shi ba domin duk yadda take abinda takeso tana gudun bacin ran sa in ya baci domin bataji da dadi, inda surayya harda Mommyn ta hada ummi da ita suna waya inda ummi har gidan su surayya taje taga katafaren gidan su da kuma dumbin dukiyar dasuke da ita tasha Alwashin kuma Ahmed bashi da mata sai Surayya, inda ita kuma surayya itama take son Ahmed..inda kuma takuma bushashar ta da wasu mazan A waje Ahmed ne ta tsayar A matsayin mijin dazata Aura, inda shi kuma bai taba jin ko d'igon Son ta ba cikin zuciyar sa duk irin Abinda zaiyi mata ta kyaleshi ta fita rayuwar sa takiyi sai bibiyar sa datake, Kuma yasan datana bin wasu mazaa Awaje..Amma Ummin sa zata fada bashi da mata sai Surayya,
*Bayan watshidda*
kwanaki suna ta tafiya har ya zuwa tsawon wata shidda Zainab tana gidan masu tabin hankali inda Dr Ahmed yazame mata komai nata shakuwa ce sosai tsakanin su ko bashi da aiki zai shigo asibitin ya dinga d'ebe mata kewa shiyasa babu wdda ta saki jiki kamar shi sai metirum d'in dake kula dasu Inna uwani, dakuma wata mai lalurar zainab zasu kusan shekaru d'aya, .. yanzu ma guje gujen su suke cikin d'akin inna uwani tana gefe tana jan carbi gyangyand'i yana d'an dibar ta, taji andaka wata tsawa Hatta su Zainab dake guje guje sai da suka juyo suka tsaya cak!
YOU ARE READING
A RASHIN SANI..
Mystery / ThrillerA rashin sani da jin rashin maganar iyayenta ta zabeshi A matsayin masoyin gaskiya, A rashin sani sanadiyar shi tayi rayuwa A gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya mai tabin hankali, A rashin wadda ta fifita ashe dan fashi ne..