ABDUL-HAMEED 2

75 1 0
                                    

*Paid book*
200 naira only

*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_


©️ *H W A*

Wattpad:NEIRNAHDISO

*Top Ten! Takun Haske Batch B*

*Free Page*

Na Kudine ki Bada 1000 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku


2

_______________________

Muje zuwa TAFIYAR YANZU MUKA FARA.....

Wani k'allar k'ifta idanu tashigayi daga bisa kuma ta lumshe idanun ta maganganun sa na tsarga mata cikin ranta tabbas tasan tayi sa'ar masoyi wanda kudibazai taba samar mata shiba.

Sautin mursa ce ta kara riketa ta " Amina ina miki son da bazan iya kwatanta miki ba amma kisani kowanene yatabaki to tabbas bazanyi shiru ba kiyi hakuri da dukkan furucin mutane dangani dani nasan dayawa suna tsokanarki."

Murmushi amina tayi sannan ta matso tare da mik'a masa k'wanon dak'e hannunta a hank'ali ta lank'wasar da k'anta " DanAllah karkace ka k'oshi Allah dak'aina nayi maka kuma kuma nasan bakaci abinci ba kaji please taja kalmar karshen."

Idanu ya zuba mata na wasu lokutan sannan ya karba tare da ambatar " Allah yayi miki albarka yanzu ki koma gida kada inna ta nemiki, inaso ki maida hankalinki sosai a karatunki don ni kinga inada buri naga kin cigaba da karatu."

" To inshaaAllah zankara yaushe zakazo ka gaida malam ?."

" InshaaAllahu zanzo daga nan bai kara cewa komai ba."

Har ta tashi tabar gurin yana k'allon ta shima shiga gida yayi da sallamar sa.

" wa'alaikissalam babana bana hanaka daukar abu mai nauyi da hannun ba? Yanaga kamar kamar takara sak'i? Lokaci guda goggo ta gigice zo ka zauna nagani."

Sarai yasan halin goggo akan kafarsa ko hannunsa zata iya kasa bacci don haka yayi saurin yimata murmushi tare da fadin " Goggota bata komai kawai nagaji ne kuma hannuna ai baimin zafi shiyasa narike kwanon a hannun, danAllah kada ki damu kanki."

" DanAllah abdul-hameed kadaina boyemin ciwonka so kake zuciyata ta samu matsala ne dazu dan mari yacemin yaganka a shagon chemist kuma nasan abunda zai kaika can bakarami baniba."

" Goggota kada kiyi fushi dani please ni ko batamin rai banso naga kinayimin, banason ina daga miki hankali amma kafar nan yau sati 2 kenan kullum bana bacci kuma...

Bai karasa ba baffa yashigo yace " kuma wallahi wallahi abdulhameed ranka zai baci duk ranar dana kara ganinka a chemist akan ai maka allura, kai da ake maka fatan warkewa gaba ina kai ina allura kada na kuma ji."

" kayi hakuri baffa bazan kara ba InshaaAllahu daman kafar tadan dameni amma na karbi magunguna ma yanzu tadan rage zugi."

" To Allah yakara sauki cewar baffa". Baffa kuwa harara tabi abdul hameed dashi ita a lallai tayi fushi. Miko mata kwanan yayi yana 'yar dariya " karbi wannan goggota bazan karaba amina takawomin." Baffa ne yajiyo ya kallesu don gabadaya tausayin yaron nasa yakeyi don wannan karan shima babu yadda ya iya, kuma ya tabbatar idan dan marka yafara neman amina mahaifiyar ta sai ta bashi. Yadda yaketa murmushi goggo tana tsokanarsa akan aminar shine zai tabbatar maka irin kaunar da yakeyi mata.

"Abdul hameed ". yaji baffa ya kirasa

"Naam baffa."

" Yaushe ne tafiya bautar kasar taka?."

" ai baffa sai zuwa dare zanje na duba ina suka kaini."

" To madallah Allah dai yasa kasamu kusa banason nisan nan."

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now