ABDUL-HAMEED 16

32 1 0
                                    

Paid book


*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_

Wattpad:-neirnah diso

©️ *H W A*

*TOP TEN! TAKUN HASKE BATCH B*

NA KUDINE KI BADA 1000 KI CAFKI GARABASAR NOVEL BAKWAI DA PROGRAM UKU....



FREE PAGE

16

Kai yaya sunanka cewar alhaji hadi? " ibrahim sunana ranka yadade". Naji ancemin yaron nan da nafisa takeso dan uwan kane ko? " " eh dan'uwana ne ." " To madallah inaso kakawomin shi zan baka tuk'wici mai tsoka, inaso yana zuwa a daura aurensa da nafisa kafin yakarso zan tanadi Malamai in yaso ko daga bayan an daurane sai asanar da waliyanku ko? " mama ce tace haba ranka yadade ina akataba wannan lamari? Shi yaron yace yanasonta ne kuma fa shi kansa yaron banida tabbacin yana sonta." Dakatar da'ita yayi ta hanyar daga mata hannu, " babu ruwan da so ko kaunarsa inada kudi dan haka inada makullin zuciyarsa inada kaunarsa, kinfi kowa sanin cewa yaran takalawan nan basu bukatar komai sama da kudi, to kayi masa albishir ibrahim zan basa gida mota aiki sannan zan wadatashi da kudi nidai fatana shine yakasance mijin nafisa." Nafisa dake kusa da mahaifin nata ne ta rungumeshi tare da fadin " You're such amazing dad nagode dad indai ka mallakamin Abdul hameed to tabbas ka gamayimin komai na duniyar nan kowanne kalar jindadi kabani takara hugging dinsa tana dariya." Dad ne ya shafa kanta yace " anything for you doter yanzu to ji kici abinci ko? " mikewa tayi ta bar gurin, mama ce tace " nidai bana fatan irin wannan miji ga nafisa nafison wanda zai sota yakuma kaunace ta badan kudin mahaifinta ba." " dad ne yatashi yace yarage naki kuma wannan ba matsalata bace."

Tunda ibrahim yak'amo hanya yake tunani kala kala, tabbas wannan maganar direct zuwa dady zai kaita in bahaka ba wannan miskilin yaron bazai kulashi ba, ga inteesar ma da alama tafara rikirkicewa akan abdul-hameed shiyama rasa yadda zaiyi, ahaka yakaraso har cikin gidan yana danno mota yatarar da abdul-hameed da alama inteesar ta cikashi da surutu don littafi ne ma a hannunsa.

Ibrahim ne ya sauka amota yana mai kallon abdul-hameed cikin yanayi na damuwa yace " Ke ak'u kin damesa wannan hira haka? " cikin bazata da rashin tsammani abdul-hameed yace " me ruwanka ko kai take bawa sannan yayi murmushi." " ahh lallai yau kuma akan inteesar an gwaleni lallai yarinyar nan wato har kinsa yafara sabawa dake ko?" " Inteesar ce tasa dariya tace to ya son ranka bro?" Kai yaya ibrahim kazo inji dady cewar nawal data cakare cikin wata atampha da skirt amma gabadaya sun matseta sai wani karamin veils dake kafadarta. inteesar ce tace " gaskiya nawal baki da kunya harda cewa kai? " To me ruwanki? Me yadameki? Naga yayana ne?" Ibrahim ne yace dallah mai aljanu matsa kada kikara cemin yayanki in bahaka ba to... tsaki taja itama tare da murguda baki sannan taje gefen motarsa ta tsaya, mikewa yayi gurin dady da sallama yashiga sannan yasamu guri yazauna " barkanku da rana" barka kadai suka amsa, daman dady inason magana dakai ne akan abdul-hameed " To ina sauraronka lafiya ? " dama akan maganar wata yarinya ce da yagani yana so to shine shine.." mumy ce tace wacce yarinyace haka? " saurin cewa yayi nafisa yar gidan minister, " ohh ni maryam amma dai abdul-hameed da kokari yake inashi ina yar minister ko kai tafi karfinka ballanta shi dan baffa tasa dariya." Alhaji Muhammad ne yagyara zamansa yace amma dai yaran nan da riga kuke wato abdul-hameed dinne ya aikoka? Inteesar data labe tashigo tace Allah abu zancen brother amma abdul-hameed ko sanin yarinyar baiyiba, ibrahim ne ya dallah mata harara sannan yace " wallahi minister ne ma yakirani da kanshi, mumy ce tagyara zama zuciyar ta tana mai kuna, Alhaji Muhammad ne yace go and called him don dady gaba daya baiji dadin maganar ba saboda shi kadai yasan abunda yake tsarawa amma sai ya kau da zancen, To madallah kai abdul-hameed yanzu baka daukeni matsayin uba ba kenan da bazaka iya takowa kagayamin akan wacce kakeso ba?" Mamaki ne yacika abdul-hameed wacce budurwa kuma cikin murya ta nutsuwa yace " Ni banida wata budurwa dady kuma bana tunanin zanyi wata nan kusa karatu da lafiyata sune agabana, dadyne yayi murmushin jindadi, inda inteesar tafara shashekar kuka abu ne yajiyo yana kallonta menene intee? " abu inason zuwa gurin ummi zanbi yasmeen ko 2days sai nayi" mumy ce tace " kai amma yarinyar nan da rigima kike shine na kuka? " Ibrahim da gabadaya jikinsa ya mutu yaya zaiyi da minister daman yasan abdul-hameed ba mutunci ne dashi ba, muryar dady ce ta katse shi kaje ka kai nawal school kada ta makara sannan banaso kakara tunkarata da wannan maganganun naka na shirme da kanka kamar minister din akasa dariya, " gaskiya dady bazan iya tuki daga ni sai mai aljanun can ba salon ta shakeni? Kuma ..." daka masa tsawa dady yayi mumy kam sai dariya takeyi, can kuma tace to ai sai abokin naka ya raka ka ko?" Inteesar ce tace daga nan abu sai ya ajiyeni nima bari nasa veils dina, kudai zama ready nan da some days zamu tafi.

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now