ABDUL-HAMEED 1

306 6 2
                                    

*Paid book*
200 naira only

*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_


©️ *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Wattpad:NEIRNAHDISO

*Top Ten! Takun Haske Batch B*

*Free Page*

Na Kudine ki Bada 1000 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku


1

_______________________

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Ba k'aramin zafi da radadi maganganun nata sukewa zuciyarsa ba duk da ya k'asance a kwance amma tabbas wannan cin fusk'ar yana k'okarin fin k'arfin sa alamun hawayen dak'e bin k'wancin sa zai tabbatar maka da kuka yak'e.

A yaushe ne mutane zasu daina gujin masu cuta ta musamman tabbas baffansa kullum nace masa bahaka aka haifesa ba amma haka Allah yaso ya gansa daga baya.

Muryar baba ladidi ce ta katse masa tunanin sa. " To wai goggo ince ana dole ne nace ana dole ne ku wasu irin marasa zuciya ne soyayya ce tsakanin abdul hameed da amina bazai taba yihuwa ba wallahi don wallahi diyata bazata taba auren nakashashe ba ko kiso kokarkiso wannan shine zuwana na karshe to naga auren dole ne garesa??? Mutum gashi nan dai wayasani ma ko zai iya aikata abun arzuki in yayi auren don ku kara bincikawa nakasar tasa har cikin...."

" Kinga ya'isa ladidi wannan wani irin cin zarafi ne kuma larurar yarona inaga ba da'ita na haife shi ba daga baya allah ya jarrabeshi? To menene na bakakaken maganganu? Menene makusar abdul hameed ?? Inba kallon kurullaba kokuma yana tafiya kin isa ki gano bashida cikakkiyar lafiya? Kuma maganar aminatu ina rabaki da shiga soyayyar da Allah ya kullata aminatu taganshi ta sanshi kuma tana sonshi menene.."

" Ke goggo iya bakinki wai ku dangin mayu ne nace ko ku mayu ne narantse da Allah in shanyayyen danki bai rabu da yarinyata ba to kuna cikin tashin hankali don wallahi kaf cikin garin nan sai anjimu daku banzaye... reee taja mayafi tafita."

Cikin nutsuwa da kunar rai yafito zuwa tsakar gidan. Goggo ta dago kanta tana kallonsa yadda yake jan kafar tasa a hankali tabbas nakasar abdulhameed in ba lura kayi ba bazaka taba cewa yanada wata larura ta musamman ba. " babana naga bakajin dadi me kuma yafito dakai kaga jibi zaka fara bautar kasar ka dole muyi tattalin lafiyarka asamu agama lafiya."

Murmushi yayi wanda inba mutum uku ba baya taba iyayi agabansu. " Goggota sannu da hutawa daman akwai 'yar maganar da nakeso mu tattauna dake ne dafatan bazan shiga lokacin aikin ki ba.
" Kallon sa tayi tana nazari tabbas Allah yabawa ABDUL_HAMEED nutsuwar da babu abunda zata cewa Allah sai gobe agaresa wannan, aduniya idan akwai farincikin wanda takeson gani to tabbas abdul hameed shiyasa kullum addu'arta Allah yabasa ingantacciyar lafiya yakuma hore musu kudin da za'ayi musa aiki. " babana ai gaba daya lokacina lokacin ka ne ko inda wani farin cikin ne bayan kai? Tayi murmushi tana matsa masa kafarsa, ni wannan hasken naka babana sai nake ganin yayi dau dayawa anya ba shawara ke damunka ba? amma inada wani ragowar magani zan jika maka anjima danAllah kana kula da lafiyar ka wannan aikin dakake fita in banda ka dage nidai ba'ason raina bani ba Ina hannunka ina aikin karfe babana?.

Murmushi yakuma yi sannan yace " goggota ai Allah ke tsarewa, kinga shekarun baffa sunja kyanta ace ni nake daukar hidimar komai ta gidan, kuma wannan makanikan cin yana dan tallafa mana goggo nidai abunda zaki cigaba da yimin shine addu'a ita nake bukata agurin ki kuma kinga tunda bautar kasar nan wani garin zanje shima bazan zauna haka ba zan dinga kokarin neman dan aiki inayi ko.?".
" Allah dai ya inganta maka lafiya babana yashiga lamarin ka maganar me kakeso kayi dani?"..

" goggota banajin dadin yadda kike kara shiga damuwa saboda ne zuciyata tanayi min zafi da radadi ina sauraron duk abunda innar amina tazo tace miki, bazanso ana ja'in ja da mahaifiyata ba goggo ni zan hakura da amina zan sakata alayin sauran matan kawai duk da ita ta babbanta dasu."

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now