ABDUL-HAMEED 6

40 1 0
                                    

*Paid book*

*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_


©️ *H W A*

Wattpad:NEIRNAHDISO

*Top Ten! Takun Haske Batch B*

*Free Page*

Na Kudine ki Bada 1000 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku


PAGE *6*

_______________________

Itama k'uka tasa ta tsugunna tana ambatar danAllah kada k'a tafi abdul-hameed ina sonk'a ina k'aunar ka.

A hankali yajiyo har cikin soron k'afadar ta ya rik'o sannan ya k'alleta yace " amina idan har k'inaso na to inaso k'i k'arbi k'addarar k'i hannu bibbiyu tabbas nasan in babu k'i babu wacce zangani har ta shiga cikin zuciyata,k'e daya zanso cikin duniya,ganinki k'isa hank'alina ya k'wanta,ina yawan jin bugun zuciya, asanad'inki masoyiya ta,tunani nake in babuk'e ina zana sanya raina d'an k'ece k'ike shigar mini har k'uryar zuciya k'i zauna, ba lallai nayi ko budurwa ba, bazan canza hali ba, Nasan amina mai nutsuwa da tarbiya ce to inaso ki tabbatar wa duniya hak'an yanzu shige ki tafi agaban idona Allah yatabbatar muku da zaman lpya."

" Allah yabak'a wacce tafini jarumin jarumai yabak'a wacce zata k'ula dak'ai fiye dani yabak'a wacce zata iya sadauk'ar dak'anta ak'an soyayyar k'a na yarda da kaddara abdul-hameed kuma inshaaAllah zanyiwa iyayena biyayya zanyi musu zan kuma yiwa mijina biyayya ina maka fatan Alk'hairi a rayuwark'a da nasara mara yank'ewa da dauk'aka mai amfani da tsare daga sarki Allah." A hankali tashige tatafi tunda ta isa soron gidansu ta tsaya tayi dan hawayenta sannan tashiga malam tatarar acikin dakinsa nan ma turawa tayi tashiga gurinsa, " baba sannu da hutawa gashi abdul-hameed yabani yace gudunmawar sa". " To madallah Allah yasaka da alkhairi kije ki shirya kayanki dattijo yanata waya." " To baba tace sannan ta mike."

Inna ce ta k'alleta tace " tun dazu dan mark'a na naimank'i fa ina kika shiga ne?"

Ina zuwa inna shine abunda tace k'awai.

Inna ce ta k'alleta dajin abunda ta fada k'ai anya amina ce larai bak'iji abunda yarinyar nan tafada baniba? " Nima nayi mamak'i ko asirin yaron nan ya k'arye ne?" " To wayasani."

Dan marka dake tsaye a kofar gidan kusan awa daya sai k'allon kofar yakeyi yaga ko zata fito aikuwa daga idonsa kenan sukayi ido biyu murmushi ya sakar mata " yau sarauta akeji kenan ko gimbiyata." Da har zatayi masa banza sai kuma ta tuna da lafazin abdul-hameed " Na kiyimasa biyayya kiso shi sama dani aminatu ki inganta rayuwar aurenki wannan shine kaddarar mu". Tsugunnawa tayi har kasa tace " ina yini yaya? Kayi hakuri uzuri yarikeni." Dagota yayi yace " banason kina tsugunnawa gimbiya kinji, yanzu me dame kika shirya nabikin?" " Duk abunda ka shiryamin yayi...

"Goggo ne zantafi kiyimin addu'a danAllah kiyafemin idan na batamiki zan dinga zuwa ko wata watane dan yafimin sauki."

"Abdul-hameed ina rokon Allah ya tsaremin kai kayi hakuri duk inda zaka shiga sannan wannan magungunan naka na hausa ne ka adanasu da zarar jikinka kaga ya motsa kaji, sannan gidan da zaka zauna kayi hakuri kaji, Allah yayi maka albarka zanyi kewa tafara kuka."

" Ameen goggota bari naje baffa yana jirana a tasha."

Har soro sai da ta rakasa,tare dayi masa addu'oi da fatan Alk'hairi.

Abdul-hameed tunda yatawo hanya gabansa ke faduwa komai nasa abun a taimaka masa ne yanzu kuma baisan me zai tarar ba, dole sai ta kofar gidan su amina zai huce tunda a titi suke yatawo hucewa da kayansa idonsa ya sauka akan su, tsayawa yayi yana k'allon su, gaba daya rayuwarsa da'ita abaya ya tuna irin wasa da dariyarsu akwai lokacin da kafarsa tatashi da ciwo kullum sai tazo komai ita take masa, ta dane bayansa tayita tofa masa addu'a, akwai lokacin da take cewa ita lallai zata bashi magani, ciwonta na biyu daya tashi aikin da akayi mata sai da yakasance yana dakin yana mata addu'a akasamu sauki, ko bugewa tayi tata ambatar sunansa. Hawaye ne ya zubo masa saurin yin gaba yayi saboda yanayin raunin zuciyarsa. Dan adaidaita yasamu yakarasa dashi tashar baffa yakira yafito. " kaje kayi zamanka abdul-hameed saura minti 5 sutashi ga wannan dubu 30 ce karike a hannun ka, sannan kaji tsoron Allah duk inda kake idan bama kusa kasani Allah yana k'allon ka, kada kaga wai kai kyakyawa ne kyannan naka ya rudeka agurin wasu bakada kyau kasan wannan ,daga nan so nake ka zarce master's dinki kaji, banason yawan zuwa banki ba ko awata sau 3 ne."

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now