ABDUL-HAMEED 3

48 1 1
                                    

*Paid book*

*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_


©️ *H W A*

Wattpad:NEIRNAHDISO

*Top Ten! Takun Haske Batch B*

*FREE PAGE*

Na Kudine ki Bada 1000 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku


3

_______________________

Ibrahim ne ya k'alli kofar ya zaro idanu! k'ara k'allon k'ofar yayi sai da yaji mumy tasa ihu tana fadin " ataimaketa sannan yayi waje da gudu duk mazan gurin sunyi kan nawal wacce take k'okarin jijjige kofar gate din tana wasu irin gurnani , duk wanda ya nufota to sai ta zubar dashi wani doctor ne yayi ta maza tare da dakko allurar bacci ya soka mata. A Hankali ta sulale ibrahim ya rungumeta suka koma asubutin bayan an shimfid'e ta akan gadon dakin yayi shiru kukan mumy kadai ke tashi.

Ibrahim ne yace" mumy kalli abunda nawal tayifa wallahilazim wannan aljanu ne yaya za'ayi yarinya kai ko k'atotan saurayi bazai iya cire kofar nan ba."

Shiru mumy tayi dan ita gaba daya nutuwarta bata tattare da'ita.

Doctor ne yashigo " yace yanason ganin daya cikin ku."

Mumy da har yanzu bata gama shashikar kukanta ba tace " ibrahim kai jika don ni bana cikin nutsuwa bama gane bayanin nasa zanyi ba."

Fita ibrahim yayi yabi doctor din har offices dinsa yanashiga yabashi hannu suka gaisa.

Doctor ne ya k'alli ibrahim yace" ta taba samun matsala abrain din??"

Ibrahim ne yagyara zama yace " no bata taba ba and this is her first time doing. "

To nidai atawa shawarar ko zaku kaita asubutin brain don ina tunanin tasamu matsalar brain just look at how she broke this door abun ya girgiza kowa da komai."

Ibrahim ne yayi murmushi yace thank you doctor kawai yafita don shina zazzabi ke kokarin rufesa fitarsa ke da wuya yakirawo hajjah awaya ringin daya tayi ta dauka " babban jika ya akayi ne sarkin kawo kara yau kuma waka kawo kara?"

"Hajja babu lafiya nan nawal k'e ta wasu abubuwa da mun kasa ganesu please kisa driver ya kawoki." Bai jira abunda zatace ba kawai yakashe wayar yakoma dakin duk karfin allurar amma sai sukaga nawal din na faman shure shure alamar har ta saket.

" Mumy bari nakira doctor din yakara yimata allurar kinga farkawa zatayi".

" anya ibrahim kanada imani kuwa wacce allura kuma yanzu fa ta hudu sukayi mata aa abarmin yarinya ta huta inajin zazzabin yasaketa kasan shike saka mutum wannan firgicewar da kid'emewa."

" Wani kallo yayiwa mumy wai zazzabi lallaima mumy sai yayi gefe kawai ya zauna yana dafe kansa."

Mumy ce tahada mata shayi ta mika mata kawai binsu takeyi da ido tana wani fizge fizge, tana daukar shayin ko rabin sakan batayi ba ta shanye nan fa mumy da ibrahim suka hau kallon juna.

Ibrahim ne hantar cikinsa ta kada yace " mumy ni wallahi cikina juyawa yakeyi bari naje nadawo." Ko jiyowa baiyi ba yaji mumy tasa kara tana fadin " ibrahim wayoo gashina zanyi fitsari ibrahim zata ciren gashin."
Ai a firgice ibrahim yatawo hantar cikinsa nakadawa da kyar ya kwaci mumy daga hannun nawal ai kamin ya juya yaji an fizgo hannun sa yayi karas ai tuni yace " wayooo nakaryani wayoo hannuna." Hajja da dady da wasu nurses din da sauri suka karaso dakin ibrahim na rikeda hannunsa yana azaba na cinsa nawal kuwa hanyar fita tayi inda dady yarigo ta yashiga tofa mata addua sai kawai bacci yakamata.

Hajja ce tace ko ni yanzu ta karya maka hannu ibrahim amma dai kuma da tsautsayi kuke me yakaiku kusa da'ita.

" Hajja bafa aljanu baniba cewar mumy maleria ce tayi... "

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now