ABDUL-HAMEED 17

87 2 1
                                    

Paid book


*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_

Wattpad:-neirnah diso

©️ *H W A*

*TOP TEN! TAKUN HASKE BATCH B*


LAST FREE PAGE

17
_______________________

Har ya k'arasa bak'in mota tana k'allon sa ta window maganar amina k'awai k'e wad'o mata, 'kema mutuniyar kirki ce'. Wannan kalma itace tayita yawo acikin kanta har malamin yafita batasan ya fita ba, sady ce ta baro gurinta tazo kusa da nawal tace " ke baby nawal ina kikasamo handsome dinnan nidai gaskiya bana ganinsa agidanku wallahi yayi min, mutum so gentle and calm, please kawata kibani number dinsa i love him." Tunda sady tafara magana nawal ta zuba mata idanu har sai data ga ta kammala sannan ta dubeta tace " yanada aure to." " danAllah dagaske to ni sai nazo a tabiyu please kawata do this for me." Murmushi ne ya subucewa nawal da sai da dimple dinta ya loba tace " ai ta biyun yake kokarin karawa" sannan ta tashi tayi hanyar waje, tsaki sady tayi tace " zan laluba nasan ko wanene." Direct gurin shugaban bangarensu ta nufa tana zuwa tayi knocking din kofar har ta zura kai sai kuma tayi sallama ta shigo tunda tashigo yakeyi mata wani mayataccen kallo, gaba daya nutsuwarsa tana kokarin barinsa tabbas dole yajewa yarinyar nan," sir gani jiya ance na sameka a offices". Tasowa yayi gurinta yace " have a st" zama tayi batare da nuna wata damuwar ta ba ita dai kawai ta tsani malamin ko dan yanayin budewar idonsa, gyara zama yayi tare da matso da kujerar kusa da'ita wani danyen k'allo yakeyi mata mai cike da nuna kwalafuci cikin wata murya tanuna rashin da'a yace " nasan kinaso ace kina fita da sakamoko me kyau ko? " " yes inaso sir". " Don haka sai kinsaki jiki dani kin kuma yarda dani inaso kuma kina kashemin kishirwata nasan dai ke ba bakuwa bace ba a wannan harka, yana kokarin taba mata breast tayi saurin tashi, " idan tunanin ka yana nuna maka ni yar iska ce to tabbas ya yaudareke kuma kujera sakamako,jarabawar ta shiga aljannah ce?? Eh? To menene aciki don ka wadar dani, wallahi wallahi dana aikata abunda kake bukata gwara na mutu babu karatun banza mara mutunci azzalumai masu lallata yaran mutane kuma wallahi wallahi kakara gigin yimun makamanciyar maganar nan kaga wayata nayi recording din duk maganganun ka kasani sai na yadashi ko'ina kowa yaji, matanku suna gida kuna cin amanarsu kuna cutar yaranku, tir da masu irin dabi'ark'a." Tunda tafita take jan tsaki, har da hawayen ta, kowa ya maidani yar iska kowa yararemo shararsa kai na yake saukewa, wallahi zama da mutanan banza ma baiyi ba InshaaAllahu sai na canza rayuwata gaba daya, har tazo inda wata salihar yarinyar ajinsu take zama wato Ameera, "sannu da hutawa amira". Murmushi yarinyar tayi tace " nawal ko?" " lah ashe kin iya sunana please inaso muzama kawaye, ina son yadda kike kame jikinki komai naki daban da namu." Murmushi amira tayi sannan tasamu ta nuna mata guri ta zauna, sunata hira nawal na cikata da surutu taga sady abida duk sun nufota, sady tun kan ta karaso tace " ke nawal me kikeyi a gurin bulun bulun uwar hijjabi ina munafukar ajin mu mekikeyi agurinta??" " menene damuwarki don nazauna agurinta??eh nutsuwa muka fita ko kamun kai kinga sady in zamu gyara rayuwar mu mu gyara kowa sai kallon mutanen banza yakeyi mana kowa bashida buri sama ya sokemu da 'yan iska nidai wallahi kalmar nan ta'isheni.

Ni ba 'yar iska ba adinga jifana da kalmar" " inji ubanwa yace miki ba 'yar ki iska ba kujimin yarinyar da har club muke zuwa shine zakicemin ke ba 'yar iska ba ko zaki rantse baki taba sanin d'a namiji bani?? Aikin banza da wofi." " ai wallahi karya kikeyi sady inada tabbacin ko fahad bai taba tab'ani ba ballantana wani dan iska, club din da muke zuwa kin taba ganina nasha ko taba ce kokuma bayan rawa kinga nayi wani abun?" " sady ce taji haushi kawai ta kira fahad bugu daya kuwa ya dauka " love ya'akayi?" Ai k'an nawal ne ya k'usan fashewa love wato cin amanarta sukeyi soyayya sukeyi." " wannan jakar yarinyar ce tace min wai baka taba sanin taba saboda tsabagen ta mai dani yar'iska," " Sani nawa sadyna ai ko last week sai da mukasha dadin mu tare." " munafuki makaryaci Allah ya'isa banyafe maka ba mugu tasa kuka" Amira ce taja hannunta domin su bar gurin taga mutane suna kallonsu, " wallahilazim natsaneki sadiya nayi danasanin saninki kuma Allah ya'isana lallatamin rayuwa da kikayi". tsaki sadiya tayi tace " can dai yar gidan marowata me kawancen namu yataba min, naga nayi nayi dake kifada harkarmu kinki to me zai dameni na yardake jaka kawai wacce ko izu daya bata'iya ba, gwani na'iya izu uku."

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now