ABDUL-HAMEED 11

37 1 0
                                    

Paid book


*ABDUL-HAMEED*

_NA NANA DISO_

Wattpad:-neirnah diso

©️ *H W A*

*TOP TEN! TAKUN HASKE BATCH B*

NA KUDINE KI BADA 1000 KI CAFKI GARABASAR NOVEL BAKWAI DA PROGRAM UKU....



FREE PAGE

11

_______________________

Dady ne ya fizge belt din hannun ibrahim zabgawa nawal yayi wacce batasan sanda ta firgice ta shiga sosa bayanta wayarta ma ta yar da'ita ,wata k'alar k'ara datayi tare da gigicewa da ķidemewa tana neman agaji, yadda dady ya yashiga shaud'a mata zai tabbatar maka da cewa ransa ya baci, batasan sanda ta rungume abdul hameed ba tana ambatan danAllah ka ceceni wayoo zasu k'asheni,,Dady danAllah k'ayi hakuri wayoo bayana,mumyna ki taimak'eni, wani k'alar fizga dady yayi mata ajik'in abdul-hameed, sannan ya cigaba da shauda mata cik'in firgicewa tashiga ihu tana wani irin zabura, mummy dak'e kuka reeehh tak'araso k'usa da hajja tace danAllah k'iyi masa magana k'ada ya k'ashe min yarinya hajja ak'an Nak'ashashen yaron nan zai illatamin yarinya nan ta cigaba da kuka.." hajjah ce ta k'auda k'anta duk da irin duk'an k'awo wuk'an da dady yak'e mata batace komai bama sai tayi kokarin fita daga shashin, Abdul-hameed da k'ansa k'e sarawa ga wani irin zugi da k'afarsa tak'eyi yanada tabbacin sai yayi jinya ahaka ya daddafa ya tashi, jiyayi k'ansa ya sara cik'in wata iriyar murya mai rauni da tausayi yace " Dady kayi hakuri bazata kuma ba kuma ba laifinta baniba laifi nane da na zaunar musu a palour danAllah ka barta haka". Dady da kansa k'e sarawa saboda yanayin wata murya dayaji abdul hameed yayi ne yasa shi dago idonsa yana bin abdul hameed da k'allo tabbas yanayin muryarsa ce amma kuma sanyin na sumbula ne wani irin soyyayyar abdul-hameed ne yaji yashige sa haka ya dinga kallon sa har yabar palour yana jan kafarshi ibrahim ma binsa yayi suk'a fita ran kowa babu dadi, dady ne yajiyo kan nawal tare da dak'a mata tsawa yace " bani wayoyinki,bani mukulin motarki,sannan kibani system dinki." "Dadyna please dady am sorry please dady tasa masa kuka." Yadda zuciyarsa tafara yimasa rauni ne yasashi kara daka mata tsawa wacce cikin mintuna uku har ta firgice ta hado masa duk abunda ya buk'ata tana kuka kuma jikinta duk ya kumburo, " daga yau sai yau babuk'e babu fita ke daya duk inda zakije to ki tabbatar driver ne ya kaiki ke makaranta kadai na amince idan kuma kika saba maganata to ki kuka da kanki, da safe kije kibawa abdul-hameed hakuri ko bakini ba?" " Am sorry dady zanje am sorry please dadyna." Kayan ya k'washe sannan yabar part din.

Mumy kuwa tunda ta shiga dak'inta take kuka kuma tayi alwashin sai tasaka abdul-hameed acikin masifar da duk danginsa bazasu iya fitar dashi ba, wayarta tajawo sannan ta dannah wayar mahaifiyar ta wato hajiya party bugu biyu ta dauka tana mai fadin " mum nawal ykke." Kuka mumy tasaka sannan ta k'washe komai ta gayawa mahaifiyar ta, harda karya da gaskiya. " maryam gaskiya anan bazan taba goyan bayanki ba inada tabbacin yanzu kinkusa 45 ko? Amma kuma narasa gani kanki, nawal yakamata ace kunbata tarbiya tagari saboda macece ita yanzu hatta ni nawal ban isa ta tako inda nake ba, yan'uwana kuwa kowanne bata ganinshi da gashi ba gaisuwa ba mutuntawa, ga budewar ido to tayaya mahaifin ta bazai hukunta ta ba? Saura ki dauki wannan gabar mara amfani, hajja tasamu yadda takeso kin dai san basonki takeyi ba dama kadan take jira ta fegeki agidan duk da mun riga mun mamaye gida, nawal kuma Mikikeso yayi mata sama da haka, Sannan maganar bak'o dakike magana ba sai nayimiki bayanin yadda zaki rabashi da gidan ba in bahaka ba mallake ku zaiyi har ke kinsan talaka bai iya samun guri ba." Murmushi kawai mumy tayi tare da kashe wayar batare da tace komai ba sannan tafita zuwa dak'in nawal kuka sosai ta tarar da'ita tanayi zama tayi kusa da'ita yare da fadin " come and hug your mum babyna oyaa come" nawal ce tayi saurin rungumeta tana fadin mumy dady yadaina sona yadaina kauna ta, " never say that nawal kinji babanki yana sonki wannan bak'on ne dai yashiga tsakanin ku dan haka inaso ki tayani yakin da zamuyi yabar gidan nan kinji. To mumy pls kibani wayarki nakira sady munada party anjima danAllah kirufamin asiri kada dady yasan bana nan kinji mumyna, kallonta tayi kamar tace a'a sai kuma tayi shiru tace tohm baki damuwa daman kinsan babu mai gadi yanzu."

ABDUL-HAMEED Where stories live. Discover now