*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
https://chat.whatsapp.com/HFVRd4aXG6A8v3OngGn29A
1&2
Manyan motoci ne a jere sun yi jerin gwano kala-kala, idan ka ƙare musu kallo kusan kalolin motar launi biyu ne akwai launi farare da baƙaƙe. Abokan ango ne tsaitsaye kusan kowanne yana jiran ƴan matan da ya sauke don mayar da su gida, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin farincikin taya abokinsu murnar aure.
Gidan babba ne amma plat ne cike yake da kayan more rayuwa, ya sha ƙyalƙyali da hasken ƙan lantarki. Kana ƙare wa gidan kallo za ka fahimci dukiya ta samu makwanci a wurin, duba da irin ɗimbin dukiyar da aka narka a ciki.
"To Zarah kin ga dai kin samu gida irin wanda kowacce ƴa mace take fata, ki yi biyayya ga mijinki ku zauna lafiya, shi zaman aure ɗan haƙuri ne yi na yi bari na bari..." Wata Dattijuwa da take kusa da Amarya Zarah ta riƙa yi mata nasihar zaman aure, ƴan matan da ke tsaitsaye sai kalle-kalle suke yi kowacce tana ayyana ina ma gidanta ne. Matan auren cikin su mafi yawa suna raya Allah ya hore wa mazajensu suma daƙara musu kamarsa, wasu daga cikin iyaye kuma na fatan suma Allah ya bawa nasu ƴaƴa irin wannan gida.
Zarah bata furta komai ba kasancewar kanta na cikin mayafi, har mutanen da suke cikin gidan suka watse sakamakon abokan Ango sai zabga horn suke yi. Ɗakin Zarah ya rage daga ita sai ƙawayenta uku, a hankali ta zame mayafinta tana ƙare wa ɗakin kallo. Amma kana ƙare wa fuskarta kallo za ka fahimci akwai ɓacin rai a tattare da ita, Lubna da ke gefe ta ce: "Zarah ya dai na ga har yanzu ba ki da walwala ko dai akan maganar nan ne?"
Dogon tsaki Zarah ta yi ta furta, "Lubna an yi min adalci kenan? Ace daren farkona wai za a kawo min wata ƴar zaman ɗaki?" Aisha ta taɓe baki tana faɗin, "Ni fa ban ga abin damuwa ba, kuna ɗakinku tana nata. Kuma mutumin nan yana tsananin ƙaunarki, ki dangwali arziki ki bar arziki a mazauninsa." Sadiya ta yi gajeren tsaki tana cewa, "Wallahi Zarah abin haushi gare ki, bakya cin uwar yarinya idan ta ji wuya da ƙafarta za ta gudu.Ki zauna wata ƙanƙanuwar yarinya ta ɓata miki farincikinki, ki zo ki yi biyu babu."
Nan take ƙawayen Zarah suka ci gaba da bata shawarwari na kyau da na banza, lokaci ɗaya ta ware tana farinciki don ta fahimci abin da suke ɗorata a kai.
Ba a jima ba Ango ya ƙaraso shi da abokansa, fito wa ya yi daga motar abokinsa Sani. Bayan motar ya buɗe Walida na zaune tana ƴan kalle-kalle, tana ganin ya buɗe mata ta yi masa murmushi. Hannunta ya kama ya ce, "Fito mun zo gida." Wani Abokinsa Yunusa da ke gefe ya ce,
"Mutumina ba ka so cin amarci ba, haka kawai ranar aurenka ka ɗauko yarinya yoo ko ƴar cikinka ce ai ka kaita ajiya." Khalid ango ya yi dariya ya ce, "Ku dai kuka sani kanku ake ji." Cikin raha abokansa suka raka shi, aka yi barkwancin da aka saba tsakanin Angwaye da Amare, daga ƙarshe aka yi sayen baki ƙawayen amarya da abokan ango suka watse.
Zarah ban da yaƙe babu abin da take yi don kar ta nunawa Khalid bata so zuwan Walida ba, Khalida ya ɗauko manyan ledoji biyu duka cike suke da kaji. Gefe ɗaya katan-katan ɗin lemuka ne sai manyan yegot da kayan ƙwalam da maƙwalashe. Khalid da kansa ya ɗauki Walida ya kaita ɗakinta haɗe da ajiye mata ƙaramar ledarta da ya saya mata kazarta guda ɗaya a ciki, sai lemon jarka da alawoyi. A madadin Khalida ya fita sai ya zauna a gefen gadon, shi kaɗai ya yi jim kamar mai nazari sannan ya furta, "Wannan wacce irin rayuwa ce haka ni ban haifa ba, ba dangin iya ba na baba amma na ƙare da dakon wahala."
Walida da ke gefe ta zuba masa ido ta ce, "Uncle magana kake yi?" Khalid ya wayance da dariyar yaƙe ya ce, "A'a Walida. Cewa na yi Walida ƴar Uncle, yanzu dai ga namanki ko sai da safe za ki ci?" Walida ta leƙa ledar tana juyar da kanta gefe tana shinshine-shinshine ta ce, "Amma dai wannan kazar ba gashin inji ba ce?" Khalid ya zuba mata ido wani takaici ya kama shi, a ɗiƙile ya furta, "Idan bakya ci ki bari sai da safe kya ci."
Khalid na gama maganar ya nufi bakin ƙofa tun bai ƙarasa ba Walida yanƙare baki ta fashe da kuka. Riƙe ƙugu Khalid ya yi a ƙagauce ya dawo murya a shaƙe ya ce, "Me ye kuma?"
Ledar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙaraas alamun taunar ƙashi, da sauri Khalid ya sake buɗe wa sai dai ga mamakinsa yana buɗe ledar ya ga sai taunannun ƙashi, wasu ma an yi dugu-dugu da shi. Cinyoyin kazar ne kawai aka cinye tsokokin ba tare da an tauye ƙashin ba.
Yana shirin yin magana ya ji Walida ta saki ƙatuwar gyatsa sannan ta ce, "Uncle zan sha ruwa." Khalid ya ƙwalalo ido waje ya ce, "Ina kazar cikin ledar?" Walida ta ce, "To ai sai na sha ruwa zan ci." Khalid ya sake bankaɗe ledar ya ce, "Ba yanzu na nuna buɗe kazar har kika ce ba gashin inji ba ce?" Walida ta sake sakin gatsa haɗe da ɗaukan tsinken sakace tana kwakwule haƙoranta.
MEYE HARSASHENKU AKAN WALIDA? 😂
LITTAFIN KYAUTA NE AMMA BAN YI ALƘAWARIN YIN TYPING MAI TSAYI BA SABODA LITTAFIN KUƊIN DA NAKE YI, ZAN YI ƘOƘARIN YIN POSTING KULLIN INSHA ALLAH.🥰
Ummou Aslam Bint Adam🌚
YOU ARE READING
'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT
Short StoryLedar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙa...