*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
🔚🔚🔚🔚🔚
AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS
Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.
ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G
PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.
KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.
Lokacin da su Halifa suka je bakin gate a daidai lokacin Allah ya bawa su Zarah nasarar ficewa daga gidan. Su Halifa suma suna zuwa sula rufa musi baya, Khalid na zuwa bai yi wata-wata ba ya fice yana ƙwala musu kira amma ko waige babu wanda ya yi balle ya saka ran za su kula shi.
Kaza da sauri ta buɗe ƙofar ta rufa wa Khalid baya tana tafe tana faɗin, "Angona ka zo mu sasanta don Allah." Khalid bai bi ta kanta ba suka ci gaba da zabga gudu.
Da yake unguwar ta su babu nisa da gidan Khalid nan take suka ƙarasa gida, sai dai wannan karon hatta iyayen Zarah da ita gidan su Khalid suka faɗa, Malam Liman yana ƙofar gida ya riƙa kallon su da mamaki, bai tsinke da lamarin ba sai da ya hango Mahaifin Khalid da Halifa suna tafe zakara da kaza na biye da su. A madadin Mahaifin Khalid ya faɗa gidan sai ya maƙale Malam Liman ya ce, "Don Allah Malam ka taimaka mana yaron nan Khalid ya janyo nana masifa." Malam Liman zai yi magana karaf suka ji kazaran ya ce, "Abba wallahi sharrin shaiɗan da na Mai turakar aljanu." Malam Liman ya zaro ido waje ya ce, "Me nake gani haka kamar zakara yana magana?" Abba ya ce, "Malam mu je ciki wallahi akwai magana, wai Khalid ne fa ya koma zakara."
Ba musu Malam Liman ya shiga suna shiga ciki tuni ƴan biki sun dare kowa ya faɗa ɗaki, a kan tabarma suka zauna har lokacin Abba bai saki Malam liman ba. Khalid da ke cikin siffar zakara ya rakuɓe a gefe shigarsa keda wuya kaza ta shiga tana kwarkwasa, kallon Malam Liman ta yi ta ce, "Kai amma na yaba da wannan shi ma a yau zai koma zakara." Tana gama magana Abba ya zayyane masa duk abin da yake faruwa.
Malam liman na gama jin bayanin Abba ya ce, "Komai ya zo ƙarshe da ikon Allah." A'uziya ya yi fara karanta suratul baƙara yana biyawa yana tofa wa su Khalid. Nan take jikin Khalid da Walida fara wata irin karkarwa, ba a ɗauki lokaci ba jikinsu ya fara sauya launi har ya dawo daidai kamar ba su ba. A hankali Walida ta fara kalle-kalle ganin mutanen da bata sansu ba ya sa ta ce, "Ina Umma?" Khalid gefe ya matsa yana sauke ajiyar zuciya.
Ɗaya bayan ɗaya mutanen ɗakin suka fito suna ƙare wa su Walida kallo, Malam Liman ya dubi Khalid ya ce, "Mahaifinka ya sanar da ni komai game da yarinyar nan ka yi mana bayanin a ina ka samo ta har ta kusa halakar da ku gabaɗaya?" Khalid ya hau sosa ƙeya yana muzurai, yana cikin wannan yanayin sai alamun tafiya suka ji. Wani tsoho ne ya shigo shigarsa kaɗai za ta nuna maka alamun boka ne, yana shigowa Walida ta yanke jiki ta faɗi. Da ido suka riƙa binsa suna kallo, a zabure Khalid ya miƙe zai yi magana Mai turakar aljanu ya nuna shi da sandar hannunsa ya ce:
"Ka bani mamaki Khalid da har ta sanadinka ake neman karya ƙadarina, ka manta sharaɗinmu ko?" Malam Liman ya dube shi ya ce, "Wanene kai?" Mai turaka ya sake nuna Khalid ya ce, "Mai turakar Aljanu nake, kuma ba zan ce komai ba sai dai ku ji daga bakin wancan idan ya so sai na ɗora daga inda ya tsaya." Gabaɗaya idanu ya koma kan Khalid. Lokaci ɗaya ya fashe da kuka sannan ya ɗora da cewa.
"Tun tasowa ta Allah ya ɗora min son rayuwar hutu da jin daɗi, amma sai dai kash iyayena ba masu yatsu da yawa ba ne. Hasalima Mahaifina saran itace yake a unguwar gwammaja dake jihar Kano, Mahaifiyata koko take da safe ana zuwa har gida ana siya. A haka suka ci gaba da tallafar rayuwarmu har muka samu ilimin boko da na addini daidai gwargwado ni da ƴan uwana mu uku. Lokacin da na gama sakandire mahaifina bai da hali don haka na faɗa harkar gwangwan har ta kai nake bin ubangida wasu garuruwan amma ba don na so ba, kwatsam sai muka haɗu da wani abokina Sale sai ra'ayinmu ya zo ɗaya nan muka ƙulle muka zama abokan juna. Shi ya yi mini hanyar mai turaka na fayyace masa buƙatata ta yin kuɗi lokaci ɗaya, a ranar da muka je wurinsa ba mu dawo ba sai da damin kuɗi sama da miliyan guda. Tun daga nan muka ga wuri kuma duk abin da ya buƙata a wurinmu muna aikatawa, saboda na san halin iyayena ya sa ban nuna musu azzikina lokaci ɗaya ba. Sai na riƙa fito da su kaɗan-kaɗan don kar a zargi wani abu daga gare ni. Na shafe sama da shekara bakwai ina hulɗa da mai turaka, kwatsam da aurena ya matso na nuna masa ina buƙatar mahaukanta kuɗi saboda na lura yarinyar da nake so ita ma irina ce ido a kuɗi.
YOU ARE READING
'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT
Short StoryLedar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙa...