7&8

425 26 0
                                    

*'YAR ZAMAN ƊAKI*

     ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️

               7&8

     Khalid na jin yanda Kaza ta cafki hannunsa ya ware murya cikin tashin hankali ya ce, "Wayyooooo Allah Kaza za ta haike min." Kazar ta ra gwaɗar da kai tana girgiza tozonta ta ce, "Angona yau fa ranar farinciki ne ka taimaki kanka ka ba ni haɗin kai." Tana gama maganar ta miƙa bakinta wurin saitin fuskar Khalid ta ce, "Matso na sumbace ka masoyi." Khalida ta juyar fa kai gefe yana tofar da yawu. Kazar ta tashu sama firrr kamar tsuntsuwa tana kaɗa fukafukanta, bata dira a ko'ina ba sai kan tafin ƙafar Khalid da suke can saman fanka. Khalid na jin Kaza a daidai ƙafarsa ya fashe da wani matsanancin kuka tare da faɗin, "Wayyo za ta mayar da ni Zakara, wayyo Zarah Kaza za ta mayar da ni zakara." Kaza ta sa faratan ƙafarta ta shafo gwiwar Khalid tana faɗin.

"Me ya yi saura Angona da kai da Zakara duk ɗaya ne a wurina."

   Zarah na shirin yin magana ta ji cinyar kaza ta ce, "Amaryata ki ba ni dama kar ba tafi da ke a neme ki a rasa." Zarah na jin haka ita ma ta fashe da kuka don wannan karon ta kai maƙura, ta gama saddaƙarwa rayuwarta. Suna cikin wannan halin wayar Zara fara ringing, ringtone ɗinta  karatun alƙur'ani ne, yana fara ƙara duka suka nemi komai suka rasa daga kazar har cinyar kazar da take iƙirarin ita zakara ce.

  Khalid da yake maƙale a saman fanka sai ji kake faaaaaaaf ya faɗo kan gado, zumu-zumu ya yi saboda yadda ya galabaita. Ya juyar da kansa ya kalli Zarah murya a shaƙe ya ce, "Zarah yai muna ganin rayuwa." Zarah ta goge ƙwallar idonta ta ce, "Khalid wallahi gari na wayewa zan bar maka gidanka, kana gani cinyar kaza wannan ƙaramar hallita tana cewa za ta min fyaɗe." Khalid ya shafa wurin da Kaza ta taɓa ya ce, "Ki gode wa Allah Kaza ba ta haike min ba, kina ji fa wai kaza ce za ta min fyaɗe."

  Zarah bata kula shi ba  ta ɗauki wayarta, za ta bi kiran da aka yi mata daga can ƙofar ɗaki suka ji takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas. Da sauri Khalida ya wawuro zanin gado ya zagaya ta gefen Zarah ya ce, "Zarah ki ɓoye ni wallahi ta dawo, daga ji Kaza je wallahi haike min za ta yi."

  Kafin Zarah ta yi magana daga bakin ƙofar suka ji an ce, "Kun ci sa'a amma babu komai a juri zuwa rafi." Jikinsu ba ƙaramin sanyi ya sake yi ba, Khalid na son yin waya yana tsoron tashi daga wurin.  Dabara ce ta faɗowa Zarah va shiri ta saka wayarta a Airplane mode ta kunna karatun Alƙur'ani, tun suna jin taku a bakin ƙofar har suka daina.

  A hankali Khalid ya janyo doguwar riga ya saka sannan ya ɗauki wayarsa ya wuce wani ɗakin da aka ware don hutawarsu. Yana shiga ya ciro wayarsa ya nemo wata lamba sai da ya kira sau biyar aka ɗauka, tun ba a fara magana ba Khalid ya fara magana bakinsa har rawa yake.

  "Mai turakar Aljanu akwai babbar matsala fa. Yau daren amarcina amma Kaza da zakara sun hana ni walawa, yanzu haka da ƙyar na sha wai ni Kaza za ta yi wa fyaɗe..."

   Khalid bai rufe baki ba kukan Walida a ƙofar ɗakinsu, wani dogon tsaki ya Khalid kamar zai yi kuka ya ce, "Mai turaka don Allah ka yi wani abu wallahi ina cikin damuwa." Daga can ɓangaren aka bashi amsa da cewar, "Khalid ka ji da yarinyar da take yin kuka idan ka daidaita nutsuwarka sai mu yi magana." Khalid ya guɗe baki zai yi magam ƙit ya ji Mai turakar aljanu ya katse.

  Khalid tsabar takaici bai san lokacin da ya fashe da kuka ba, yana tafe yana hawaye ya isa bakin ƙofar ya buɗe. Walida na ganin Khalid ta goge hawaye ta ce, "Uncle na kasa bacci." Khalid baƙinciki ya sake kama shi a daƙile ya ce, "Mu ma ai ba mu yi ba."

  Walida ta fara shinshine-shinahine ta ce, "Uncle ƙanshin zakara nake ji." Khalid ya fisgi hannun Walida cikin ɗakin yace, "Sai ki ci idan kin gan shi."

Zarah na hango Walida ta kashe karatun ta diro gabanta fuska a haɗe ta ce, "Ke! Me ya hanaki bacci." Ta haye kan gadon Zarah ta kishingiɗa tana lumshe ido ta ce, "Uncle bacci zan yi."

  Zuciya ta ɗebi Zarah ta kai wa Walida duka ta ce,  "Ɗaga min gado ko na ci uwarki wallahi." Khalid ya zaburo a fusace ya ce, "Ke Zarah me ye haka?" Walida ta fice daga ɗakin tana kuka ta nufi sashen da Khalid ya fara kaita, da gudu Khalid ya rufa mata baya sai da ya je tsakiyar gidan ya ji fuurrrr a saman kansa. Yana ɗago kai ya hangi Kaza tana ɗaga fuka-fukai ta ce, "Yau babu mai hana ni abin da na yi niyya, ƴan uwa ku kawo min ɗauki." Tana rufe baki sai ga tawagar kaji sun dira a kan Khalid masu danne hannuwa na yi masu danne ƙafa na yi.

  Kazar ta fara rangwaɗa ta ce, "Bari fara salon jan hankali don na birge Angona." Rufe bakinta kw da wuya sai ga gashin jikinta na salewa. Khalid bai yi aune ba ya ganta a sulluɓe ba shiri ya ƙwallah ƙara yana faɗin, "Zarah Ki zo wallahi za ta haike min ta mayar da ni Zakara."

ANGON KAZA A SHA AMARCI LAFIYA, GOBE MAJE GANIN AMARYA DA ANGO😂

AYI HKR DA ERRORS BAN YI EDITING BA.

Ummou Aslam Bint Adam🌚

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLTWhere stories live. Discover now