*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
11&12
AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS
Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.
ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G
PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.
KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.
Washegari.
Asubar fari Zarah ce ta fara farkawa daga bacci, da sauri ta ƙarasa ta fara tashin Khalid da ya saki baki da hanci yana shaƙar bacci. A firgice ya tashi yana faɗin, "Zarah! Zarah ina kazar?" Zarah ta yi ƙasa da murya ta ce, "Khalid gari ya fara wayewa ka tashi mu yi sallah ka buɗe ƙofar mu fita, wallahi ni da ka gani ba zan sake wuni a gidan nan ba." Khalid ya fara muttsuka ido yana dube-dube ya ce, "Zarah ina nan yadda nake ko?" Zarah ta dube shi da mamaki tana faɗin, "Ban gane ba."
Hannunta ya janyo shafa mata a jikinsa sannan ya ce, "Don Allah a mutum nake ko na koma Zakara? Kin san zakarun nan fa suma har magana suna yi." Zarah ta yi guntun tsaki ta ce, "Idan so kake ka koma Zakaran sai ka bari idan na tafi gidanmu ba zakara ba ko Toro (Mijin agwagwa.) Sai ka koma." Ta ƙarasa maganar tana janyo jarkar faro ɗaya, ta fisgo bargon da yake kan gadonta, ta shinfiɗa a ƙasa ta fara yin alwala a kai. Khalid ya kalle ta ya ce, "Zarah ga banɗaki me kike yi haka?" Zarah ta yi masa kallon sheƙeƙe ta ce, "Jiya ina jinka da ƙyar ka ƙwaci kanka amma za ka ce min na shiga banɗaki, wallahi ko kashi na ji kafin na tafi gidanmu a nan zan yi." Shiru Khalid ya yi Zarah ta ci gaba da alwala.
Tana gamawa shi ma ya suri robar ruwa ɗaya, ya gabatar da alwala suka yi sallah. Bayan sun idar Zarah ta dubi Khalid ta ce, "Khalid ka leƙa idan babu komai a waje ka buɗe mana na tafi gidanmu wallahi ba zan ƙara kwana a nan ba." Khalid ya riƙo hannun Zarah cikin shauƙi ya ce, "Haba my love amma ai ko raya darenmu ba mu yi ba." Zarah ta haɗe fuska ta ce, "Khalid!" Yanda ya ji ta kira sunansa ya sa ya tsaya tsam yana sauraronta.
Ta nuna masa ƙofa ta ce, "Wallahi ba dare ba ko safiya ba za mu raya ba, da na samu na kwaci kaina a hannun zakara yana ƙoƙarin haike mun. Ni tun da nake na taɓa ganin masifa irin wannan? A ce kaza da zakara sune za su yi wa mutum fyaɗe wai har da kidinafin." Ta miƙe tsaye ta ɗaura ɗankwalinta ta je wurin ƙofa ta ce, "Don Allah ka zo ka buɗe min na tafi." Khalid ya haɗiyi yawu makwat sannan ya ce, "Haba Zarah ango nake fa ki tausaya min kina ganin baƙar wuyar da na ci hannun kaza kafin na tsero ɗaki."
Zarah ta ɗaga kafaɗa ta ce, "Yanzu ma dama na wurinka ka zauna sai ku kashe amarcin kai da amaryarka kaza, amma wallahi wuni ba zan ƙara a gidan nan ba." Zarah da Khalid haka suka yi ta ja'inja har gari ya waye suna ɗaki kowannensu na tsoron buɗe ƙofa.
Suna nan cikin ɗaki Walida ta ƙaraso bakin ƙofar ɗakin ta fara bugawa, ta window Khalid ya leƙa ya ce, "Walida kin tashi." Walida ta yi miƙa haɗe da hamma ta ce, "Wallahi Uncle na tashi don ma jiya ban samu bacci da wuri ba." Zaro ido Khalid ya yi suka haɗa ido da Zarah don shi a tunaninsa ko abin da ya faru tsakaninsa da kaza ne ya hanata bacci, ya tattaro murmushin ƙarfin hali ya ce: "Me ya hana ki bacci Walida?" Walida ta sake sakin hamma sannan ta ce, "Ga jikina duk tsami yake na so huce gajiyata amma haka bata samu ba, amma zan sake gwada sa'ata anjima." Khalid na shirin yin magana wayarsa ta fara ƙara.
Lambar mahaifinsa ya gani da mamaki ya ɗauka don lokacin ko tara bata yi ba. Cikin girmamawa ya ɗauka da sallama, tun bai rufe baki ba Mahaifinsa ya rufe shi da faɗa.
"Kai wanne irin mara hankali ne? Kai ka haifi kanka da ba za a gaya magana kaji ba? Tsabar ka raina mutane ba sai da nace maka yarinyar nan babu inda za ka da ita amma ka mayar da ni ɗan iska ko? Wallahi tun wuri ka haɗa kayanta ka dawo da ita ina dalili ka ɗauki son duniya ka ɗorawa yarinya, a daren aurenka ka ce za ka tare da ita." Khalid ban da gyaɗa kai ba abin da yake yi. Sai da mahaifinsa ya gama magana sannan ya zayyane masa duk abin da yake faruwa. Da farko bai yarda ba sai da ya ce a bawa Zarah tukunna, Zarah na karɓar wayar ta sakawa Mahaifin Khalid kuka ita ma ta ƙara yi masa jawabi. Wayar ta miƙa wa Khalid, murya a sanyaye ya ce: "Baba yanzu haka mun kasa buɗe ƙofar wallahi tsoro muke ji don Allah ku taho daga gida ka taho da su Halifa su haura ta katanga, idan kuka zo sai mu fito amma wallahi tsoro muke ji."
Hankalin Mahaifin Khalid ba ƙaramin tashi ya yi ba, a gaggauce ya ce masa: "Ba damuwa gamu nan zuwa."
Khalid na gama waya Zarah ta kira mahaifiyarta ita ma ta sanar mata abin da yake faruwa, hankali a tashe Mahaifiyar Zarah ta sanarwa da Mahifin Zarah nan take suma suka ce ga su nan tafe zuwa gidan.
Walida na daga bakin ƙofa bayan sun gama wayar ta sake buga ƙofar ta ce, "Uncle buɗe min na shigo man." Takaici ya kama Zarah don yanda take jin haushin Walida ji take kamar ta janyota ta hau dukanta. Sai da Khalid ya sake leƙawa ta window sannan ya buɗe ƙofar da sauri ya fisgo hannun Walida ya datse ƙofar.
Walida ta samu wuri a gefen katifa ta zauna tana kallon Zarah da take wurga mata harara ta ce, "Aunty ba dai gida za ki tafi ba." A ƙufule Zarah ta ce, "Idan gidan ubanki ne zai ki hana ni tafiya." Khalid ya ɗan ɓata fuska ya ce, "Haba Dear me ya sa kike haka ne." Zarah ta ɗauke kai gefe ba tare da ta kula shi ba.
Bayan wani lokaci.
Bugun ƙofa suka fara ji wanda ya nuna musu alamar Mahaifansu Khalid da Zarah sun ƙaraso ƙofar gidan, wayar Zarah ce ta fara ringing da sauri ta ɗauka. Daga can ɓangaren Mama ta fara cewa, "Zarah ga mu da su Haruna sai iyayen mijinki ko haurowa za a yi ne." Tun Mama bata gama magana ba Zarah ta ce, "Mama a hauro don Allah." Mama na jin haka ta katse wayar.
Walida ta kishingiɗa kamar wata babba ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar Khalid ta ce, "Khalid!" Lokaci ɗaya suka kalli Walida shi da Zarah don yanda ta yi maganar kaɗai sai da ya basu mamaki. Walida bata damu ba ta ci gaba da cewa, "Allah ya sani ka lasa min zuma a baka, ina ji ina gani za ka tsere min ne? Sam ba zai yuwu ba Angona." Khalid da sauri ya matsa jikin Zarah ya maƙaleta. Yana shirin yin magana ya riski muryar Walida na ci gaba da cewa, "Ka ba ni haɗin kai ko yanzu na yi maka fyaɗe don na jima ina jiran wannan lokacin jiya ka kubce min, amma yau ba a yi haka ba."
Kuna son more barkwanci ko kina cikin damuwa zuciyarki ta yi wasai💃🏼 ki nemi littafin *DUBU JIKAR MAI CARBI* Cmplt ɗinsa 300 kacal🥱
Ki ji yadda ake tafka kishi tsakanin matar aljani da bil'adam, zallar soyayyar Aljani da ɗaukan darrusa nemi littafin *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*🤒 300 ne rak karki bari a yi babu ke.
Sarƙaƙiya, makirci da rikicin masarauta. Ki ji yadda ake rayuwa da ruhin mutum uku, sannan kuma a ɗauki fansa da kowanne ruhi. Izzar mulki da rayuwar masarauta ki nemi *AN YA BAIWA CE* Cmplt 300 ne 🥱 Ki siya ki huta nema a groups💃🏼
Aisha Adam
3090957579
Firstbank
0706 206 2624 turo da evidence🥱Ummou Aslam Bint Adam🌚
ŞİMDİ OKUDUĞUN
'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT
Kısa HikayeLedar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙa...