13&14

386 18 1
                                    

*'YAR ZAMAN ƊAKI*

     ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️

               13&14

AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS

Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.  

ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G

PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.

KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.

      Zarah ba ƙaramin mamaki ta yi da jin maganar da Walida ta yi ba, haɗe fuska ta sake yi ta dubi Khalid ta ce, "Dama shi ya sa ka nace sai ka ɗauko yarinyar nan? Dubi yarinya ƙarama yadda take faɗar maganganu marasa ɗa'a, an ya Khalid baka lalubar yarinyar nan a bayan fage? Idan ba haka ba ya za a yi ta faɗi haka?" Khalid ya yi fiƙi-fiƙi da ido don abin ba ƙaramin ɗaure masa kai ya yi ba. Khalid ya kalli Walida fuska a haɗe ya ce, "Ke Walida yaushe muka yi haka da ke? Baki da kunya ne an gaya miki ana gayawa babba haka?" Walida ta yi wani faarrr da ido ta sake kashe murya ta ce, "Kabar kewaye-kewaye ka matso ka bani haɗin kai saboda tun jiya na yi niyyar mayar da kai Zakara Allah bai nufa ba. Ni fa a duk cikin zakarun da na aura kai ka bani wahala." Cikin Khalid ne ya bada sautin ƙuuuuu! Har sai da suka haɗa ido da Zarah. Tsoro ya fara kama shi don maganganun Walida kama suke yi masa da na Kazar daren jiya. Ita kanta Zarah ayar tambaya ta fara ɗora wa Walida don haka ta ja bakinta ta tsuke, babban burinta mutanen gidansu su shigo ta buɗe ƙofa ta fita don ta ci alwashin ko auren ne tana iya haƙura da Khalid.

   Khalid haɗe fuska ya yi shi a dole yana son nuna dakiya don kar ta fahimci ya tsorata, yana shirin yin magana ya ga Walida ta tsugunna a wurin ta fara kyarkyara. Hannu ta zura ta ɗebo kwayaye kaji manya guda huɗu ta ce, "Ungo Zarah je ki soya min su."

Daga Khalid Har Zarah baya suka yi jikinsu na karkarwa, Zarah ta nuna Walida baki na rawa ta ce, "Ko kece kazar ne?" Walida sake sako ƙwai uku sannan ta ce, "Ni ce kaza shi kuma a yanzu ba sai anjima ba zai koma Zakara." Khalid na jin haka ya maƙale Zarah hawaye na bin fuskarsa ya ce, "Zarah ki taimaka min don Allah za ta mayar da ni zakara, wallahi jiya ganin idona na ga Zakaru suna   magana." Walida ta karɓe zancensa da cewar, "Ita ma ba sha za ta yi ba, don jiya dama Ƙanina Ɗanliti ya so yin gaba da ita dukkanku babu mai fita daga gidan nan. Suma waɗanda kuka kira ɗin su ƙaraso ina nan jiransu." Walida na gama magana suka ji muryar su Mama a cikin gidan da alama har sun saka an hauro gidan. Wata gauruwar ajiyar zuciya suka sauke a tare don gani suke mafita ta zo musu, Walida na ganin haka ta yi tsalle sai ga ta fuurrrrr ta koma ƙatuwar kazar daren jiya tana buɗa fuka-fiki. Zarah da Khalid a tare suka yi baya cike da tsoro, kazar ta fara takawa gabansu gashin jikinta na saɓulewa sannan ta ce, "Ku dube ni da kyau, wallahi duk wanda ya tona asirina a gaban mutanen nan ba gida ba ko ina kuka koma sai na biku na hallaka ku." Khalid sai gyaɗa kai yake kamar kaɗangare.

  Zarah ba bakin magana sai ruwan hawaye, Kaza ta yi girgiza sai gashi ta dawo siffarta ta Walida. A daidai lokacin Mama ta ƙaraso wurin ƙofar, Walida da kanta ta buɗe ƙofar ɗakin Mahaifiyar Khalid na ganinta ta ce, "Walin Walin 'Yan zaman ɗaki antashi ƙalau?" Walida ta yi murmushi ta ce, "Mama ya ce muje falo." Mama ta waiga ta ce, "Halifa ka ce da su Babanku da Hajiya Amina su shigo."

Tana gama magana suka wuce Falon, shigar su babu wuya sai ga Zarah da Khalid sun shiga, lokaci ɗaya falon ya cika maƙil sukan su goma a ɗakin, iyayen Zarah da Khalid sai ƙannensu. Mahaifin Khalid ya dubi Mahaifin Zarah ya ce, "Alhaji ya muka ji da abin da yaran nan suka gaya mana?"

  Mahaifin Zarah ya ce, "Wannan aikin shaiɗu ne kawai, ta yuwu ba a yi wa gidan sauka ba shi ya sa suke son hana zama a ciki." Mahaifin Khalid yana shirin yin magana ya hango giftawar saluɓaɓɓan zakara ya wuce ko gashi ɗaya babu a jikinsa yana tafe yana jan buhun shinkafa, da sauri ya kauda idonsa don ya san shi ma buɗe masa ido suka yi.

  Halifa na daga gefe ya yi dariya ya ce, "Ni fa wallahi Abba duk jin su nake, ya za a yi a ce wai kaza har ta yi magana kawai dai sun ruɗa kansu ne." Khalid da Zarah suka kalli juna suka sunkuyar da kai ƙasa, Mahaifiyar Khalid ta ce, "Amma dai Allah sakawa yaran nan wannan wacce irin la'ananniyar kaza ce za ta hana yara sukuni." Khalid ya ɗago ya kalli Walida sannan ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, "A yi dai abin da za a yi amma don Allah a daina zagin kazar nan tana jin ku."

  Gabaɗaya suka saki baki suna kallon Khalid da duk ya yi zuru-zuru, Mahaifiyarsa dama irin mutanan nan ne masu faɗa ta sake cewa, "Zagin kazar wani zunubi ne ban da la'ananniya ka ƙere gida kamar wannan amma ta riƙa tsorata ku wai har da wani tsinannan zakara. Wallahi ka ji jiki Khalid da baka bige shegiya ka karya ƙafafuwanta ba." Mama na yin shiru Mahaifin Khalid ya sake hango wani saluɓaɓɓan zakaran ya zo wucewa kansa ɗauke da tukunya yana tafiya. Cikin Abba ne ya fara kaɗawa, Khalid zai yi magana Baba ya ce, "Yanzu dai ku zo mu wuce gida su Kaji daraja gare su, ƙimarsu har ta fi ta mutum shi ya sa ko namansu ya fi na komai daɗi. Allah dai ya yi musu albarka."

  Walida na daga wurin da take ta ce, "Baba ai kun zo kenan, kai kanka yawuna ya tsinke da kai kaima ina jin zakaran za ka koma. Na ji daɗin kalamanka kaine mijin da zan aura na tara." Halifa na kusa da ita ya zabga mata mari dama ya jima yana jin haushinta tun lokacin da Khalid ya kawota.

Cikin faɗa ya ce, "Wai ke baki da mutumci waye sa'anki? Yaya Khalid shi ya ɗaure miki kike iskanci dama." Khalid ya girgizawa Halifa kai ya ce, "Ummm-Ummm Halifa wallahi yanzu za ka iya komawa zakara ka yi ta kanka." Walida ta kalli kusuwar bangon ɗakin ta ce, "Ɗanladi" Tana rufe baki sai ga wani dogon zakara ya fito yana miƙa wuya gaba jikinsa babu gashi ko ɗaya." Mama na ganin haka ta maƙale Mahaifin Zarah duk a tunaninta Mijinta ne ta ce, "La'ilaha'illallahu. Kai Khalid baka ce min haka sheɗanun gidan suke." Walida ta dubi Zakaran ta ce, "Ɗanladi je ka tsattsage wa Halifa gemu sai ka cire shi tass idan ka gama da gemun ka koma kansa." Tana rufe baki zakaran ya ce, "Dama yunwa nake ji babbar yaya." Halifa na jin haka ya sa hannu ya dafe gemu ya ce, "Ku taimaka min Ɗanladi zai tsattsage ni."

😂 Ku yo ɗauki kun san a cikin Kaji har da wanzamai😂😂

Kuna son more barkwanci ko kina cikin damuwa zuciyarki ta yi wasai💃🏼 ki nemi littafin *DUBU JIKAR MAI CARBI* Cmplt ɗinsa 300 kacal🥱

Ki ji yadda ake tafka kishi tsakanin matar aljani da bil'adam, zallar soyayyar Aljani da ɗaukan darrusa nemi littafin *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*🤒 300 ne rak karki bari a yi babu ke.

Sarƙaƙiya, makirci da rikicin masarauta. Ki ji yadda ake rayuwa da ruhin mutum uku, sannan kuma a ɗauki fansa da kowanne ruhi. Izzar mulki da rayuwar masarauta ki nemi *AN YA BAIWA CE* Cmplt 300 ne 🥱  Ki siya ki huta nema a groups💃🏼

Aisha Adam
3090957579
Firstbank
0706 206 2624 turo da evidence🥱

Ummou Aslam Bint Adam🌚

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLTWhere stories live. Discover now