17&18

357 19 0
                                    

http://www.amiraadam.com.ng/2022/08/yar-zaman-aki-page-17.html

*'YAR ZAMAN ƊAKI*

     ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️

               17&18

AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS

Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.  

ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G

PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.

KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.

   Jin carar da Khalid ya yi ya sa Balele tuntsirewa da dariya har da riƙe ciki, wata gajeriya kaza ce ta ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa tafe tana ɗingisawa. Ɗan lasan na ganinta ya ce, "Ke ƴar chogal me ya kawo ki keda ba a gayyace ki ba?" Kazar ta sake chogala ƙafa ɗaya ta ce, "Kale na zo don kasan ba za a yi babu ni ba." Ƴar chogal na gama magana ta nufin ƙofar da Walida ta shige da Khalid, sai da ta kara kunnenta a wurin ta ce, "Babbar yaya don Allah idan kin gama da Angon naki ki bani ɗani ko siɗin kwano na samu."

Walida na daga cikin ɗaki ta ce, "Duk cikin Angwayen da nake samu babu fitacce zazzafa kamar wannan, idan baki ba ni wuri ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Ƴar chogal na jin haka ta matsa da baya har ta yi niyyar tafiya sai ta hango Mahaifin Zarah a zaune suna ta kiciniya da Ɗanlasan.

   Mahaifiyar Khalid duk ta yi zuru-zuru don Ɗanlasan kai caki yake yi mata ta ko'ina, shi kuwa mahaifin Zarah na zaune ya miƙa wa Allah lamuransa sai kabarbari yake. Cikinsa gabaɗaya Ɗanlasan ya caccake shi, ban da raɗaɗi da zugi babu abin da yake yi masa. Halifa na maƙale a hannun Ɗanladi ya taƙarƙare ya kaiwa Ɗanladi duka a kansa. Lokaci ɗaya ya ga Ɗanladi ya faɗi gefe, kamar yadda tangaran yake fashewa haka ya ga Ɗanladi ya wargaje ya yi ɗaiɗai. Farinciki ne ya kama Halifa yana miƙe wa tsaye ya fara shafo geminsa sai ji ya yi fayau babu gashi a jiki, abin da ya ɗaga masa hankali ganin jini na bin hannunsa. Motsi ya fara ji kamar na ƙarar ƙarafuna yana kallon wurin da Ɗan ladii yake ya ga ya fara haɗe gaɓoɓin jikinsa, tsoro na ya sake kama Halifa yana shirin guduwa Ƴar chogal ta yi tsalle ta cafo Halifa tana cewa:

  "Ɗanlami ka gama da wannan kayan na yi gaba da shi?" Halifa na jin an ce za a yi gaba da shi ba shiri ya fara sakin fitsari a wando, hawaye na zuba ya ce:" Aunty 'yar chogal don Allah ki yi min rai." Ƴar chogal daɗi ya kama ta don ta san ko ba koma za ta yi kalace da Halifa.

  Ɗan Lasan sai da ya ƙare wa Mama kallo ya ce, "Ki ba ni Mama na sha idan ba haka ba zan sauke su ƙasa." Mahaifiyar Khalid na jin haka ta sake fashe wa da kuka ta ce, "Yaro ka dubi girman Allah kar ka yi mini haka." Ƙarar bugun gate ne ya karaɗe ɗakin don da alama su su Zarah sun kasa buɗe ƙofa ta ƙi buɗuwa, Ɗan lasan ya buga tsalle ya faɗa kitchen ɗin Zarah, Mama na shirin arcewa sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da sharɓeɓiyar wuƙa.

A gaban Mama ya tsaya ya ce, "Ki ban na zuƙe ko kawai na farke ki da wannan." Kafin Mama ta yi wani yunƙuri suka riski Ƴar chogal na cewa Halifa.

  "Haba matashin saurayi ka ba ni haɗin kai mana, ni ban damu da sai na mayar da kai zakara ba amma idan ka ba ni haɗin kai daga yau muzuru za ka koma, sai mu ci karenmu babu babbaka." Halifa yana shirin ja da baya sai ji suka yi Baaaam an banko ƙofar da ƙarfi. Halifa na kai idonsa wurin ya ci karo da wani tsololon zakara, tsayinsa zai kai yaro ɗan shekara goma. Jikinsa a saluɓe yake babu gashi sai tozon kansa da aka liƙawa wata tuta, kallon mutanen wurin ya fara yi ɗaiɗai.

  A tsorace Halifa ya ja baya don ya yi tsammanin kansa zai sake yowa, Mama da Mahaifin Zarah suka yi saranda suna jiran ko ta kwana. Zakaran yana nan tsaye suka ga ya fara tsalle yana ɗaga saluɓaɓɓun fukafukansa. Kaza ce ta turo ƙofa tana tafe tana kwarkwasa, ganin haka ya sa Zakaran ya ce, "Kai Halifa ku zo mu gudu kafin su halaka mu." Da mamaki Halifa ya dubi Khalid ya ce, "Khalid kaima ka koma Zakaran ne?" Khalid ya yo kan Halifa ya ce, "Don ubanka na ce ka zo mu gudu kana min zancen zakara." Ganin zakaran mai ban tsoro ya yo kan Halifa ya sa gabaɗaya suka ɗiba a guje suka nufi hanyar gate. Khalid ya ke cikin siffar Zakara ya rufa musu baya, Kaza ta bi bayansa tana faɗin, "Angona ina za ka tafi ka bar ni, ai ni da kai mutu ka raba."

Na  Samu ƙorafi akan link ɗin rannan da na saka, zan ci gaba da typing amma ba kullin zan ke saka wa ta whatsapp ba. Idan wannan page ɗin an karanta da whatsapp next page sai a tafi duniyar Chrome wato a bi link🤒

Kuna son more barkwanci ko kina cikin damuwa zuciyarki ta yi wasai💃🏼 ki nemi littafin *DUBU JIKAR MAI CARBI* Cmplt ɗinsa 300 kacal🥱

Ki ji yadda ake tafka kishi tsakanin matar aljani da bil'adam, zallar soyayyar Aljani da ɗaukan darrusa nemi littafin *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*🤒 300 ne rak karki bari a yi babu ke.

Sarƙaƙiya, makirci da rikicin masarauta. Ki ji yadda ake rayuwa da ruhin mutum uku, sannan kuma a ɗauki fansa da kowanne ruhi. Izzar mulki da rayuwar masarauta ki nemi *AN YA BAIWA CE* Cmplt 300 ne 🥱  Ki siya ki huta nema a groups💃🏼

Aisha Adam
3090957579
Firstbank
0706 206 2624 turo da evidence🥱

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLTWhere stories live. Discover now