*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
15&16
AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS
Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.
ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G
PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.
KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.
Ɗanladi ya fara tafiya yana miƙa wuya gaba ya buga tsalle ya haye kafaɗar Halifa ya fara kai caki gemunsa, Halifa na jin haka ya ƙwallah ƙara ya fara kiciniyar kare gemunsa. Walida ta sake kallon kusurwar bango ta ce, "Ɗan lasan!" Tun bata rufe baki ba Sai ga wani dogon zakara tsayinsa zai yi tsayin yaro ɗan shekara goma sha biyu. Shi kuma yana fitowa tun Walida bata bashi umarni ba ya fara baza hanci yana shinshine-shinshine, da sauri ya buga tsalle yana shirin kai wa Mahaifiyar Khalid cafka, Walida ta buga masa tsawa da cewar, "Kai Ɗan lasan ka kama kanka bana buƙatar rawar kai, ka san aikinka yanzu?" Ɗan lasan ya ware idanu akan Mahaifiyar Khalid ya ce, "Idan kika bar min wannan ma kaɗai ta isa, don da ganinta babban kai ce."
Walida ta buga tsalle ta dira a gabansa ya shaƙo shi da hannu ta ce, "Ni maitarka ta fara ba ni haushi. Yanzu ga wannan tsohuwar ka fara tsotse mai da ruwan jikinta sannan ka ɗaye min fatar jikinta."
Halifa wata dabara ce ta faɗo masa don gani ya yi idan ya yi sake zakaran nan zai iya halaka shi lokaci ɗaya, saboda tuni ya tsattsage rabin gemunsa jini har ya fara tsattsafowa. Halifa wani kukan kura ya yi irin wanda jaruman india suke yi, ya yi ƙaraji ya dunƙule hannunsa ya kaiwa zakaran naushi a kansa.
Zakaran ya faɗi can gefe sai ji kake ya ce, "Ƙiƙiriƙiiii." Halifa ya naɗe hannun riga ya ce, "Matso maza ka ji, wai kai Ɗanladi ko Ɗanladidi ne zan ga ƙarshen iskancinka." Zakaran ya ɗage ƙafa ɗaya kamar yadda masu adaidaita sahu suke yi idan sun tafi kai amarya, sai ya fara gaba yana yin baya yana tura zumɓutu da cikinsa. Halifa sai bin sa yake da ido yana jiran ko ta kwana. Cikin shammata zakaran ya yi tsalle ya haye wuyan Halifa ya fara zazzagar kansa, azaba ce ta ishi Halifa ya fara kaiwa da kawowa a ɗakin yana cewa:
"Ƙwaƙwalwata! Wallahi zai zuƙe min man ƙwalƙwalwa don Allah ku taimaka min wallahi Ɗanladi bakin sirinji gare shi."
Ɗanlasan ya kalli wurin da Mahaifiyar Khalid take maƙale da Mahaifin Zarah, Shi kuma mahaifin Zarah tun lokacin da Mahaifiyar Khalid ta haye bayansa ya fara zungurinta da hannu yana faɗin, "Subhanallah wannan haramci ne, wato da za ki sai mu yi istigari a wuce wurin."
Ɗanlasan ya fara takawa yana tafe yana tsalle-tsalle shi a dole cikakken ɗan gaye don dukin zakarun Walida shi ne wayayye, ya ce, "Wannan fatarta a kwance take da kitse ayau zan sha romo na more." Tsalle ɗaya ya yi ya dira a kan cinyar Mahaifin Zarah, ya fara ƙoƙarin zura kansa ta cikin wuyan Mama da take maƙale da Mahaifin Zarah zakaran ya ɗaga hanci sama yana shinshine-shinshine sannan ya ce, "Tsohuwa da alama baki daɗe da daina shayarwa ba."
Mama na jin haka ta sake ƙwaƙume mahaifin Zarah cikin firgici ta ce, "Don Allah ku taimaka min, yaro dube ni nan ni banma taɓa haihuwa ba." Sauran mutanen ɗakin tun fitowar Ɗanladi, ragowar mutanen ɗakin suka tafi da gudu bakin ƙofa amma ƙofa ta ƙi buɗe musu. Ɗanlasan ya waiga wurin mutanen bakin ƙofa sai kawai ya bushe da dariya, dariyar Ɗanlasan ce ta dawo da hankulansu wurin da yake tsaye. Ya ɗago ƙafarsa ɗaya ya fara nuna matan ɗakin sannan ya ce, "Zan fara tsotse wannan tsohuwar don ƙarni-ƙarni nake ji a jikinta, alamu sun nuna bata daɗe da daina shayarwa ba." Mama ta sa hannu biyu ta dafe ƙirji tana faɗin, "Wallahi rabona da shayarwa tun haihuwar Nasiru yau shekara ashirin da bakwai." Ɗanlasan ya yi tsalle ya fara tura kansa wurin ƙirjin Mama ya ce, "Wallahi a lokacin aka yaye ni yanzu zan ɗora daga inda na tsaya." Mama na shirin magana sai ji ta yi zakara ya cake ta, zuuuuu ta ji yana zuƙe ruwan jikinta.
Kuka ta fashe da shi ta ce, "Kai Khalid ka janyo mana masifa a ina ka samo yarinyar nan da za ta halaka mu." Walida na jin haka ta buga tsalle sai gata ta koma ƙatuwar kaza, ta fara sakin murmushi tana tun karar Khalid. Duk taku ɗaya sai ta saki ƙaton ƙwai, Khalid na ganin haka ya zuba ihu yana faɗin, "Wallahi ni na janyowa kaina, Allah ya isa tsakanina da Mai turakar Aljanu. Wallahi shi ya jaza min komai, yarinyar nan ni ma a hanya na tsince ta." Walida da take cikin siffar Kaza ta ce, "Uban gidana kake zagin aikuwa yau za ka gane baka da wayo." Tana gama maganar ta saka baki ta ja ƙafarsa fiiiii duk yadda Khalid ya so ƙwacewa kasa wa ya yi.
Mahaifin Khalid tun da ya fahimci ƙofar ta ƙi buɗewa ya yi kukan kura ya doki ƙofar yana yin A'uzubillahi. Nan take ƙofar ta buɗe wurin fita har rige-rige suke yi, Halifa na ganin ƙofa ta buɗe ya yunƙura zai fita da sauri Ɗanlami ya danne masa wuya yana faɗin, "Ai wallahi idan ka ga ka fita daga ɗakin nan na gama tsattsafe gashin kanka da gemunka."
Mahaifin Zarah na ganin haka shi ma ya yunƙura yana faɗin, "Hajiya ni fa ba muharraminki bane don Allah ki sake ni." Ɗanlasan ya turmushe su gabaɗaya ya ce, "Wallahi babu inda za ka, tare na ganku tare zan yi muku hukunci." Ɗanlasan na gama maganar ya kafa kansa a jikin ƙeyar, Abba lokaci ɗaya Abba ya fara biya kalmar shahada don a ganinsa ƙarshensa ya zo.
Khalid ban da ihu babu abin da yake yana ji yana gani haka Kazar nan ta shige wani ɗaki da shi, shigar su ɗakin babu jima wa Balele da ya zo wucewa da bahon alkakin Zarah ya bushe da dariyar ƙeta ya ce, "Aikin gama ya riga ya gama." Rufe bakinsa ke da wuya sai ji suka yi Khalid ya ce, "Kikirikiiiiiiii."
Shi kenan Khalid ko an koma zakaran ne oho😂
Masu ƙorafin typing ku yi hkr littafi biyu nake yi fa.
Kuna son more barkwanci ko kina cikin damuwa zuciyarki ta yi wasai💃🏼 ki nemi littafin *DUBU JIKAR MAI CARBI* Cmplt ɗinsa 300 kacal🥱
Ki ji yadda ake tafka kishi tsakanin matar aljani da bil'adam, zallar soyayyar Aljani da ɗaukan darrusa nemi littafin *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*🤒 300 ne rak karki bari a yi babu ke.
Sarƙaƙiya, makirci da rikicin masarauta. Ki ji yadda ake rayuwa da ruhin mutum uku, sannan kuma a ɗauki fansa da kowanne ruhi. Izzar mulki da rayuwar masarauta ki nemi *AN YA BAIWA CE* Cmplt 300 ne 🥱 Ki siya ki huta nema a groups💃🏼
Aisha Adam
3090957579
Firstbank
0706 206 2624 turo da evidence🥱
KAMU SEDANG MEMBACA
'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT
Cerita PendekLedar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙa...