*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
https://chat.whatsapp.com/Bkw4WZsTlH5I8pEbP946SA
5&6
Khalid bai za ci lamarin haka yake ba don haka ya kai duka da gwiwar hannunsa, a daidai wurin da yake jin alamar ana kartarsa da yatsun kaji. Yana kai dukan ya ji siririyar muryar ta sake cewa, "Haba mijin kaza kar ka bari mu yi haka da kai." Hantar cikin Khalid ba ƙaramin kaɗawa ta yi ba, da farko ya ɗauka idan ya kutuntuma wa mai maganar ashar za su dawo daidai. Yana tsaka da tunanin ya ji an dafa kafaɗarsa ana cewa, "Mijina na baya ma gardama ya so ya yi min, kaima karka min haka mijina, don idan ka min gardama gunduleka zan yi." Khalid ko saurara bai gama yi ba ya zuba uwar ƙara yana ƙoƙarin jan ƙofa amma ta ƙi buɗuwa. Ganin ba shi da mafita ya sa ya fara ƙwala wa Zarah kira, don yadda ya ji ana shafar ƙeyarsa abin ba ƙaramin tsorata shi ya yi ba.
Zarah ba ƙaramin tsorata ta yi ba don haka ta koma can ƙuryar gado ta duƙunƙune kanta a ciki, tana nan zaune ta ji ƙarar dirar abu a kan gado. A hankali ta zaro kanta don ganin abin da ya faɗo saboda ilahirin jikinta rawa yake yi, ta gama tsorata har ta ayyana gari na wayewa za ta koma gidansu idan ya so sai dai Khalid ya nemar mata wani gidan. Zarah na ɗago kai ta ci karo da ƙatuwar soyayyar cinyar kaza tana murginawa tana faɗin, "Sai ni ƙanin kaza wato zakara, yayata za ta tasha amarci da mijinta Khalid ni ma ga tawa amaryar tana jirana, amma ni dai ki gafarce ni ɗan ƙunan baƙin wake ne amaren mata nake bi ina kaiwa farmaki." Zarah ta waro ido waje don ko a mafarki bata taɓa tozali da abin da ta gani ba, tana nan zaune ta ji Khalid ya ƙwala ihu yana kiran sunanta.
Zarah na jin haka ta fasa ihu cikin tashin hankali tana cewa, "Khalid don Allah ka fito ka ga kaza tana magana wallahi gidan nan aljanu sun yi yawa a ciki." Zarah na rufe baki ta ji cinyar kazar gabanta ta buga tsalle ta ce, "Ki daina mayar da mace don ni ba Kaza ba ce, yanzu haka haƙƙina na zo karɓa yau mu ɓarje amarci." Cinyar na gama magana ta fara fisgo zanin Zarah nan take Zarah ta fara jan zaninta suka fara kiciniya da cinyar kaza.
Khalid na jin abin da Zarah ta ce ya sake waigawa ya fisgo towel ɗin yana faɗin, "Wallahi ni ma ina cikin wani hali Zarah ki kawo min ɗauki." Daga bayansa ya ga an ɗauke towel ɗin an yi saman toilet ɗin da shi aka ce, "Wallahi ka bani haɗin kai ko na kira ƙannena zakaru su sheme min kai na haike maka yanzu." Khalid na jin haka ya rushe da kuka kamar ƙaramin yaro har da majina ya ce, "Don Allah ku yi haƙuri ku sake ni wallahi ni ba mijin Kaza bane."
Shiru ya ji ba a amsa masa ba don haka ya yi tsammanin ko an rabu da shi ne, ƙofar ya ci gaba da fisga yana bugawa da ƙarfi kamar almara sai ji ya yi ƙofa ta buɗe. Da sauri ya fice daga banɗakin a lokacin ya samu cinyar kaza na ta kiciniya shiga zanin Zarah. Daga wurin da yake a tsaye ya yi kukan kura ya faɗa kan gadon da niyyar ya janye matarsa daga kaidin cinyar kazar, sai ji ya yi an ɗauke shi an buga da ƙasa sannan ya ji an ce, "Ka tashi kasa kayanka ka tafi wani ɗakin ba wannan ba, kuma karka sake ka tafi ɗakin da babu ɗan'adam a ciki. Idan so samu ne ka je ɗakin Walida ko ta zo ta same ka."
Khalid duk irin buguwar da ya yi bai sa ya karaya ya ce, "Wai uban waye yake son shiga tsakanin ma'aurata a daren amarcinsu? Babu inda za ni kowanne matsoraci ne ya fito mu yi gaba da gaba." Khalid tun bai rufa baki ba sai ji ya yi an yi saman fanka da shi, ƙafafuwansa na jikin fanka kansa yana ƙasa yana reto. Tsoro azaba da wuya ta sa ya sako fitsari daga sama ba tare da ya sani ba, Zarah na ganin an tasamma halaka mijinta ta sa kuka tana faɗin:
"Don Allah ku ƙyale shi karku kashe min mijina." Zarah bata rufe baki ba sai ji ta yi an turo ƙofar ɗakinsu an shigo, Khalid yana daga saman fanka idanunsa suka hango masa wata ƙatuwar kaza, tsayi da girman kazar za su iya yin girman yaro mai shekara huɗu. Cikinsa ne ya fara kaɗawa cikin rawar murya ya ce, "Wayyo Zarah Kazaaaaaa."
Zarah na shirin yin magana Kazar da take tafe tiƙis tiƙis ta karɓe zancen da cewar, "Haba Mijin kaza zuwa na yi da kaina ba aike ba, na tafi da kai mu ɓarje amarci ko na biyo ka sama Angona." Khalid ya fara saka hannuwa yana kare jikinsa ya ce, "Don Allah ki koma ni wallahi ba mijinki ba ne." Khalid tun bai rufe baki ba Kaza ta hau saman madubin Zarah tana tafe tana wata irin girgiza za ta ɗafe saman fanka, Zarah na daga zaune Cinyar kazar ta ce mata:
"Zarah ki bani haɗin kai ko na yi kidinafin ɗinki."
Khalid na ganin Kaza ta tunkaro shi gadan-gadan ya sake ƙwallah ƙara yana faɗin, "Zarah kazaaaaaaa, wayyo za ta min fyaɗe." Zarah ita ma ta kanta take yi don haka ta ce, "Khalid Zakara zai yi kidinafin ɗina." Kaza na hawa saman fanka ta yi tsallake ma maƙale hannun Khalid yana cewa, "Angonaaaaaa."
NI MA SAI NA CE NA BARKU LAFIYA KU TAFI CETO KAR KAZA TA HAIKE WA ANGO, NA YI NAN BYEEEEEEEEE😂😂😂
Ummou Aslam Bint Adam🌚
KAMU SEDANG MEMBACA
'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLT
Cerita PendekLedar kazarta ta nuna masa tana maƙale hannu ta ce, "Kazar nan ce take cizo na a hannu, kuma ni ka zo ka kwanta a nan." Da mamaki Khalid ya furta, "Kaza kuma? Gasasshiyar kazar ce take cizonki..." Khalid bai rufe baki ba ya ji ledar kazar ta bada ƙa...