9&10

399 27 0
                                    

*'YAR ZAMAN ƊAKI*

     ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️

               9&10

AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS

Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.  

ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G

PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.

KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.

       Zarah na daga wurin da take a zaune kan gado ta ji yo ihun Khalid nan take hantar cikinta ta sake kaɗawa, takurewa ta yi a lungun gado tana karanto duk wata addu'a da tasan ta taɓa biyata a bakinta don lamarin ba ƙaramin kaɗamata ciki ya yi ba. Saboda tsabar tsoro ta karanta addu'a har da ta hawa abin hawa tun bata direta ba sake ɗaukan wata.

  Kaza na jin abin da Khalid ya faɗa ta waiga tana ɗaɗɗaga ƙafa ɗaya ta ce, "Haba Angona wa za ka kira mana a wannan yanayin da muke ciki." Khalid ya fara ja da baya yana kallon sauran kajin da suka haye kan hannunsa sannan ya ce, "Don Allah ki rabu da ni wallahi ni ko da mace bil'adam ƴar uwata ban taɓa yin zina ba, me ye haɗina da ke kina Kaza ina mutum."

   Kaza ta turo masa ciki gaba sannan ta ce, "Wannan cikin da ka gani sai da ya ɗauki cikin mazan bil'adam bakwai. Kai ne na takwas kuma duk namijin da na yi mu'amala da shi Zakara yake komawa, kalli can."

Kazar ta yi magana tana nuna masa kusurwar bango nan take Khalid ya kai idanunsa, bai yi aune ba sai gani ya yi zakaru na fitowa ɗaya bayan ɗaya daga cikin kusurwar bango. A tsorace ya zaro ido yana shirin yin magana zakaran farkon ya buga tsalle sai da ya yi sama sannan ya fara buɗa fuka-fukai sannan ya miƙa wuya gaba ya ce, "Kukkurukuuuuu." Khalid ya saki baki yana kallon ikon Allah don duka jikin zakarun a saɓule yake babu gashi, zakaran yana gama cara ya kalli Khalid ya ce, "Ɗan uwana ina yi maka murna da shirin fara sabuwar rayuwa, don nan ba da jimawa ba kaima za ka dawo zakara kamar mu. Ni sunana Bala Mai leda yau shekarata huɗu a cikin siffar zakara."

Zakaran farko na gama magana sauran  suka riƙa gabatar da kansu, na ƙarshen cikinsu ya yi girgiza sannan ya : "Jikinka zai ɗau raɗaɗi fatarka za ta saluɓe kafin ka koma Zakara zan gaya maka gaskiya ka yi ta kanta don fyaɗen wannan kazar ba alheri ba ne. Ni nan da ka ganni Harisu sunana Bakanike ne shekarata ɗaya a haka..." Kazar na daga wurinta ta bugawa Zakaran da ya ke magana tsawa na take ya katse sauran maganar da yake yi.

Khalid wani wawan kuka ya saki ba tare da ya shirya ba, ya dubi Kazar da ta yi ƙerere a gabansa, tana banƙaro ƙirji gaba  ya ce, "Yanzu waɗannan da gaske mutane ne kamar ni?" Kaza ta kai tsinin bakinta za ta sunbaci bakin Khalid da sauri ya goce. Zakaran da yake gefe ya ce, "Ɗan uwa ka yi duk mai yi wa ka tsira da kanka."

Khalid na jin haka ya zabura ya watsar da kajin da suka danne shi, ya riƙa surarsu ɗaya bayan ɗaya yana buga su da ƙasa. Duk wacce ya buga da ƙasa sai dai ka ji ta girgije ta ce, "Ka tsokanowa kanka wallahi nima sai na ɗana bayan uwar gayya ta gama da kai." Kaza na shirin faɗo masa gadan-gadan ya yi sufa da gudu ya faɗa ɗaki haɗe da danno ƙofa ya sakar mata sakata.

  Da gudu ya faɗa gefen Zarah ya riƙo hanunta sai kawai ya fashe da kuka. Zarah ita ma kukan ta saka masa don rayuwarta gabaɗaya a dagule take, cikin kuka ta dubi Khalid ta ce.

  "Khalid wannan wacce irin rayuwa muka samu kanmu a ciki?"

Khalid ya matse ƙallar idonsa ya ce, "Zarah yau na ga mutanen da suka koma Zakaru da idona, yanzu haka ni kaina kaɗan ya rage Kazar cen ta haike min, da tuni na koma zakara angon kaza." Saboda takaici Zarah shiru ta yi suka ci gana da zurawa sarautar Allah ido, suna nan zaune sautin karatu na ci gaba da tashi daga nan har bacci ya yi gaba da su.

PLS SHARE 🌚

Ummou Aslam Bint Adam🌚

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLTTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang