02

658 55 4
                                    

Karfe daya daidai aka daura auren Sauban, a Tahir Guest Palace aka yi liyafa. Duk wani kai da kawo da ango ke yi Abiey na zaune guri daya ya natsu kallonsu ma sai ya ga dama yake. Daman can Abiey wani murdadden mutum ne da ba komai yake burgeshi ba, abun da kuma kake ganinsa ba a bakin komai ba, shi za iya daukarsa mai muhimmanci.
Sauban ya masa uzuri ne, saboda ya san halin da yake ciki, kuma ya san abokinsa ba mai yawan son surutu da hayaniya ba ne, tun bayan tafiyar Zahra. A gidansu Sauban Abiey ya karasa wuninsa, duk kasancewar Sauban din baya tare da shi yana can tare da sauran abokansa, shi kuma yana dakin Sauban din doing nothing, ya kwanta sai dai ba bachi yake ba, kansa kuma yana jin kamar babu komai a ciki, domin kokarin tunani yake tunanin komai ya ki zuwa masa. Tashi ya yi zaune ya nufi bathroom sai da ya shiga sannan ya cire tufafin jikinsa ya kunna shower ya sakarwa kansa ruwa, ya rufe ido jikinsa na amsa each and every drop of water da ke sauka a fatarsa. Haka nan kawai ya ji yana bukatar bata lokaci a tsaye ruwan na zubar masa.
Ya kusan awa a tsaye sannan ya kashe shower ya nufi inda tawul yake ya dauka ya daura, ya sake daukar karami ya soma goge jikinsa. Zuwa ya yi gaban madubi ya tsaya yana kallon yadda Allah ya tsara halittar kirjinsa. A nan ma ya bata lokaci sannan ya bawa jikinsa hakkinsa na kamshi kana ya nufi wardrobe din Sauban ya bude dayan bangaren da ya san sabin kaya yake ajewa, ya cire hanger ya saka tufafin sannan ya nufo wayarsa ta dauka tare da key din motar ya nufi kofa kamin ya karasa kofar Anty ta bude ta shigo fuskarta dauke da murmushi.

"Anty..."

Ya furta with confused.

"Me kake yi a daki Abiey?"

Ya dan yi baya kadan kamar mai tunanin abun da zai fada. Anty kuma ta tsare shi da ido.

"Uhm.. Talk"

Ya yi murmushi.

"Anty bana jin sakewa cikin mutane, so i decided na zauna a nan"

"Yanzu da ka tashi ina zaka je?"

"Gida..."

Ya fada da kamar tunanin gurin zuwa, domin ba da niyar zuwa gida zai fita daga dakin ba, kuma idan ba gidan ba be san inda zai je ba.

"Abiey haka kake son zama kamar ba mutum ba, yau ranar daurin auren babban abokinka amman ace kana nan daki kamar mai tsoron mutane? Ka bar shi can by himself ka kyauta kenan? And now you're talking me gida zaka je? Ba kai za a je kai ango ba?"

"Da ni mana, kawai dai zan je na dawo ne"

"Waya fada miki ina dakin nan?"

"Na tambayi Ammy tace bata ganka ba, na kira wayarka baka daga ba, sai na kira Sauban ya fada min kana dakinsa saboda ka karbi makullin dakin"

"Yanzu zan ba wani keys din sai na same shi a inda yake"

"Za'ayi Dinner Anjima"

"I don't think zan iya zuwa, amman zan gwada"

"You have to, Dr ma ta tafi tare da Ammy gida yanzu, saboda su samu shiryawa anjima su zo dinner, sai dai ni ba zan samu dawowa ba yanzu zan wuce"

Ta fada a sanyaye sannan ta juya kamar zata tafi sai kuma ta juyo ta kalleshi.

"Abiey...."

Sai kuma ta yi shiru ta kasa karasawa.

"Ba... Sai.. Kaje gida ba yau.. Zaka iya kwana a gurin Ammy if you like"

Abiey ya yi murmushin da be shirya ba ya shafa kansa ya juya ya juyo.

"Mai Martaba yace kar na kwanar masa a gida?"

"No akwai inda zan je ne yau, maybe can zan kwana bana son ka kwana gidan bana nan"

Wani murmushin ya sake yi na miskilanci.

CIWON - SOWhere stories live. Discover now