For advert contact 08036126660
“Ina ta jiran ka kira ni tun jiya baka kira ba, kuma ka san idan ban ji muryarka bana oya bachi”
Na fada a shagwabe bayan na dauki wayarki. Sai yayi dariya
“Babe ayi min afuwa”
“Miyasa baka kira ni Deen”
Na tambaya cike da damuwa domin na ji muryarsa ba a yanayin dana saba jinsa ba. Sai yayi kamar mai tunanin abun da zai fada min.
“Na je kallon kallo ne sai hankalina ya dauke sosai kuma a lokacin da na dawo na san kin yi bachi so bana son na tashe ki”
“Baka saba yi min karya ba Deen, kallon kallo a daren da kace police za su kame?”
“Yeah bayan mun dawo ne muka samu labari kuma a lokacin na san kin yi bachi shiyasa ban kira ba”
“Amman ni na kira ai, kuma na san kallon kwallo be tana hana ka kirana ba”
“Yes lokacin wayar tana silent ban sani ba”
“At the same time Hajiya ta kira ka kuma ka amsa?”
Ajiyar zuciya na ji ya sauke, sai ya sassauta muryarsa.
“Zahra, can you trust me?”
“Yes one thousand percent, but that doesn't mean to lie to me...”
“Babe na i don't want to hurt you”
“Hurt me like how?”
“No ba zan ci komai ba sai ka fada min, haka zan wuni da yunwa”
Na fada saboda na san shi ne tashin hankalinsa rashin cin abincina, ya san duk yadda na ke fushi bana fushi da abincin, kuma bana bakunta da abincin, idan har na ki cin abinci hakan na nufi damuwar tawa babba ce sosai.
“Serious bana da lafiya Zahra kuma bana son ki sani ne saboda kar hankalinki ya tashi?”
“Me ke damunka?”
“Ciwon kai ne, tun da na aje ki na dawo kaina ke ciwo na sha magani yaki sauka, amman dai yanzu Alhamdulillah”
“Ko dan bana kusa da kai ne”
“Kamar kar mu rabu Babe na”
“Ka ci wani abu?”
“Yeah na karya, kuma yanzu zan tafi asibiti”
“Allah ya baka lafiya Deen”
“Amin i love you”
“I love you more”
Sai da ya sumbanci wayar na ji karar kiss dinsa sannan ya kashe, gaba daya sai jikina yayi sanyi domin komai na mijina ina daukarsa da muhimmanci, ko da kan akaifarsa ya ce yana masa ciwo zan ji kamar nawa ne. Haka na tasa kayan karyawa na saka a gabana na kasa taba komai, gaba daya na ji bana sha'awar cin komai.
“Zahra baki ci abincin ba? Ko wani abu kike so a dafa miki?”
Na dago cike da damuwa na kalli Hajiya da shigowarta kenan take min maganar tana rike da kofin koko da alama kanta ta zubawa.
“Hajiya kin san Deen ba shi da lafiya kuma ba ki fada min ba”
Wani irin dauke numfashi ta yi ta sauke ajiyar zuciya, a take idonta ya cika da kwalla, sai ta zo kusa da ni ta zauna ta aje kofin kokon.
“Idan ma na fada miki ai ba magani zaki masa ba, muna gudun ki shiga damuwa ne shiyasa muka boye miki, a kullum tsoronsa kar ciwonsa ya jefa ki cikin wata damuwa”
Hawayen da na gani yana sauka a idon Hajiya, da kuma kalamanta sai suka ba ni mamaki kuma suka tabbatar min cewar ba a yanzu Deen ya fara ciwon nan and that's mean akwai abun da suke boye min, ina tsaka da tunanin abun da zan fada ko na tambaye ta da zai kara fito min da ainahin abun da yake damun mijina sai na ji ta yi sara a gabar da nake so.
YOU ARE READING
CIWON - SO
General FictionA masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama w...