Tun kamin ta karaso hankalinta ya tashi ganin Abiey a duke gurin motar.
"Innalillahi Abiey"
Ya kalleta daker idonsa har sun soma sauya kala daga fari kal zuwa ja saboda ciwon da yake ji a kirjinsa.
"Sannu bari na kira...."
Bata karasa ba ta mike tsaye da sauri ta kuma dakin taron, da gudu ta nufi inda Ammy take tare da Dr Zainab ta fada musu hankalinta a tashe, kamin Ammy ga mike tsaye kasancewar ta mai nauyin jiki Dr Zainab har ta kusa kai wa kofa, da gudu ta karasa kusa da kanenta ta dafa shi.
"Abiey?"
Rumtse ido ya yi sosai kana ganinsa kasan ba karamin azaba yake ji ba, jakarta ta bude ta ciro key motarta ya nufi inda ta faka motar, sai dai ba damar fitowa da ita saboda motocin da aka faka bayana nata ba za su bari ta fito da motarta ba. Dawowa ta yi da sauri ta saka hannunta aljihunsa ta dauko key dinsa ta zagaya ta bude motar ta yi mata key sannan fito da taimakon securities din da suke gurin aka saka Abiey motarsa Ammy ta shiga baya ta rumgume danta hankalinta a tashe domin ta fara zubar da hawaye. Safeena kuma ta shiga front seat tana kuka da ambaton Allah.
"Wani abu ya same shi ko ya ci wani abu?"
Dr Zainab ta tambaya tana tukin kamar zata tashi da motar sama. Sai Safeena ta girgiza mata kai tana kuka.
"No ni dai muna tare muna hira sai yace min na je ma dauko jakata mu shiga gari ina dawowa sai na same shi a haka"
Ta daga mata kai tana da juyawa ta kalli Abiey. @360 ta isa asibitin kai tsaye ta nufi emergency ko fakin din kirki ba ta yi ba ta bude motar tana fadin
"Ku fito da shi lemme get the bed"
Da gudu ta shiga cikin asibiti, tsakanin shigar kofar emergency din da fito nurses kamar ka rufe ido ka bude ne, domin asibiti ce da ake bawa ko wane marar lafiya da kudi suka zauna a jikinsa kyakkyawar kulawa, balle kuma shi da yayarsa take aiki a asibitin. Da gudu suka iso da gado gurin motar suka dauke shi suka dora saman gadon sannan suka nufi cikin asibitin da shi da gudunsu, kamin a shiga ICU da shi Dr Zainab ta shigo cikin shiga ta manyan likitoci da suke bawa manyan patient kulawa tare da wani Dr Haroon. A take suka hau ba shi kulawa Dr Zainab mace ce Jaruma mai matukar karfin hali hakan ya saka take bawa kanenta kulawa cikin natsuwa da gwarewar aiki. Cikin abun da be fi awa daya ba Allah ya sassauta masa har ya samu bachi.
Ammy ce ta kwana da shi asbiti yayi da Dr Zainab ta koma gida ta kwana, tun a dare Ammy ta sanarwa Anty Amaryar halin da Aliyu yake ciki, sannan ta kira Angon ma ta sanar masa, bikin dinner da ba a kasa da angon ba kenan ya nufo asibitin gurin duba abokinsa, sai ya duba jikinsa ya tabbatar da sauki sannan ya bar asibitin, a daren Sauban ya kwana a gidansa tare da kyakkyawar amaryarsa, Abiey kuma ya kwana asibiti tare da mahaifiyarsa. Karfe bakwai da yan mintuna Anty Amarya ta dira asibitin tare da Narjis da Aisha hankalinsu a tashe. Zaune suka samu Abiey rike da gorar ruwa Ammy kuma tana zaune saman carpet din data gama sallah hannunta rike da carji. Juyowa ta yi a hankali ta kalli Anty Amarya fuskarta dauke da murmushi"Maraba da Hajiya"
Narjis ta karasa gurin Abiey da sauri ta zauna, sai ya sakar mata murmushi.
"Narjis"
"Na'am Abiey ya jikinka?"
"Alhamdulillah"
"Ya jikin Abiey?"
Anty Amarya ta tambaya sai ya amsa mata fuska a sake.
"Alhamdulillah Anty"
Sannan ta maida hankalinta gurin Ammy.
"Ya jikin nasa"
"Gashi nan ai kina gani ya samu sauki"
Sai kuma ta sake juyowa ta kalli Abiey.
YOU ARE READING
CIWON - SO
General FictionA masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama w...