14

377 47 18
                                    

Jikin sanyi jiki na shigo dakin na sai na samu Deen a kwance idonsa a bude alamar be dade da farkawa ba kenan. Da sauri na karasa kusa da shi ina kiran sunansa.

“Deen...”

Sai ya kalli detection dina da idonsa kamar baya gani da kyau, na mika hannu na kama hannunsa ina masa murmushin karfin hali da kuma hawaye a lokaci, sai dai na lura kamar kallona kawai yake ba dan ya fahimci ni dince ba, wata kila ba baya ganin komai. Na saki hannunsa na fita da sauri na zuwa kiran nurse domin bana jin zan iya komawa dakin likita ma, nurse din ta shigo da saurinta dayar kuma ta tafi kiran likita, na tsaya daga gurin kafafuwansa ita kuma tana gurin fuskarsa tana dubawa sai kuma ta karasa gurin da file dinsa yake ta dauka ta bude ta duba sannan ta matso kusa da shi.

“Zaharadeen”

Ta kira be amsa mata ba, kuma be yi wata alama dake nuna yana cikin hayyacinsa ba, ta taba hannunsa ta koma gurin idonsa kamin ni da ita mu juya muna kallon likita daya shigo, kallona yayi sannan ya dauke kai ya karasa kusa da Deen ya shiga duba shi, sai ya juyo ya kalleni.

“Ina maganin da na ce a siyo masa?”

“Kowa be zo ba, shiyasa ban samu fita ma siyo ba, kuma ban ma san inda ake siyarwa ba ina jiran Baba ya zo ne sai a bashi saboda shi yake siyowa”

Ya girgiza kai yana wani guntun murmushi.

“Malama kina wasa da rayuwar mijinki Wallahi, kika yi wasa kadan zaki rasa shi”

“Ai ba kai ne Allah ba, ba kai ke da rayuwarsa ba, na kai ka hallicce shi ba, balle kasan lokacin mutuwarsa, idan Allah yace zai tashi zai tashi Wallahi baka isa ka kashe shi ba”

Tun da na fara ban tsaya ba, hawayen dake sauko min kuma ba su tsaya ba, Nurse sai kallona suke domin sun lura kamar fada nake da likitan, be ce min komai ba yayi masa abun da zai masa ya fice. Sai na durkushe a gurin na fashe da kuka, taya wani zai fada min cewar zan rasa Deen mutumen da yayi min fuka fuka a lokacin da nake tsananin bukatarsu? Na kai hannu na shafa cikina.

“Mun kwallafa rai da buri da yawa akan cikin nan, taya wani zai zo ya nemi abun da ba zan iya ba”

‘Yanzu kenan da aka fada miki cewar zaki rasa shi ina ga kin rasa shi? kina son rayuwar mijinki, idan shi ne zai iya bada komai saboda ki rayu cikin kuwa har da danku ko yarku’

Wani bangare na zuciyata ya soma karantomin abun da ban yi zaton zai zo min ba. Na mike tsaye na karasa kusa da Deen hawaye na ta aikinsu a fuskata ina kallonsa har lokacin oxygen na fuskarsa idonsa kuma a bude sai dai ba kallo yake irin an masu gani ba, kuma irin wadanda suke cikin hayyacinsu.

“Deen zai yi komai dan na rayu, Wallahi ba tabbatar ko rai zai iya kashewa saboda na rayu, da shi ba zai jure ganina a cikin wannan halin ba”

Na sake kai hannuna ina taba cikin nawa.

“Amman zai jidadi idan na yi haka?”

Na durkusa kasa na kama hannunsa ina tabawa.

“Idan ka rayu zamu iya samun wasu yayan, amman kai idan na rasa ka na rasa ka har a bada, Hajiya ma ta rasa da har abada, Bahijja ta rasa yaya, yar da za haifa ta rasa uba, kuma na rasa farinciki kenan”

Na lumshe ido ina jin wani irin rauni na rashin makama abun da zan yi.

“Idan kuma ka rayu na rasa ďan na ce maka me?”

_Zamu baki matacce wanda zaki shaidawa duniya da yan'uwanki cewar abun da kika haifa be zo da rai ba_

Maganar da likitan yayi ta dawo min a rai.

“Ya kamata dai na yi shawara”

Na fada ina mikewa tsaye, sai kuma na tambayi kaina.

“Toh da wa zan yi? Duk wanda zan yi shawara da shi zai iya fallasa wannan sirrin ko kuma ya hana ni, idan ba wannan ba ina da wata mafitar ne? Babu wanda yayi min taimakon da zai ceto rayuwar mijina, wannan ce kadai damata”

CIWON - SOWhere stories live. Discover now