Kwance yake tsakiyar gadonsa talkamin daya saka da niyar fita yana nan a kafarsa ya rumgume hannayensa saman kirjinsa, idonsa a rufe Dr Zainab ta turo kofar dakin ta shigo, kamshin turarenta ne ya sanar masa da zuwanta, daman ta kamshin turare yake gane kowa.
"What now? I thought na baro miki asbitin saboda na samu na huta a nan"
"No ka baro asibiti dai saboda ka san dole zan biyoka na binciki lafiyarka, kuma kasan ina aiki a asibitin ne, idam ba haka ba waye zai bar asibiti ba tare da likita ya sallame shi ba?"
Ta karasa tana dora jakarta saman gadonsa, ba tare da ya bude idon ba yake mata magana.
"Ina tunanin Zahra ne, kin zo zaki dagula min lissafi"
"Zahra kuma? I thought ma zaka min magana fadanka da Mai Martana ne?"
"No wannan ya zama jiki, kawai ina son na tambayi Zahra ne da ace ina da wannan damar, taya akayi take farinciki ta ke rayuwa kamar bata taba sanina ba a rayuwarta, i Just want to know, ni miyasa na kasa samun sukuni ne?"
Ta tabe baki tare da zaunawa kusa da jakarta ta ciro maganin da ta zo masa da shi.
"Zahra tana can ta yi aure Abiey tana rayuwa cikin farinciki da kwanciyar hankali, har ta manta da kai, kai ne kake nan kana wahalar da kanka"
Sai a lokacin ya bude ido ya kalleta.
"Zahra ba zata taba mantawa da ni ba, Zahra ba zata taba son wani ďa namiji kamar yadda ta so ni, no matter what happens Zahra ba zata iya cire so na a zuciyarta ba, I'm first love, first male friend, but tana rayuwa cikin farincikine saboda kin biye son zuciyar Deen kin bashi damar samunta, kuma a duk lokacin da zata tuna da ni zata kalleni ne a matsayin wanda ya ci amanarta, ya yaudare"
Wani irin dauke numfashi Dr Zainab ta yi ta sauke a hankali, ko kadan bata son furucin da kanenta yake yawan yi mata akan abun da ya faru.
"Wannan zaka sha biyu da rana biyu da safe biyu da dare"
Ta fada tana aje masa maganin one after the other. Ya kalleta
"Sometimes kana da wuyar sha'ani... Taya za'ayi na zabi Deen na barka? Ana canja miji a canja yaya amman ba a taba canja dan'uwa, duk abun da na aikata na aikata shi ne cikin..."
Sai kuma ya kasa karasawa sai hawaye suka cika idon, shi dai kallonta kawai yake.
"Ka gyara zan maka allura"
"No need"
Ta saka hannunta ta share hawayenta.
"Miya hada ka da Mai Martaba?"
"Daman ai ba mu taba shiri ba"
Ya amsa mata a takaice sannan ya motsa gefen gadon ya sauke kafafuwansa.
"Abiey..."
Ta kira sunansa a hankali sai ya daga kansa ya kalleta.
"Ka girma, be kamata ace kana sa'insa da Maihaifinka ba, abun da duk kasan zai bata ran Mai Martaba ya kamata ka bar shi?"
"Haba Dr I'm not a child taya Mai Martaba zai hada ni da wasu dogarawa na rika yawo da su kamar akaina aka fara dan sarki"
"Mi ya saka zai hada ka da dogarai?"
"Saboda Anty ta fada masa kirjina na ciwo har na kasa motsawa"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta.
"Babu komai a tsakanin idanuwan Mai Martaba da kirjinsa sai kaunarka Abiey, zan iya hade kur'ane babu wanda Mai Martaba yake so a cikin yayansa irinka, kiyayyarka tana iya bakinsa ne kawai saboda baya iya nuna maka, kai ma kuma ta wani gurin kana masa abun da baya so, look at your hair, nan kitso nan gashi nan ashki a matsayinka na dan sarki be kamata ka yi haka ba"
YOU ARE READING
CIWON - SO
General FictionA masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama w...