*A&A*
_Youghurt Online Class_Learn how to make Youghurt.
Know what brand of ingredients to use,
Equipments and best technique.Dreaming of starting a Youghurt business? 🤩
This class is for you🥰💃🏻CAURSE OUTLINE...
1- Regular Youghurt
2- Sweetened Youghurt
3- Flavored Youghurt
4- Yogo-fruitWhat are you waiting for? 🥳🤩
*Hurry now and register @ ₦500 naira Only 😱*VENUS: Whatsapp & Telegram
DATE: 30th Sept 2022Pay your 500 to 0220232459
GT Bank
Amira Ilyasu RajiAnd send your evidence of payment/Screenshot to this number 07036882378
Matan dake da Freezer aje ba ku san ya zaku yi sana'a da ita ba wannan damarku ce, da kuma ma su son sanin yadda ake hada Youghurt a gida, musamman amare karku bari wanna damar ta wuce ku da kudinki kalilan ki ko yi abun da zaki dade kina amfana.
*** *** ***
Misalin karfe goma na safe ya kira wani abokinsa ya bada masa yadda komai zai kasance na game da taimakon Deen da Abiey ya ce ayi, domin shi ba zai iya zuwa da kanshi saboda Mahaifiyar Deen ta sanshi idan har yaje unguwar neman sanin asibitin da aka kwantar da Deen wata kila zai iya haduwa da ita ko kanwarsa ta fada cewar ta ganshi wanda ya san Abiey ba zai so hakan ba domin ya bukaci a taimaka mata ba tare da ta san shi ya aikata ba.
Ya bawa abokinsa addireshin gidansu Deen ya kuma fada masa yadda zai binciko masa komai cikin har da neman ganin likitan da zai yi aiki da kuma account din da za a saka kudin.Tun daga lokacin be sake waiwayar mutumen ba, har sai da dare da mutumen ya same shi har gida ya fada masa komai, ba karamin mamaki Sauban yayi ba jin cewar an biya komai na aikin, sai kuma daga baya wata zuciyar ta raya masa ko dai Abiey ya saka wani yayi aikin ne bayan shi, duba da ganin be kira shi ba tun safe har yanzu da ake daf da kiran sallah Isha'i.
"Maybe Abeiy ya biya"
Ya fada with confused domin ba shi da tabbacin haka.
"Amman ka bincika wanda ya biya"
"Yeah na bukaci hakan amman likitan ya nuna min wani ne kuma ya bukaci kar ya fada, har yana nuna kamar be yarda da ni ba ma"
"Tun yaushe ka je can? Ni aiki ya dauke min hankali ban samu na kira ba, kai ma kuma ya kamata ka kira ni ka sanar min"
"Haka ne, amman ganin an riga an biya shiyasa nace bari sai na zo gida na fada maka, na je gurin ne da La'asar a lokacin ma likitan baya nan sai daga na samu aka hada ni da shi daker Wallahi"
"Anyways thanks, maybe wani ne ko Abiey"
"Yeah ni ma na yi wannan tunanin"
Sauban ya mike tsaye yana kallon bedroom din Nuratu, sai da ya shiga ya fada mata zai leka gurin abokinsa sannan ya fito, a tare suka fito da Hafiz yana ta fada masa abubuwan da likitan ya fada masa akan ciwon Deen, daga bisani Hafiz din ya shiga motarsa shi ma ya shiga tashi.
ABIEY POV.
Da tunanin halin da Zahra zata shiga ya kwana a ranshi, washe gari ma kana ganinsa kasan akwai damuwa a tare da shi, sai dai Ammy bata ce masa komai ba, domin bata da wata kalma da zata hada a yanzu ta furta masa, cewar zata yi hakuri? Ko kuma ya cire abun a ransa? Ba zata ce tausayin Deen ne ya saka shi wannan halin, sai dai tunanin Zahra da take kyautata zaton shi ne ya dawo masa sabo.
A gida ya wuni ko bakin gate be fita ba falon ma sallah ce kadai take fitar da shi, sai yayi kamar ya daga waya ya kira Sauban ya tambaye shi halin da ake ciki sai kuma wata zuciyar ta hana shi, wai akan me zai damu da mutumen daya raba shi da rayuwarsa? Haka ya wuni har dare be iya kiran Sauban ba, ba dan kuma be damu ba, sai dan yana son ya zuciyarsa ta kara tabbatar da tsanar Deen da yake, idan ma zai kira saboda Zahra ne kawai.
Bayan gama sallah Isha'i yana fitowa daga masallacin dake cikin gidan, ya nufi wani guri da aka kawata da fitilu saboda hutawa da dare ko kuma yin wata tattaunawar, kujera ya ja ya zauna ya daga kansa sama yana kallon taurarin da suka yi ma sararin samaniya ado, wani bangare na rabuwarsu ta karshe da Zahra a ranar dauren aurensu ya dawo masa.
YOU ARE READING
CIWON - SO
General FictionA masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama w...