11

341 62 5
                                    

Jinina suka diba sannan aka shiga dashi dakin gwaje gwaje, bayan mun fito ina jin yadda Hajiya ke fadawa Mama likita ya tabbatar musu ciwon ya kusan lalata hantarsa, sai dai gaba daya hankalin Mama yana kaina ne, na lura tsoro take tana ala ala kar ace ina dauke da ciwon ni kuwa a yanzu ba shi ne a gabana ba, burina ya za'ayi mijina ya samu lafiya.
Alhamdulillah shi ne abun da Mama ta furta lokacin da likitocin suka tabbatar dacewar lafiya kalau nake babu wani ciwo a tare da ni, sai dai hankali ya tashi sosai ganin likitocin da suke zuwa duba Deen, idan wannan ua shiga ya fita wannan ya shiga, basa ce mana komai sai dai su yi magana a tsakaninsu, a kuma yawan shiga da fitan da suke bana jin Deen ya ga fuskar daya daga cikinsu domin idonsa a rufe yake kamar mai bachi wata kila kuma bachin yake ban sani ba.
Bayan mun gama sallah isha'i, Bahijja ta kawo mana taliyar da Hajiya ta buga mata tace ta dafa, kusan lokaci daya suka shigo da Yaya Maryam da wanta ta kawo mana tuwo tare da mijinta, gaba daya hankalinta yana kaina, har mijinta na lura ni kawai yake kallo da alama sun yi zance na ita da mijin nata, ni dai kallo daya na musu na dauke kaina mijinta ma tun da muka gaisa yace min ya mai miji bakina da na shi be kara haduwa ba. Sai kusan tara da rabi suka fito ganin ban motsa da zimmar rakata ba ta kalle ni ta ce.

"Kanwata babu rakiya"

Na dago na kalleta da fuskata data gama bayyana rama ta ta wuni daya da tashin hankalina.

"Ki rakata mana, tun dazun kina zaune guri daya"

Mama ta saka baki, hakan ya tabbatar min cewar akwai maganar da Yaya Maryam take son yi da ni, a dole na yunkura na tashi ina jin cikin na min wani irin nauyi da be taba yi min ba. Ko da muka fito dakin mijinta har ya bace a ward din, muka jero a tare muna tafiya.

"Kanwata ki kwantar da hankalinki Deen zai samu sauki, kuma kin ga likitoci sun ce a nisance shi ya kamata ki kiyaye wannan ko dan babynki"

Na kalleta ina mamakin yadda zata iya bude baki ta furta kalmar na nisanci mijina.

"Ya kike magana kamar baki san tsakanina da Deen ba?"

Sai ta yi saurin dafa ni.

"Na sani, wata kila shi ya saka ya kasa fada miki gaskiyar cewar likitoci sun ce yana bukatar kariya saboda akwai shakuwa sosai a tsakaninku wata kila kuma...."

Bata karasa ba, ni da ita muka huya muna kallon Mama da ta kira sunana tana ta zuba sauri.

"Zahra... Ki bi Yayarki ki kwana a gidanta, idan kuma gidana kike son kwana sai mu tafi"

Shi ne abun da Mama ta fada a lokacin data karasa kusa da mu.

"Zan kwana a nan"

Na fada muryar a sanyaye kamar cike da damuwa.

"Aa ba zaki kwana a nan ba, damuwar kuma ta isa haka, idan kika kwana a a nan ba zaki dauke masa ciwo ba, ki yi ta addu'a kawai"

Zan bude baki na yi magana Yaya Maryam ta rika fuskarsa.

"Yar kanwata ki rika jin magana jin? Tun da Mama tace mu tafi ki bini mu tafi mana"

Na daga kai a hankali akamar toh ba san ina son zuwan ba, sai dan bana son na yi musu a yanzu, domin bani da karfin musun da dai a da ne zan iya har sai sun yarda sun barni.

"Bari na yi ma Mama sallama"

Na fada ina juyaawa na koma inda na fito, tafiya kamar wanda ke jin nauyin kafa haka nake takawa har na isa cikin dakin na tura na shiga sai na samu Hajiya ita kadai a dakin Bahijja ta fita, wata kila an aike ta siyo wani abun ne ko kuma waya take oho.

"Hajiya zan bi Yaya Maryam ma kwana a can"

"Toh Allah ya tashe mu lafiya, Zahra dan Allah ki kwantar da hankalinki kin ji"

CIWON - SOWhere stories live. Discover now