ZAHRA POV.
Bayan mun gama cin abinci ya kwashe kayan sannan ya gyara gurin, kana ya dawo ya rika ni na tashi na koma dakin na zauna, shi kuma ya fita falon domin karasa gogarsa.
“Deen”
“I will be there Zahra”
Yana rufe bakin ya shigo dakin ya zauna kusa da ni.
“Me kike so?”
“Wayarka zan yi game”
Be ce min komai ba ya tashi ya fita falon ya dauko wayar ya miko min sannan ya koma ya cigaba da gugar. Daman na san password din wayarsa kamar yadda ya san nawa, duk abun da nake so ina yi da wayarsa haka shi ma yana daukar tawa yayi bukatarsa. Kai tsaye na cire password din na shiga cikin wayar na danna game din da nake so na soma yi. A lalace na bata awa daya da rabi ina game din ina hamma abun ka da raguwa nan da nan bachi ya sace ni. Ana daf da kiran sallah magariba na farka kaina yayi matukar nauyi alamar bachin na ishe ni har na wuce ka'ida. As usual ina farkawa na ga Deen ya lullube ni da blanket daman ya saba idan ina bachi sai ya gyara min bachin ya lullube ni, wayarsa kuma na rumgume a kirjina that's means be fita da wayarsa ba, wata kila yana gudun na farka ne shiyasa be daga hannuna ya dauki wayar ba. Mika na fara yi sannan na tashi na shiga bandaki na yi alwala na fito na gabatar da sallah la'asar ina zaune ina lazimi har aka gabatar da sallah magariba.
Cike da kuzari na mike tsaye na gabatar da sallah magariba, ina cikin lazimi na ji cikina ya motsa da gudu na isa bandakin tsakar gida, arzikina daya Deen ya saba cika mana durum bandakin ba sai na yi wahalar shiga da ruwa. Sai da na yi yadda raina yake so sannan na fito bandakin ina jin cikina safal kamar ban ci komai ba, sake komawa na yi bandakin dake cikin dakinmu na wanke hannuna kamar yadda addinin musulunci ya koya mana. Ina fitowa ana dauke nepa a take gabana ya fadi, a duniya bayan mutuwa babu abun da nake tsoro kamar hudu, saboda ina ganin komai zai iya taba ni ko kuma ya cutar da ni idan akwai hudu. Da sauri na nufi gadona na lalaba inda na aje wayar Deen na dauka na kunna fitilar sannan na nufi din gulof dinmu na solar na kunna sai gaske ya cika daki, tsoron hudun falo ya hana ni fita na kunna wutar falon, sai kawai na yanke shawarar haye gadona na zauna, idan gogan ya dawo ai dole ya kunna, tsayar gado na koma na zauna domin ban yarda da zaman gefe ko karshen gado kar wani abu ya same ni, wannan yasa idan yana a gida bana da gurin zama sai a jikinsa. Data na kunna da zimmar shiga YouTube na kalli funniest videos sai ga kira ya shigo, kamar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hana ni ganin bakuwar number ce, na san yadda Deen yake kishi idan wani ya ji muryata. Kiran na yankewa sai ga sakon kar takwana ya shigo wato SmS, da bakuwar number da ban wayance ta ba._Deen kana ina, ga mu anan muna shanawa, kaya sun samu ka zo dan Allah_
Ina gama karanta sakon jikina yayi sanyi, tunanina ya tsaya cak, kan kace kwabo hawaye ya taru a idona. Me hakan ke nufi? Deen be daina abun da yayi min alkawarin dainawa ba? Ke nan har yanzu Deen yana hulda da wadannan gulbatattun abokan nasa? Yana nuna min shi na kwarai ne a nan a bayan idona kuma yana aikata abun da ya ga dama? Yaushe Deen ya koyi yi min karya? Yaushe Deen ya koyi boye min sirrinsa? Idan har na ce ban ji komai ba a zuciyata a game da sakon nan dana karanta a yanzu tabbas na yi karya, babu mace da son ta ga mijinta yana shaye-shaye. Abun nan yana da matukar zafi da bakinciki, ta wani bangaren ma ina ganin kamar kara ace mijin mace na neman mata sama da shan kayan maye, domin shaye-shaye yana taba kwakwalwa ya taba lafiyar mai yinsa kuma ya haddasa fitina da juna, wasu mazan ma har duka suke yi ma matansu, mai shan kayan maye baya aje komai baya iya kula da iyalinsa yadda ya kamata, sai dai nawa mijin ya banbanta da sauran mazan, domin ko kuje bana jin Deen zai bari ya taba ni sai idan ban gani ba ko kuma idan baya kusa. Deen baya min karya yana gudun zuciyata tana gudun abun da zai bata min balle har ya saka ni damuwa. Amman miyasa yace min ya daina alhalin be daina ba? Wata kila saboda shaye-shayen miyagun kwayoyi abu ne da ba za'a iya dainawa a take ba ko? Ko kuma saboda ya saba da shaye-shayen tun yana karamin yaro? Haka dai na yi ta magana da kaina kamar wata tabbabbiya ina tambayar kaina ina amsawa kaina, kokari nake na kar zuciyata ta ga laifin Deen, domin har ga Allah ina matukar kaunar mijina, bana son na yi masa wani kalami da zai sosa masa zuciya ko ya saka shi a damuwa, a cikin duhun so na na shiga na yi ninkaya ina ta tarewa zuciyata ganin laifinsa! Daina shaye shaye-shaye ba abu ne da mutum zai iya kai tsaye ba, Deen ba shi da wani aibu, domin baya neman mata, baya sata, kaddararsa kawai shaye-shaye ne, shi ma na dan zai daina idan ma be daina a yanzu ba zai daina wata rana, sai dai wata ranar yaushe? Gobe? Jibi? Gata? Wata nawa? Shekara nawa? Yanzu fa girma muke ciki nake dauke da shi na wata bakwai mace zan haifa ko namiji Allah masani, amman babu macen da zata so ta tara ya'ya ace mahaifin yayanta dan shaye-shaye ne.
YOU ARE READING
CIWON - SO
General FictionA masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama w...