MIJIN DARE Page 1

467 10 2
                                    

*👺MIJIN DARE👺*
  _(Spiritual story)_

    STORY AND WRITING
                  BY
R HUSSAIN(Zinariya)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
       {R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
  *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

  The writer of
So halitta ne
Masarautarmu
Ɗaukar fansa
Iffah ko Hibbah
      and now
MIJIN DARE.

_BANYI DAN CIN ZARAFIN WATA KO WANI BA, IDAN KINGA WANI ABU WANDA YA DANGANCE KI TO A RASHINE._

 
SADAUKARWA GA ƳAN ƘUNGIYATA ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION,☀️🌟 INA ALFAHARIN DA  KU

---------------Kwalliya take ta sheƙawa kamar wacce za taje gasar fitar da sarauniyar kyau,sai jujjuyawa take tana ganin ina ne bai yi ba, wata ƴar tsamurmurar Mata ce,ta shigo ɗakin "mtswww a banza duk wannan kwalliyar ta ɓata lokaci kike, tunda ba wanda zai gani ya yaba"
Matashiyar Yarinyar mai suna INTISAR ta zumɓuro baki tace" ni nagaji da gorin Saurayin nan da kike min, duk abinda nayi sai ki ce a banza,a banza"
"Za kiyi min shiru ko sai na bige bakin, ni kam Inteesar kinyi sallah?"
"Eh nayi" Budurwan ta amsa tana ɓata rai
"to ai shikenan saura in kinje party'n ki ta rawar da kika saba kamar wacce ake wa gangi a ka"
Umma ta faɗa tana ɗaukar garin tuwonta ta fita.
" haba kullum sallah, kullum sallah dai, idan na  dawo daga party'n na haɗa nayi"
Siff ta buɗe  ta tsaya tana tunanin wanne kaya ma za ta sa, dan tafi kowa kyau a wajen.
Wani lace mai sauƙin kuɗi orange colour ta sanya, ɗinkin riga da skirt ,ɗas kayan suka zauna a jikinta sosai kirarta ta fito, juyawa tayi ta kuma juyawa ta kalli kanta sosai tace"wow gaskiya nayi kyau,zama tayi ta ɗanɗasa ɗaurinta,jelar gashinta ta sauka a bayanta,baƙin mayafinta tasa, tare da jakarta da takalmi du baƙaƙe, ta fito tayi kyau sosai, dan daman Inteesar ɗin mai kyau ce.

"Umma ni na tafi"
ko kallonta Umman ba tayi ba, sai cewa tayi kar dai ki kai dare na gayamiki"
ba wata addu'a bare Allah ya tsare sai kin dawo.
Tunda ta fita take jin kamar ana bin ta, sai ta juya taga ba kowa, da haka ta sami napep ta hau sai gidan ɗan Hausa inda za'ayi kamun ƙawarta Amina Bashir wacce ita ce  ta bakwai cikin ƙawayensu waɗan da sukayi aure,saura su biyu,a group ɗinsu,ita da Zaliha Rabi'u.

Tunda taje wajen ta haɗu da ƴanmata take rawarkai,ana saka kiɗa, kuwa Inteesar ce ta buɗe fili da rawa,sosai ta ƙayatar, har DJ ya nemi suyi tare ba musu kuwa,aka sa musu wata 9ja music tuni suka hau yin rawar waƙar ya kamata ya rungume tana wani salo, a jikinsa tamkar tarwaɗa haka ta ke juyi a filin rawar. Rap,rap,rappp!!!! kawai ke tashi a wajen ana ihu,dan sun burge ƴan kallo.
Har tara Inteesar na dare Inteesar na wajen sai da taga Amarya ma anzo ɗaukarta sannan ta wuce  zata tafi, wasu wizaye ne suka biyota, a'a big girl ya tafiya za kiyi ne?"
Kallonsu tayi tace"eh dare ya yi zan koma gida ne"

"gaskiya kin bala'in burgeni yanda kike buga show a jikin DJ kin haɗu fa"
Haushi ne ya kama Inteesar  ta ɗauka ms ko wani ne zai ce yanasonta, tace "nagode tayi gaba abin ta.

Suna mata magana akan ta tsaya, tayi musu banza ta shige napep ɗin da ta tsaida.
Babanta Malam Ayuba yana zaune a tsakar gida yana cin tuwo,ta shigo tana raɓe-raɓe.
"Assalamu alaikum, sannu da zuwa Baba, yi yayi kamar bai ganta ba ya tsani ya buɗe ido yaga Inteesar a gida.
Ƙannenta da sa'anninta duk sunyi aure amma ita, har yau babu wanda ya zo da sunan wai ana sallama da ita.

"Sai yanzu kika dawo, daga party'n, ke ko kunya ba kyaji,kina yawon party'n ƙawaye ke ce can party can Suna ko"
turo baki tayi gaba tana ƙunƙuni ta shige ɗakinta"wash!!!!!nagaji,wai gaskiya yau na burge a wajen nan na fa haɗu ba ƙarya,kawai ihu kake ji da tafi, na iya rawa fa hahhh" ta ƙara da kwashewa da dariya.
Cire kayan tayi, ta ɗaura zani ta fito ta ɗebi ruwa a rijiya kanta ko ɗankwali babu, ba addu'a  ta shige toilet ta yi wanka.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now