MIJIN DARE 19/20

104 0 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*


  
   

     __________Tunda Umma da Nazifa su ka shiga ɗaki su ke hira, tsarabar da ta tawo musu da shi ta bata, girki ta yo musu har da naman kaji sosai Umma ta yi ta sa mata albarka,i Nazifa ta ce"dan Allah Umma ki lallaɓa aunty Inteesar ta zo muje koyan sana'o'in nan ko ɗinki ne ta koya ya fi zaman haka,idan kumai ba za ta yi ɗinki ba, ga airfreshner, car wash, Vaseline, su shampoo, hair condition da sauransu Wallahi Umma ana samu sosai a sana'ar hannu" Umma ta ce "ihum kinga dai yanda muke da ita, yanzu wanke-wanken can tun safe nake fama da ita akan ta wanke amma abu ya gagara ina tabbatar miki ƙarshe dai ni zan wanke kayana" Nazifa ta ce "a'a bari in wanke Allah ya kyauta" Umma ta ce "ki bari na yi, daga zuwanki sai aiki, kui kenan kullum aiki, haka ma da Firdausi ta zo ko zama ba ta yi ba ta hau yi mana wanki ni da Babanku daman Irfan da Imran ke yi, ni kuma in yi na su Salma to makaranta kullum a tafe su ke" Nazifa ta miƙe ta ce "ba ri dai in wanke muku kwanukan, fita ta yi, ta na janyo ruwa a rijiya ta ɗauki omo ta zauna ta fara wanke kwanukan ta na son su yi hira da Inteesar amma ta kasa magana sai dai tayi da Ummi,Umma ce ta fito daga ɗakin ta zauna suka ci gaba da hira, Nazifa ta ce" aunty Inteesar fito ki ji wani labari" shiru ba amsa, ta ƙara maimaitawa Umma ta ce" ki rabu da ƴar banzar Yarinya wa za ta yi wa zuciya kar Allah ya sa ta fito ai ta saba" Nazifa ta yi shiru ta na tsoron kar Inteesar ta ƙara hawa dan ɗazun nan ta gama zaginta,sai da ta wanke kwanukan ta share gidan tas, ta wanke musu bokitai da robobi da butocin gidan sosai ta zage ta gyara musu gidan har yana ta cire musu, daman ta kawo musu abinci ga Masara da Umma ta dafa, Nazifa ta ɗebi masarar dan tanaso ita da ƴaƴanta, duk abin nan da su ke zai ton su Inteesar na ɗaki ta na jinsu, sai da azahar ta yi sannan Nazifa ta da hankalinta ya ƙi kwanciya ta koma ɗakin aunty'n nasu dan lallaɓata ta yii haƙuri, ta na buɗe labulan ta ga babu kowa a ɗakin, gabanta ne ya faɗi ta ce" ina kuma ta tafi, Umma ba ta nan ko kin aiketa?" ba tare da damuwa ba Umma ta ce" yo daman ni na isa ta sanar da ni inda za ta je, ai ta saba" cikin tashin hankali Nazifa ta ce" ni wallahi hankalina bai kwanta ba, bari na duba ko gidan Hajiya ta shiga"
Umma ta ce"kar ki wahalar da kanki ki je ki yi sallar ki, ta dawo dan kanta" har su ka yi sallah su Na'ima da Salma da Imran su ka dawo daga makaranta babu Inteesar nan hankalin Umma ma ya fara tashi,Salma da Na'ima ganin Yaya Nazifa a gidan sai murna su ke suna ganin abinci da nama sun san ita ta kawo musu tare suka ci, da su Muhammad  sai da su ka yi sallah sannan suka sa kayan islamiyya su ka tafi, Nazifa ta ɗauki gyale ta ce" Umma ba ri in dubo Aunty daɗewar ta isa haka" Umma ta ce "to nima hankalina bai kwanta ba wallahi" Ummi ta yi bacci su Muhammad na wasa Nazifa ta fita nema.

Inteesar kuwa tunda ta baro gida ta miƙi hanya ta na ta jin haushin su Umma, wajen wata bishiyar tsamiya ta je ta zauna ta haɗa kai da guiwa ga ta ba tada tsarki tana al'ada MIJIN DARE da shi ne ya tun zura zuciyarta sai dariya ya ke ya sata a ƙunci da damuwa, bacci ne ya fara ɗaukar ta a wajen babu wanda hankalinsa ya kai kanta, ta ke ta fara mafarki da wasu halittu su na ce wa, idan su ba sa sonki ai mu muna sonki, idan su ba za su iya zama da ke ba daman mu muna tare da ke, za mu iya ɗauke ki mu mai da ki duniyarmu, Ummanku ba sonki ta ke ba, tafison su Nazifa zamu tafi da ke inda za'a baki kulawa za ki zama sarauniya a duniyar aljanu, sai dai muna tsoron ƙaninki Irfan Yaron ba zai bar mu ba"  a baccin Inteesar ta ce" kar ku kaini  dan Allah ku yi haƙuri ku barni cikin ƴan'uwana, zan zauna da su a hakan kar ku cutar da ni" cikin kuka ta ke faɗa wa halittun haka,haɗi da tsananin tsoronsu.

Aljani MIJIN DARE wanda shi ne shugaban tawagar aljanun ya daka mata tsawa ya ce" kin manta akwai ƴaƴanki a duniyarmu muna da yara har huɗu da ke kuma ba zan rabu da ke ba, ƴaƴanki duk aljanu ne dan haka dole ki bi mu"


Nazifa sai maƙota ta ke bi neman Inteesar har ta haƙura ta dawo, Umma ta ce ƙila gidan wata ƙawar ta tafi, kinsan daman ta ce ba za ta ci masara ba, ni nafi tunanin hakan" Nazifa ta ce"kai amma aunty ba ta kyautawa gaskiya ta ɗau alhakina, haka ta ƙara ci wuninta ta biya wajen Baba ta gaishe shi, nan ya dinga karanto mata uzurinsa, na babu,babu har bashin da ya ci jiya na Haidar wai ya ari dubu ɗaya ankai Inteesar asibiti, ya ce" kinga yanzu ba dan yayarku ba ai ba na dinga cin bashi ba, ga ta har yau babu Saurayin da ya taɓa zuwa da sunan zance wajenta" Nazifa ta ce" Baba aure lokaci ne ina ji a jikina Aunty za ta yi aure muddun lokacin ta ya yi,addu'a za ku dinga  yi mata na Allah ya bata Miji nagari, wanda zai kula da ita Allah ya na sane da ita" Baba ya ce " addu'a ta nawa kuma tun kuna ƙanana nake muku har ita, ku ba ga shi kunyi auren ba, amma ita inda kikasan na shuka dusa har yau shiru, mtsww abun nan na ƙona min rai, Allah duk wanda ya zo ko waye ba shi ita zanyi na huta"
Nazifa ta ce "da sanin Allah Baba komai mai wuce wa ne, fatan mu dai Allah ya nuna mana  auren aunty da rai da lafiya" kuɗi ta ɗauko dubu uku ta ba shi, ya karɓa ya na washe baki sai ya hau shi mata albarka, ta yi masa sallama ta ja ƴaƴanta su ka tafi.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now