17/18

93 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*






  

__________Duk da su  Mama sun tafi, sai da Ibrahim ya fita dan samawa kansa abinda zai ci,Kheesat ta kwantar da yaronta Ammar ta na jiran Ibrahim ya dawo, tsire da Rufaida fura ya siyo ya dawo,sallama ya yi ya ga ba ta parlour sai Ammar da ke bacci, zama ya yi, ya yi bisimillah ya fara ci, Kheesat ce ta shigo sanye take cikin night gown riga da wando masu santsi milk colour, zama ta yi tasa hannu ta na ce wa" au da cinyewa za ka yi?" bai kula ta ba dan ɗabi'arsa ce ba ya magana idan ya na cin abinci, ranar dai kamar Khaleesat ta nutsu haka su ka kwanta lafiya ba masifa, bayan Ibrahim ya dawo daga sallar asubah ne, ya ga Khaleesat ko tashi ba ta yi ba, "haba Ummu Ammar me ye haka ne, yanzu ki ce duk tashin ki da nayi akan kiyi sallah ba ki tashi ba har aka idar?" Khaleesat ta yi miƙa haɗi da hamma hahahh mtswww ai zanyi ni banason takura sai ka ce kabarinmu ɗaya" ta na mita ta shige bayi Ibrahim ya girgiza kai kawai, ya na mamakin sauyawar Khaleesat da ba haka ta ke ba, ƙur'aninsa ya buɗe ya ci gaba da karatunsa, cikin ƙasa-ƙasa da murya, Khaleesat kuwa na idarwa ta koma gado dan ko addu'ar ma ba ta tsaya yi ba bare a je ga azkar, Ibrahim da abun ya ke ba shi mamaki ya tsaya da karatun ya tafi tunanin da, farkon aurensu Khaleesat ce ke tashin sa,dan ita tun huɗu idan ta tashi ta gama bacci sai dai da rana, ko ya ce ta koma baccin asuba sai ta ce masa babu kyau akwai mala'ikun da su ke saukowa su na nemawa bayi gafara a daidai wannan lokacin amma banda masu bacci, sai dai akwaita da son jin kiɗe-kiɗe da rawa, sai ta wuni jin waƙoƙi, tun ya na magana har ya rabu da ita, abun bai ta'azzaraba sai da ta sami ciki, sai ta fara sauya halayenta daga mai biyayya zuwa mai taurinkai, duk sai Ibrahim ya ɗauka ciki ne ya sauya ta, har cikinta ya isa haihuwa ya kaita gida, duk abinda ya kai mata a wulaƙance ta ke karɓa, sai bayan ta haihu ya na ganin yanzu za tak dawo dai-dai sai yaga saɓanin haka, ranar suna kuwa yanda Khaleesat ta yi wa dangin Ibrahim abun ba kyan gani, a cikin mutane ta ce" anzo a ci banza, bayan nak kowa daban kamar yanda ya kawo nan, ai haka aka kai musu" Hajiya Hajara mahaifiyar Ibrahim ta ji ba daɗi, dan da wani ne ya ce mata Matar Ibrahim za ta yi musu haka ba za ta taɓa yarda ba,sai ga shu a gabanta ta yi, Khairat wacce ta ke ƙanwa ga Ibrahim ta miƙe dan maida martani, Hajiya ta hanata ta kaɗasu su ka tafi.

A ka dinga yi wa Khaleesat faɗa, kamar za'a cinye ta, ko ajikinta musamman Mama ta je har gida ta ƙara bawa Hajiya haƙuri,tun daga lokacin Khaleesat ta sauya, har aka maida ita gidanta bayan arba'in,Ibrahim ya na ta zumuɗi iyalinsa sun dawo,tun a ranar su ke samun saɓa ni har yau.

Sai da rana ta yi sannan Khaleesat ta tashi, gani ta yi Ibrahim har ya yi wa Ammar wanka ya na shirya shi, taɓe baki tayi ta fita dan ɗora breakfast, Ibrahim yana jiran a gaishe shi yaga banza ma ta fi shi a awajen Khaleesat, cikin sauri ta haɗa breakfast ta shiga wanka, kafin ta fito Ibrahim har ya karya ya na ta sauri zai wuce aiki, tana fitowa taga yak ci mata abinci, ta tsare shi da ido, "waye ya ce ka ci min abinci iyi, ba kai kasan hanyar kai ƙarata gidanmu ba, to ka ci Allah ya isa" ƙarfin hali Ibrahim ya faɗa a ransa ya ce" ki shiga hankalinki Khaleesat duk abunda kike yi ina sa ne da shi, ba wai tsoronki nake ji ba,a'a ina duba mafitar mu ne,but idan kika ƙure ni, wallahi za ki yi da na sani" Aljanin da ya haɗa wannan faɗan sai rawa ya ke yana ta sheƙa dariya, burinsa kawai shi ne Ibrahim ya saki Khaleesat.

A Fushi Ibrahim ya bar gidan, ya na driving ya na  faɗar innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun,haka ya ke ta maimaitawa harm zuciyarsa ta yi sanyi....

SHAMS da ya zo ma'aikatarsa dan yin sallama da sauran staff waɗan da su ke kula da ita, ya sanar da su za'ayi interview nan da ofer week zai shigo garin kafin lokacin, fatan alkhairi su ka yi masak sannan ɗaya daga cikin staff ɗin ya kai shi har airport ya hau jirgi dan komawa garin Lagos.

Su Iftihar da Daddy su na garden ya na jin hardarta, kafin malam ya zo, dan duk alhamis da juma'a ya ke zuwa,sauran ranakun kuwa ta na makaranta, kakarewa Iftihal tayi, ta sake ayar Daddy ya girgiza kai alamar ba haka ba ne, ta kuma sakewa nan ma ba haka ba ne, sai ta fashe da kuka, tun asuba ta ke biyawa amma ta kakare, murmushi Daddy ya yi ya na mai ce wa "I'm sorry my daughter haka Al-ƙur'ani ya ke, ba shi da gwani ba kiga Sudees ba kwanaki ya na cikin karanta fatiha ya ji ta gudu" Iftihal ta ce"Daddy tun asuba na ke biyawa kuma fa na iya"Daddy ya ce "haka ƙur'ani ya ke ba'a alfahari da shi,yanzu sai ya ba ki kunya, tuna mata ya yi sannan ta ci gaba da karatun, jin buɗe gate ya sa su ka kalli Habu mai gadi, Shams ne ya shigo, cikin murna Iftihal ta fara "oyoyo Yaya,oyoyo" murmushi ya yi yana mai isa gurunsu, riƙe masa hannu Iftihal ta yi tana ta murna, Daddy ya rungume shi ya na masa welcome, duk kansu su ka shiga ciki, Mami ta ce"to ka ce tafiyar safe ka yi, sannuka da zuwa"ɓ durƙusawa ya yi ya na mai gaishe da Mami, sannan ya wuce sama dan shiga ɗakinsa ya watsa ruwa ya zo ya yi breakfast.

Bayan ya karya ne ya ke sanarwa da iyayennasa duk kan abinda ke faruwa na dange da sabon company da zai buɗe, sannan ya ce "wallahi Daddy naga wani Yaro jiya da yamma, yana tafiya a galabaice daga gani ma daga school ya ke, na tausaya masa har revised na yi, ko zan ganshi in taimaka masa ban sa me shi ba"
Gaba ɗayansu su ka cika da jin tausayin Yaron, Daddy ya ce"ai da ba ka wuce ba Shamsudeen ƙila Ubangiji ne ya kaika wajen dan ka taimaka masa,ka yi saka ci da damarka" Shams kamar zai yi kuka ya ce"idan na koma insha Allah sai na nemo shi a duk inda ya ke" Allah ya sa, duk kansu su ka amsa, ameen Iftihal ta ce, a sanyaye.

"Assalamu alaikum" Feenat ce ta shigo da sallama sanye ta ke cikin ɗamammiyar riga top ta sha kitson attachment brown da blue, da matsattsen wandon ta pencil, ga glass da ta kwama a fuska duk ya cinye rabin fuskarta ta,"wa'alekumussalam da Feenat yanzu ki ke tafe"
Mami ta amsa da fara'a a fuskarta, kamar gaske ta ce" eh Mami ni ce" ta zauna ɗaya daga cikin kujerun parlour'n ta na gaishe da Daddy,Shams da kallo ɗaya ya yi mata ya ji zuciyarsa ta fara tashi,ya miƙe ya ce" bari in ɗan zaga gari Daddy" tsilum Feenat ta miƙe " pls bros may i follow u?" harararta ya yi ya ce"no!" ya fice da sauri, Allah ya kiyaye a ganni da wannan Yarinyar, ya faɗa ya na nufa parking space dan hawa mota.
Iftihal ta ce"aunty Feenat kinsan Allah tunda kika dawo nake son zuwa in ganki" Feenat da bata ji daɗin shariyar da Shams ya ke mata ba, ta yi yaƙe ta na mai gyara glass ɗinta dan kar hawaye ya zubo, ta tsani a jizgata in public, Mami ta ce" ku shiga ciki ke da aunty'n taki sai kuyi hirar yau she gamon, daman ba ki da magana sai aunty Feenat,aunty Feenat" dariya Iftihal ta yi ta na tashi ta kamo hannun Feenat ɗin ta na ce wa"zo mu shiga ciki, sannan ta ce"Mami Lantana ta kawo mata drink ɗakina" su ka nufi sama tare sai lokacin Feenat ta sami damar barin hawayenta ya zubo,a wayance ta share su ka shiga ɗakin,sai hira  wacce duk rabin hirar akan Shams ne.

A gidan Dr.Raihana kuwa ba ta san ma Feenat ta fita ba,sai da ta duba ɗakinta taga batanan, sannan ta kira wayarta, su na cikin hira Feenat ta ji kiran amsawa ta yi da "hello mom" daga can Dr. ta ce kina ina?" Feenat ta ce "ina gidansu Yaya Shams'' Dr ta ce"okay,okay ki gaishe su" ta ajiye wayan.
Iftihal ta cika da mamaki wai daman za ka iya fita da mota ba tare da sanin  iyayenka ba?.

*Zinariya ce✍🏻*

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now