15/16

96 1 0
                                    

*بسم الله الرحمن الحيم*

          Page 15/16

___________Sosai Inteesar take kuka cikin daren, babu wanda ya ji ta bare a taimaka mata, MIJIN DARE da ke ƙara sakar mata ciwo ya na ta dariya dan babu abinda ke saka shi nishaɗi irin cutar da bil'adama, Inteesar da ke ta faman jan tsaki "mtswww kai wayyo Allah, sai kuma ta sa kuka, babu ambaton Allah ba komai, sai dan kansa Aljanin ya sakar mata mara sannan ya daki jikinsa da nuna alfahari ya ce"sai ni uban arna dangin shaiɗanu sai   ni kafuri uban kafurai duk wanda ya bar Allah zan kasance tare da shi har ya mutu hahhhhh" bacci mai nauyi ne ya ɗauki Inteesar Aljanin ya rikiɗa ya fara saduwa da ita,a wahale ta ke baccin, har asuba Umma su ka fito su ka yi sallah tasan Inteesar na hutu ya sa bata tashe ta ba.
Da matsananciyar damuwa Inteesar ta tashi ,su Irfan ne da su ke karyawa a tsakar gidan tare da ƙannensa, ganin Inteesar ta fito su ka gaisheta ba, babu wanda ta kalla bare ta amsa masa,murhu ta nufa ta buɗe ganin Masara Umma ta ɗora zata dafa musu a matsayin abincin rana, Inteesar ta ce"kutmar durin uwar nan, idan na ci wannan abun Allah ya tsine min,tsabar talauci masara za mu ci wallahi ba zan ci ba" ta sauke ƙasa ta ɗora wata tukunyar ta zuba ruwan wanka, Umma ta ce "to kar Allah ya sa ki ci, mara hankali jiya kamar ki mutu abun tausayi amma daga samun lafiyarki kin fara masifar da kika saba, ko tausayin kanki bakya ji" tura baki gaba tayi ta fara ƙunƙune , Baba da ya ke jin duk abinda su ke ya fito ya ce"Allah ya ƙara, akanta ki ke maida min da  magana ga shi tun ba'a je ko ina ba, ta na zaginki" Inteesar ta yi shiru a zahiri ta ke rashin kyautawa amma a zuciyarta ba ta jin daɗin hakan da ta ke wa iyayenta, su Irfan su ka yi wa su Umma sallama sannan kowa ya tafi makaranta.

Baba ya dinga faɗa akan abinda Inteesar ta ke yi, ta na zaune ta na kula da wuta har ruwan ya yi zafi ta juye ta sirka,ɗaki ta koma ta  ɗauro zani ta fito, harararta kawai Baba ya ke, ya na jin takaicin ganinta a gida haka ba aure, "ke Laure ki miƙo min hulata na ce ko, kina gani nayi rana ban je kasuwa ba" Umma  ta shiga ɗakinsa ta ɗauko masa wata koɗaɗɗiyar hula ta yi datti ta ce" ga shi Malam" Baba ya ce" yauwa Laure to mu munf  fita nema" Umma ta ce" adawo lafiya" sannan Baba ya fita, sai da Inteesar ta shafe minti arba'in ta na kwalliya sannan ta fito, ta ɗauki shayinta a cikin jug duk ya yi sanyi farau-farau da shi, dire jug ɗin ta yi, ta na mita, gaskiya ba zan iya shan wannan shayin ba, ya huce kuma ba wata madarara arziki, guntun bread ɗin kuwa ko kallonsa ba ta yi ba, ya nufi ɗakin Umma " dan ALLAH ki ban hamsin in inje in siyo awara" Umma da ta ke gyaran karkashin miyar dare ta ɗago ta ce" kinyi wanke-wanken ne?" ɓata rai Inteesar ta yi ta ce"yunwa nake ji, idan na dawo zan wanke ai" ɗari Umma ta kwance a bakin zaninta ta miƙa mata"je ki siyo ki karya" cikin jin daɗi Inteesar ta karɓa ta fita.

Tafe ta ke tana yauƙi da yanga still bin ta ta ji  a na yi a baya,tsayawa ta yi ta ji an tsaya, a hankali ta juya ta ga ba kowa, ta ci gaba da tafiyarta, wasu Samari ne su ka shigo unguwar ɗaurin auren wani abokinsu, ɗaya daga cikin su ne ya ce" kai Maleek kaga wata zazzafa?" wanda ake kira da Maleek ɗin ya ja dogon tsaki, ya ce" ko a Lagos ba na kula Hausawa ba re a Yola, kar ka ƙara yi min tayi irin haka" su ka wuce ɗayan  ya ce" kunga fuskarta kuwa, tab sai ka ce akuya hahhhh" gaba ɗayan su su ka sa dariya su na tafawa.

Inteesar jin suna wuce wa sun sa dariya yasa ta san da ita su ke, har ta shiga gidan ta na jin haushin abin da waɗan nan samarin su ka yi mata, ta ɗarin ta siyo ta dawo, kasa ci ta yi ta na jin damuwa a ranta, har Umma ta fito ta ga Inteesar ta yi tagumi tausayinta ta ji, ta ce" ba za ki ci awarar ba ne?" Inteesar ta fara ci, ta ci biyu kenan ta jin sallamar Nazifa da Yaranta Ahmad,muhamud sai wacce ta yaye Amina ana kiranta Ummi sunan Mahaifiyar Dr. Zayyad ne.

Yaran ne su ka durƙusa su na gaishe da Inteesar, ta amsa a hankali ta na ce wa''har kin zo kenan" Nazifa wacce ita anan sammako ta yi dan ta sami Baba a gida, ta ce" eh, ta ta gaishe da Umma, cikin sakin fuska Umma ta amsa ta na mai ce wa ku shiga ciki mana" Nazifa ta ce"Allah ya sa Baba bai fita ba" Umma ta ce"ayya ai kinyi rana tun ɗazu ya fita, sai dai ko a kira miki shi" Nazifa ta ce"kash! na so in same shi a gida ne, dama akwai wani form na koyan sana'o'i shi ne Abbansu ya ce min ko aunty Inteesar za ta yi, in ɗaukar mata zai biya, na ce sai na zo naji abinda Baba ya ce" Inteesar ta ce "sana'o'i kuma?" Nazifa ta ce"dan Allah  aunty Inteesar kar ki ce ba za kiyi ba, tare za mu yi fa" taɓe baki Inteesar ta yi tana ɗauke kanta, alamar zancen bai sa mi karɓuwa ba.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now