MIJIN DARE

142 2 0
                                    

NA
                 
R.HUSSAIN(Zinariya)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

       F~Page 5/6

_____________Waye ne,  Khaleesat ta faɗa ta na tsaye bakin ƙofar gidan nata, Ibrahim Mijinta ya amsa "ni ne dear "
Buɗewa ta yi ganinsa a ƙasa ba  tare da motarsa ba ta bi shi da kallo, "lafiya ka dawo?"
Murmushi ya sakar mata yana shiga ciki, ya ce" mantuwa nayi na decument ɗin Company da na shigo da su jiya da daddare, bin ta yake da kallon sha'awa,ya wuce bedroom ya ɗauko ya na zama bakin gado haɗi da   zuba tagumi hannu biyu, shigowa ta yi ta na cika ta na batsewa, "ka ɗauka, to ka koma mana"
Ɗagowa ya yi ya kalleta yace " yau ni kike kora dear, wai me yake damun kanki ne"
Khaleesat tace" ni ba korarka na yi ba, ka yi ta zama kar Allah ya sa ka koma" ta fice a ɗakin. Kitchen ta nufa dan ɗora girki kafin Yaronta ya dawo, tuno mafarkin da tayi ɗazu ya sa ta ajiye komai ta koma ɗaki domin yin wanka, ya na zaune inda ta bar shi, kayanta ta cire ta nufi toilet, jikin Ibrahim na rawa kuwa ya bita, ko Allah zai sa ya dace.

Tana wankan ta ganshi ciki, "me ye hakan ka ke yi ne, dan Allah ka fita anan"
Cikin dakewa irin ta barazana yace" ba inda zani sai kin ba ni haƙƙi na yau Khaleesat"
Cikin tashin hankali wanda batasan dalilin yinsa ba ta janyo towel ta na ɗaurawa ta fara masifa"to dole ne na ce ba na so, ba na so ko,ka ji jaraba" nufar ta ya ke ta na ja baya, "wallahi yau ko za ki mutu sai nayi"
Kokawa su ka fara tun daga toilet ɗin ya samu nasarar cire towel ɗin, ɗaukota ya yi cak, ya ɗora ta a gado, miƙewa ta ke ƙoƙarin yi,ya gwada mata ƙarfi danneta ya yi, ya fara samawa kansa satisfying da ita, gajiya ta yi da shure-shuren ta ƙyale shi, amma sai zaginsa ta ke yi, ko  ajikinsa aikinsa kawai ya ke yi, sai da ya ji ya fitar da duk wani abu da yake damunsa a cikinsa,sannan ya barta kwance ta na ta kuka da Allah ya isa.

Ko kallonta baiyi ba ya miƙe yace"Allah ya yi miki albarka, ya shirya min ke" ya nufi bayi, tsaftace jikinsa ya yi sai farinciki ya ke, ya fito ya ganta ta na nan kwance ta na kukanta, yace" to wai kukan na me ne ne, Ummu Ansar, kuma aunty'n Humaira naga abun nan ba wai ni kaɗai na ji daɗin ba ko"
Hayayyaƙo masa ta yi, to cewa nayi dole sai kayi, iye mutum sai jarabar tsiya" bai ƙara tankawa ba, ya ci gaba da shirinsa, wayarsa ce ta yi ringing ganin Oga M.D ne ya sa ya amsa " na ɗauko,ina hanya"
Daga can aka yi magana yace "okay,okay sorry sir" sannan ya kashe wayar.

"Yanzu haka zan koma babu abinda za ki ba ni naci" Ibrahim ya faɗa ya na ɓalle lence ɗin hannun rigar kayan da ya sauya.
Da masifa tace" me zan baka banda wanda ka ci yanzu mtswww ta ja uban tsaki, sai harararsa ta ke yi" dariya ya sa ya na ɗaga mata hannu " see you sweetie" ya ficek ya koma Office ya na jinsa fresh.

Duk abin nan da ya ke faruwa MIJIN DARE na gani, ya samu nasara akan Khaleesat amma ya kasa samon galaba akan Ibrahim, duk yanda ya so ya ji ya tsani Matar tasa, su dinga faɗa tsakaninsu abun ya gagara.
Sa bo da Ibrahim mutum ne mai tsananin ibada, baya wasa da addu'a.

Sai da ta gama tsine masa, sannan ta je tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallar azahar, jin yanayinta ya sauya tasan Ansar ya tashi, ta na shirin tashi taji Humaira ta na bugu, zuwa ta yi ta buɗe ƙofar, idanunta jajir alamar ta ci kuka, Humaira tace" aunty me ne ne ya sami idonki?"
Yaƙe tayi tace" bacci nayi ne sai kuma na yi wanka, shine na sa sabulu ban kula ba, ya tashi ko?"
Humaira tace"sannu" ta na kwance goyon Ansar ta bawa Mamansa.

Ki shigo mana" Khaleesat ta faɗa, kai Humaira ta girgiza alamar a'a tace" lokacin islamiyya ya kusa zanje in shirya ne"
okay ina zuwa, komawa Khaleesat tayi ta ɗauko mata allbutter biscuits guda biyu tace "ga shi nagode"Humaira ta karɓa tayi mata godiya ta tafi. Kulle ƙofar ta yi, ta zauna a parlour ta na bawa Ansar nono, idan ta tuno Ubansa sai ta gallawa jaririn harara, ƙarshe ma cire masa nonon tayi ta ce"ba za ka sha ba, Ubanka ya ja maka" Yaron da ya ke mai haƙuri ne haka ya yi shiru ya na ta kalle-kalkensa.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now