27/28

91 0 0
                                    

Baba Ayuba ya gyara zama kamar wani sarki ya ce" ai wani bawan Allah ne ya ga yanda nake ta wahala da kayan gwarin nan, shi ne ya sama min aiki a ma'aikatarsu wai zan dinga aike a cikin maaikatar,kuma za'a biyani albashi duk ƙarshen wata, sai dai fa babu yawa kuɗin, ato dan kar ki sa ma rai za ki samu ƙari dan ƙila ma kayan miyan ya fi kawo kuɗi"ya faɗa ya na ɗauke kansa Umma ta ce" to Allah ya taimaka Malam ya sa hanyar arzikin mu ne" Baba ya ce "ameen, ɗan sa min ruwa in watsa jikina duk ƙaiƙayi ya ke min" Umma ta amsa da to ta na tashi, ta  zuba masa ruwan ta kai bayi,Inteesar ce ta shigo da sallama, Baba Ayuba na ganinta ya ji wani takaici ya lulluɓe shi,take ya hauta da faɗa "ke dai wannan yarinya anyi gantalalliya daga gidan ubanwa kike da daddaren nan?" Inteesar ta ce " gidan Firdausi na je fa kuma na faɗa maka  Baba" hannu Baba ya dunƙule ya ɗora a saman lip ya ce"kai,yanzu ke dan Allah a gidan ƙanwarta ki kika share gindi kika zauna ko kunya ba ki ji ba,ki na Ya matsayin uwarsu amma ke dai anyi mara zuciya wallahi,a haka dai duk yawon har yanzu ba ki samu Mijin ba mtswww ni dai wannan baƙin jinin wallahi ba a dangina ba ne,can kika ɗebo shi dan ni kaf zuri'ar gidanmu shekara sha uku ake aure ke kuwa yanzu sai dai ayi miki fatan komawa ga Allah, dan ganinki ma ƙaramin takaici ya ke"
Inteesar ta tura baki gaba ta shige ɗakinta,ta na ƙunƙuni,Umma ta ce" ni kam wannan gori na Malam har mamaki ya ke ba ni, Allah ka bawa ƴarnan miji ta huta dai"
Inteesar ce ta fito ta ce" suna gaishe ku"
Umma ta ce"fatan dai duk ƙalau su ke" Inteesar ta yi shiru ba ta amsa ba.

Irfan ne ya shigo dan yau gaba ɗaya bai je sch ba,Baba ya ce"yauwa Irfan zo nan,ka na ji na ko na samu aiki a kamfani shi ne yanzu nake shawarar mai zai hana ka zauna min a wajen kayan miyan nan inya so da yamma idan mun tashi sai na karɓe ka zuwa dare" ya na rufe baki Umma ta karɓe "tabdi yaron da ya ke karatu za ka ce ya zauna maka wallahi ba zai yuyuba sai dai a haƙura da aikin" Baba da ya san tunda Umma ta ce haka to kuwa ba mai zama masa,ya ce"to ai shikenan dama dan wa nake yi,ba ku ba to idan akwai in baku ku ci idan babu sai kowa ya haƙura"
Taɓe baki Inteesar ta yi sannan ta ce" Allah ya sauwaƙe"ta koma ɗakinta ta ɗauki waya ta fara danne -dannenta"mtsww yanzu wai ko ƴar touch ɗin nan ba ni da ita ƙawaye duk ana ta abubuwa a waya ni kuwa babu kai talauci bai yi ba" Sai ta juya ta na ƙwafa.
Irfan da ya ke karatu ya takurawa aljanin Inteesar, tsoron yaron ya ke matuƙa, shi bai ma san abunda ke faruwa ba.

kashegari Baba na fitowa ya haɗu da Haidar, a ƙofar gida ya dawo daga morning training,gaisawa su ka yi Baba ya ce " angode da hidima ai naji ance duk abinda aka kashe na asibiti kai ne ka bayar, ni da na ce a ranta min ɗari biyar sai naji ance kyauta ka ba yar angode" Haidar ya ce" babu komai ai yiwa kai ne" ya wuce dan yasan halin Baba da zance sakaka.

Bayan  sati ɗaya,Baba ya na ta lissafin zuwa aiki company,kowa ya san zai samu aiki,har masu zuwa siyayya ya faɗa musu ce war ai ya kusa daina siyar da kayan miya aiki zai yi a babbar ma'aikata, sai murna ake masa.

Gidan Alhaji Yakub kuwa,  Amaryarsa Haj.Abida ce ta haihu, wannan ce haihuwa ta biyar sai yanzu ta sami ƴa mace, murna a wajenta kamar me, ƴaƴanta huɗu duk maza,Muzammil,Lukman,Umar,Yahaya. Uwargidansa Haj.Zainab sai hidima ta ke yi dan kowacce ta iya takunta babu wacce ta ke nuna kishinta a fili.

Umma da Inteesar ne su ka zo barka,kamar anga kashi haka aka yi musu kallon banza, zama su ka yi a parlor su ka gaisa, duk ƴanmatan gidan su ka fice aka barsu su kaɗai, maijegon kuwa ko fitowa ba ta yi ba, ta aika aka kai musu ƴar wai bacci ta ke yi, Hajiya Zainab ta ce"oh Inteesar har yanzu dai shiru, ba wani labari ko" Umma ta ce"muna dai sa rai insha Allahu" Hajiya Zainab ta ce"gaskiya Laure dole ki tashi tsaye ba wai zama za ki yi ba, ki ne ma mata maganin farinjini duk ƙannenta fa sun yi aure,tare mu ka yi goyonsu da Amina fa,yanzu Amina fa ƴaƴanta shida, gaskiya ki miƙe a to"
Umma ta ce "to Hajiya zamu nema angode" Inteesar da ta gama shaƙa ta ɗauki jakarta ta ce "umma ta shi mu tafi" Hajiya Zainab ta ce"ke kar ki min fitsara dan ana so a taimake ki, ko Ubanki bai isa ya yi min ba bare ke ƴar cikinsa"
Babban ɗanta Sunusi ne ya shigo ya gaishe da Umma ya wuce.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now