*بسم الله الرحمن الرحيم*
F~Page 3/4
______Tunda Baba ya kasa kayan miyansa ya zauna ya na tunanin yanda zai yi da Inteesar abun ka da Fulanin Daji ba wani ilimin muhammadiyya bare ya yi tawakkali, "Baba tsoho a ba ni kabewa" wata Mata ta faɗa wacce ba ta fi sa'ar Firdausi ba, ɗaure da goyonta, ga kuma wani a hannunta.
"to ta nawa" Baba Ayuba ya faɗa
" zu ba min ta hamsin"
Zuba mata ya yi ya miƙa mata,kuɗinsa ta ba shi ta ce" shige mu je" ta riƙo Yaron su ka tafi.
"yanzu ga wannan Matar da gani bata fi sa'ar Firdausi ba,amma ga Yaronta ya girma, mtswww wannan baƙin jini na Inteesar ya yi yawa,wallahi duk wanda ya zo, ko mara hankali ne ba shi zanyi na huta"
Hangota ya yi kamar ko da yaushe ta sha make-up ɗinta, ta na taku one by one.
baƙinciki ne ya cika masa zuciya, ya ɗauke kansa.Rumfar Mahaifin nata ta nufa, sannu da kasuwa Baba" ta faɗa ta na marairaicewa, "to meye kuma ke ni banyi ko sisi ba bare ki ce, Inna ta aiko a ba da kuɗin cefa ne, ruɓaɓɓun kayan miya ya fara haɗa mata attaruhu,albasa,tumatir da yayin salad.
"Baba ba kayan miya zan karɓa ba, daman Hafsat ce ta haihu yau ne suna, shine Inna tace" ka ba ni kuɗin mota in wakilceta, tunda ba ta da lafiya, idan ba ta je ba, ba daɗi tunda maƙota ne Baba Hadiza ba za taji daɗi ba"
"to radio uwar zuba, ni ba ni da ko sisi,ai ba dole ba ne ki haƙura da zuwan mana mtswww ji be ki, ko kare bai taɓa zuwa ba,bare ɗan mutum"
Cuno baki tayi ta na ƙananun maganganu.
Halinta ne rashin kunya, juyawa ta yi ta koma gida dan sanarwa Innarta Laure(Umma), " Wallahi ko da bashi sai naje" ji tayi kamar wani Saurayi na bayanta da sauri ta juya taga wayam ba kowa, mtswww ta ja tsaki.Duk abinda taka MIJIN DARE na tare da ita, duk wani fitsara da rashin son ibada da taimakonsa take duk wannan abun.
Har ta isa gida tana jin haushin hanata kuɗin da Baba ya yi.
"Assalamu alaikum, to ya ce ko sisi baiyi ba" ta faɗa a lokaci ɗaya. "wa'alekummussalamu, to ai shikenan, Babanku ba ya kyauta min ni ban je ba ke baki je ba ai ba daɗi, duk rabin hidimar bikin Hafsat a gidansu aka yi, katangarsu ɗaya da gidansu Hafsan.Irfan ne ya shigo, hannunsa riƙe da file na credential ɗinsa, Yaronk ya na da son karatu da kansa ya ke ta ƙoƙarin inganta rayuwarsa da ta ƙannensa masu tasowa.
"Umma lafiya naganku haka?"
"ni da Babanku ne yau sunan Hafsat ya ce baza ni ba, na tura Yayarku ya ba ta kuɗin abun hawa, ya ce ba shi da ko sisi"wanda ake kira da Irfan yace" to dole ne a haƙura mana, ba ance gida za'a tawo da ita wanka ba idan ta zo kwaje mata barkan"
"to ɗan rainin hankali baj za'a haƙuran ba, ka na tafiya wuya uwa mariƙar lema mtswww" Inteesar ta faɗa ta na jin haushin ƙanin nata.
Kuɗi ya ɗauko a aljihunsa ƴan ɗari da hansim-hamsin har da su biyar-biyar yace"kinga ni wallahi ba zan bayar ba"
Umma ce ta hau lallaɓashi, da ƙyar ya ba da ɗari biyu, ya wuce ɗakinsa wanda yake mai ƙofar langa-langa, sai ya durƙusa ya ke shiga ɗakin.Da murna Umma ta bawa Inteesar tace" ma za ki shiga, Allah ya sa ba'a tafi ba" to ta amsa ta na shiga ɗakinta ta ƙara shafa powder ta kuma jujjuya jiki ta fito, "na tafi"
" to ki mata barka, kafin ta iso, na shiga" (gare ku iyaye a duk lokacin da yaranku za su fita, ku dinga yi musu addu'a tare da tunasar da su addu'ar fita daga gida, idan ba su iya ba, ki na faɗa, su na faɗa har su iya da kansu).
Gidan kuwa cike yake da ɗan zuwa gidan suna, a yangace Inteesar ta shiga gidan, Yaya Haidar babban ɗa a gidan ya na ciki, ya kawo Matar Uban gidansa, ganin Inteesar ta shigo fuskarta kamar kullum two colour da Maza su ke ganinta, dan duk kyanta ba sa gani, muninta su ke gani, gaishe shi tayi, ya amsa ya na basarwa, ya fice.
"a'a Inteesar ke ce, ai kuwa Hafsa za ta ji daɗi Yayarta ta zo mata suna"
Hajiya Kursum Uwar mai jego ta faɗa da fara'a.
Haka aka tattara a ka samo mota aka tafi gidan suna.Tun kafin su isa, kiɗa ke tashi a layin,Mai jego da jaririyarta na tsakiyar fili ana ta rawa, jikin Inteesar har ɓari yake ta shiga fili, ai kuwa ta na sauka daga mota ta shige filin rawa,Mai jego na ganinta ta hau murna dan ta na sonta, a bikinta ma ita ta fidda ta kunya, yanda ta zage ta na rawa a filin wajen ba kunya ga Maza cike da kango, sosai ta burge shaiɗanun wajen.Gaisawa su ka yi aka fito da Maijego dan tarar maƙotansu.
YOU ARE READING
MIJIN DARE
AdventureLabarin ya na ɗauke da darasi mai ya wa, ƙalubale ne akan iyaye da ƴanmata masu son shanawa a rayuwa, da sakacin iyaye wajen rashin sanya ido akan motsin ƴaƴansu, da yanda Aljani yake hana aure da son raba ma'aurata da shaiɗancinsu akan bil'adama.