Ka sake ni in dai kai ɗan halak ne" Ibrahim da ya ji furuncin Khaleesat ya ce "zan nuna miki ni ɗin ɗan halak ne Khaleesat, sai kinyi danasanin wannan kalmar da kika faɗa"ya na kaiwa nan ya fice daga gidan, dan idan ya zauna zai aikata abunda ta ke so watukun su rabu,idan kuwa ya sake ta ai ta ci riba, kamar daga sama ya ga Umar abokinsa ya zo, gaba ɗaya ya manta wai zai yi rakiya zance gidansu Sadiya budurwarsa.
Da sauri Umar ya tare shi ganinsa cikin rashin nutsuwa ya riƙe shi gami da tambayar lafiya, kasa magana Ibrahim ya yi, sai huci kawai ya ke yi, ji yake ko ya koma ya sake ta ne, Umar ya ja shi cikin motarsa ya na ce masa ka ce "innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun!!!" sai yanzu ya tuna da addu'a kifa kansa ya yi ya fara maimaita kalmar, after some minutes ya fara dawowa hayyacinsa, Umar ya kafe shi da ido,ba tun yanzu ba yake karantar damuwa a fuskar abokin nasa, tun yana jiran ya sanar da shi har ya haƙura ya zuba masa ido, ruwa ya miƙa masa ya sha, sannan ya fara tambayarsa me ke faruwa, take Ibrahim ya sanar da shi irin zaman da su ke yi da Khaleesat tun bayan dawowarta daga gida, Umar ya yi shiru ya na nazari sannan ya ce"anya kuwa ba shaiɗanu ne su ke damunta ba kuwa?" da sauri Ibrahim ya girgiza kai ya ce "babu wasu shaiɗanu iskanci ne kawai irin na yarinyar nan Umar, abun da ta ke min ya yi yawa" Umar ya ce" kasan Allah na gano abun da kai baka gane ba, yanzu dai duk abun da za ta ce maka kar ka kuskura ka sake ta, zan kai ka gidan Malam Kabeeru muje mu sanar da shi halin da ake ciki, nasan zai taimaka insha Allahu"Ibrahim ya ce" ni fa ba wani aljanu kawai iskanci ne" Umar ya ce ko ma me ne ne idan muka je wajen Malam Kabeeru zai taimaka kasan dai aljani gaskiya ne kuma neman magani ma gaskiya ne ko, to ka bari mu je ɗin kawai dan nasan ya na harkar sosai" Ibrahim ya ce"to shikenan nagode abokina"Umar ya ce" yanzu a haka za ka raka ni wajen baby'n tawa?" Ibrahim ya buɗe motar ya fito ya na ce wa" babu inda zanje malam, ka yi tafiyarka kawai" dariya Umar ya yi yana ce wa" au komawa ciki za ka yi, hahhh ta ƙara haɗa maka zafi ai"Ibrahim ya yi dariya ya na shiga ciki.Khaleesat kuwa sai kuka ta ke ta na ta faman faɗi dole ka sake ni, ai ba dole ne auren ba tsabar rashin zuciya a zage ka ka nace maye kawai" a ƙasan ranta ta na son mijinta amma ta kasa daina neman ya rabu da ita, kiran sallar isha ne ya daki kunnenta hakan sai ya haifar mata da nutsuwa har ta samu damar karanta kalmar shahada,sai ta tashi da sauri ta na ɗora hannu akanta ta na danasanin abun da ta aikata yanzu nan,wanda ba ta san ta yaya take yi ba.
Ibrahim na shigowa, ko kallonta bai yi ba, ya sake alwala ya fita,tsuru-tsuru ta yi tana jin faɗuwar gaba da fargaba, a haka ta yi sallah,ta tuno da faɗar malaminsu a islamiyya lokacin da ya ke musu ƙari, inda Allah ya ke ce wa"
بسم الله الرحمن الرحيم, علاب ذكرالله تطما إن قلوب
(Da ambaton Allah zukata suke samun nutsuwa) da sauri ta ɗauko alkur'aninta wanda duk ya yi ƙura sa bo da rashin ɗauka, ta fara karantawa,Ammar na gefenta,ganin haka aljanin ya fara girgiza ya na mai jin ɗaci da baƙincikin abun da ta ke yi, sai da ta yi kusan shafi biyar sannan ta rufe kuma alhamdulillahi ta sami nutsuwa sosai,Ibrahim ya dawo zai wuce ta ta miƙe da sauri ta durƙusa a gabansa ta fara ce wa" dan Allah kayi haƙuri, ni ma bansan me ya ke damuna ba,ina ji ne a raina idan ban rabu da kai ba zan iya mutuwa bansan abun da ke damu na ba" Ibrahim kuwa ga ni ya ke ta ma raina masa hankali, tsabar rashin kunya ta gama zaginsa yanzu ta zo ta na masa ladabin ƙarya da rainin wayo, tsaki ya ja ya na mai fusge rigarsa ya wuce ɗaki, durƙushewa Khaleesat ta yi a wajen sai kuka, tamkar Ammar ya sani shi ma ya sa kuka, abu duniya duk ya isheta, (ayyah Khaleesat kin shagala da duniya ne, hattara ƴan'uwana ku sani indai muka bar Allah to Allah zai barmu, ki daure ki dinga karanta alkur'ani ko da shafi 1 ne a kullum, za ki samu salama a dukkan al'amuranki mu rage kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe ba wai mu daina ba, a'a amma dai mu rage gaskiya.)Ibrahim ya kwanta ya na auna maganar Umar da kuma abunda Khaleesat ta faɗa masa yanzu,sai ya fara tunanin ko dai Umar ya na da gaskiya akwai motsi akan Khaleesat, sai kuma ya ce kai wallahi iskanci ne da rainin hankali,za ta san ni ɗan halak ne,indai mu ka je gidan Malam ɗin kuma na san ba wata matsala gidansu za ta tafi idan ta yi hankali na dawo da ita. Sai da ta gama kukanta sannan ta shiga ɗakin, Ibrahim ya na ta baccinsa hankali kwance sa bo da tashin cikin dare da ya ke yi,shyasa ya kwanta da wuri.
YOU ARE READING
MIJIN DARE
AdventureLabarin ya na ɗauke da darasi mai ya wa, ƙalubale ne akan iyaye da ƴanmata masu son shanawa a rayuwa, da sakacin iyaye wajen rashin sanya ido akan motsin ƴaƴansu, da yanda Aljani yake hana aure da son raba ma'aurata da shaiɗancinsu akan bil'adama.