23/24

82 1 0
                                    


Ji tayi an riƙo mata hannu tare da addu'ar bismillahillazi laa ya durru ma'asmihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwassamul'aleem, an ce "aunty me ki ke yi anan ana ta nemanki?" Irfan ƙaninta ya faɗa ya na ɗagota kamar mahaukaciya ta miƙe da sauri ta ce" bacci ne ya kwashe ni, sai ka ce wata ƙaramar Yarinya me ye na ne mana kuma mtsww" Imran ya taɓe baki yasan za'a rina, gaba tayi su ka bita a baya, suna shiga Nazifa ta kira Irfan dan ji ta dawo, ya na amsawa ya ce" Yaya Nazifa ta dawo" Umma da sai kai komo take a tsakar gida taji Irfan na magana, Inteesar ta hau mita, " yanzu sa bo da Allah sai ka ce zan ɓata, ɗan fita nayi fa sai bacci ya kamani, kuma kunsan a cikin maganunguna na akwai mai sa bacci" Umma ta ce"kinsan da hakan kika fi ce ƴar nema, wanda ba'a mata abun kirki duk kin ta da mana da hankali" Inteesar ta yi shiru ta na nufan ɗakinta dan kanta ciwo ya ke mata sosai, shirin wanka ta yi, ta fito ta ɗauki kwandon sabulunsu Na'ima ganin su ma babu ya ƙare ya sa ta ja uban tsaki ta na ce wa" anan ma babu sabulun" Imran da ya siyo da yamma Yaya Irfan  ya aike shi dan ya yi wanka, wankan da baiyi ba su ka tafi nema,  sabulun Imran ya bata, ta karɓa ta ja ruwa ta shiga bayi wanka.
Har ta manta da mafarkin da tayi a ƙarƙashin tsamiya.

Baba ne ya yi gyaran murya haɗi da sallama ya shigo "uhm,uhm assalamu alaikum" sannu da zuwa duk suka hau yi masa ya na amsawa da "yauwa, ya naganku haka, lafiya?"
Umma ta ce"humm Malam yau ai munga tashin hankali Inteesar ce ta fita tun da Nazifa ta zo har ta tafi ba mu ganta ba, shi ne hankali ya tashi, sai yanzu nan su Irfan su ka gano ta"
Baba ya ce"au, au abunda kuma za ta farayi kenan, yawo dan ta ɗauko min magana a gari,to ba ta isa ba wallahi, taƙi aure duk da kallon da mutane su ke min na ganin na sata a gaba naƙi aurar da ita, shi ne zata ƙaramin da ɗauko min magana" Umma ta ce"kai fa Malam matsalarka kenan ka tambaya ka ji ina ta je mana, amma ka hau zance" da hayayyaƙowa ya ce" in tambayi me iye Laure, ai tafi kowa sanin inda ta je,ni da ta sani ma bata dawo ba wallahi kawai ince ta ɓata an nemeta an rasa nima na huta" Inteesar da abun ya yi mata ciwo ta zauna a bayi ta dinga kuka ta na jin dama ta mutu ta huta da wannan rashin auren da bata san ranar da zata yi shi ba, sai da tayi mai isarta sannan ta fito, ko sannu da zuwan ƙin yi wa Baban ta yi ta wuce ɗakinta ta shirya, Na'ima ta kawo mata abincin da Nazifa ta kawo musu, ta ce"aunty ga abinci ki yi haƙuri kinji ina miki addu'a duk lokacin da nayi sallah kuma har a makaranta ma ina yi miki......Fita ki bani guri ko inci Ubanki anan shegiyar Yarinya sai iyayin tsiya" Inteesar ta faɗa ta na nuna wa Na'ima hanya, fita ta yi cikin sanyin jiki, ta na ƙunƙunan "ita aunty'n nan ba'a mata abun kirki, Allah ya ƙara ma da Baba ya ke yi mata faɗa" ta faɗa dan taji haushin abinda aunty nasu tayi mata.

Irfan da Imran su na masallaci har tara su na sauraren wa'azin da liman ya ke yi akan muhimmancin zumunchi,da son juna a hanya su ka tawo da dafaffiyar gyaɗa ta ɗari da hamsin dan su ci tare da su Salma kafin su kwanta bacci, kowa ya na tsakar gida Baba ya na kan tabarmarsa Umma da su Salma ma suna tasu a zaune suna jin radio da Baba ya kunna, su Irfan su ka shigo  a kusa da Umma duk su ka zauna bayan sunyi mata sannu da gida tayi musu andawo,to yau akan me akayi wa'azin Umma ta tambaya dan tana ƙaruwa sosai, gyaɗar Imran ya ajiye musu sannan ya shiga bata labarin yanda wa'azin yake, Baba ya na ganin leda ya tashi daga kishingiɗen da ya ke ya ce" ke Salma miƙo min wannan ledar" Umma ta yi saurin ɗauke ledar ta ce" akan wana dalili yara su siyo abu dan kowa ya ci ka wani ce a miƙo maka ko kunya babu" ta buɗe ledar ta kasa ta bawa kowa nasa har Inteesar da ke zaman ɗaki, Baba da ya san ba shi da gaskiya ya yi shiru ya ci gaba da jin radio'nsa, Umma ta ajiye masa na shi kason, haka ya sa hannu ya ɗauka ya hau ɓarewa ya na ci, Salma ce ta shiga ɗakin Inteesar ta kai mata.Kamar wata mumina ta na zaune a takure ta haɗa kai da guiwa tana ta tunanin banza da wofi babu abinda ta ke ji a ranta illah zallar ƙunci da baƙinciki, Salma ta ce "ga gyaɗa" ta ajiye mata a kusa da ita ta fito dan tunda ta taso tasan halin aunty shi ya sa ba ta wani shiga sabgarta.

Irfan ne ya ƙarawa su Salma da Na'ima ya zama saura ƴan ƙwayayyaki a hannunsa, bayan sun gama ci ne, dake Imran ya na fita ya ɗanyi hira da abokai ya fita dan ya rage dare,shi kuwa Irfan ɗakinsa ya shige bayan ya yi wa iyayen nasa  sai da safe, kwana biyu bai karanta baƙara ba, sanin cewa maganin shaiɗanu ce,muddin ana karanta ta a gida sai shaiɗanun da ke gida sun fi ce, kuma ba za su ƙara zama ba har sai anyi wata kafin su dawo(mai zai hana mu yawaita karantata a cikin gidajenmu) ya ɗauko ya fara karantawa hankali kwance, da ke dare ne sai ya sassauta muryarsa ya na yi cikin kira'a mai daɗi,har ya yi fin rabi sannan ya yi addu'a ciki kuwa har da nemawa  Inteesar Miji na gari, sannan ya kaɗe shimfiɗarsa ya kwanta bacci, dan sammako zai yi,akwai aikin kwashe yashi da za su yi, shi da Abulhakam abokinsa, dan tare su ke aikin ƙarfi duk week end, idan an samu, kwanciya ya yi sai bacci dan a gajiye ya ke.

MIJIN DAREWhere stories live. Discover now