AYSAM
Love,passion,hatred,betrayals and power.
By Fatoums Passion.
This whole chapter is dedicated to my two lovely friends Aminatu Nura Leko and Amina Abdullahi Yahya,jinjina tamusamman gareku akan irin gudun mawar dakuke bayarwa gurin ganin littafin AYSAM yatafi kmr yajja ake buqata tahanyar qarfafa mun gwiwa.Allah yabar xumunci,ameen.
Chapter 11
(The gambler)
Sameer ne kwance tsakiyar gadon madaidaici yana kallon screen din wayarsa video call sukeyi shida Ammi amma haka kawai yaji zuciyar sa badadi kmr faduwar gaba yake taji daga qarshema kasa qarasa mgnr yay,saida safe yamata yana kashe wayar yakalli agogo qarfe 11:30pm yakalli gefen dakin susu biyune adakin nasu na hostel mamaki ne yake cikashi akullum Samar be shigowa sai after twelve satinsa daya kenan a Abuja amma duk kewar gida ta isheshi da tsohuwar makarantar sa,
don a irin wnn lokacin almost dukkansu suna sauka garden din makaranta don yin karatu musamman in akace ankusa exam kuma su duk inda takwas take anrufe hostel dinsu bame sake fita sai saida safe duk wanda kwa yayi dare saiya dau penalty mexafi,amma yaga yawanci ko maqotansu har tsakar dare suna kaiwa awaje ko Ina suke xuwa oho,
yana cikin wnn tinanin yajiyo bude qofar Samar yana waya yace
" OK Daddy"
da alama waya yake da mahaifinsa,
yace
"Daddy tundaxu dana fita xanfada masa tam,"
yakatse wayar tareda jan dogon numfashi yakalli Sameer wanda ke kwance daga shi sai boxer's daman ko agida baya qaunar kwana da complete clothes koda pajamas ne kuwa baya qaunar kwanciya da cikakken kaya,
Yace
" S fulani bakai bacci ba"
dagowa yay yana daga masa kai yanaso yasan Ina yake xuwa duk dare amma kuma yasan shiba mutum bane meshiga hurumin mutane
"Ina tareda Lilly"
yafada ataqaice kafin yanufo gadon Sameer din yace
" tayi offering xata ringa te makamin tana koyamim yajja ake analyzing data din weather nikuma xanringa koyamata lissafi duk dare daga gidansu nake,"
Sameer cikin ko inkula yace
" and so"
duka Samar yakaimasa cikin wasa yakauce yana dan sakin murmushi
"naga kanamin kallon tuhuma ne shiyasa karkai tinanin clubbing nakeyi each night kaima kamar yajja sauran keyi Ina boyewa ne sbd Lilly batasan kowa yasan She's very weak in math koda yaushe dimple kexana mata jarrabawar ta wanda take matuqar tsoron kar Abuya dinta yasani",
jinjina kai Sameer yay yana furta
" you and her are pretty close"
Yace
" yah Lilly and I nikaina bansan sanda muka xama haka ba she's nice gurl get to know her man harda sauran3 dinma kawai dai xaka dan shawiya saboda dukkansu gigin teen age kefuxgarsu sunajin kansu dayawa amman yaran kirkine sosai,"
Juyawa Sameer yay yakashe wuta gefen gadonsa yanajan blanket alamar bayason maganar Samar,
cikin yan kwanakinnan yagama karantar halayen Sameer xaka dauka shi mutum ne maigirman kai da jiji dakai amma bashida kodaya cikin wnn dabi'un shi mutum ne miskili wanda bayason shiga abinda beshafeshi,mutum neshi wanda ke kaffa kaffa da takatsantsan da rayuwarsa musamman daya taso yana tareda yaran masu shi hakan besa yamanta da shidin wayeba yana jan mutuncinshi matuqa shiyasa ko mutum ya girmeshi xakaga yana respecting din Sameer sbd shima yana ganin girman kowa.
"Aysha"
Sameer yafurta aqasan labbansa kafin ya gimtse idonshi yana kore duk wani tinaninta dake bijiromasa aransa.
Qarfe shida darabi daidai suka fito daga masallacin dake babbar makarantar Sameer da Samar sanye suke da jallabiya doguwa faraqal suna tafe sunajin dadin iskar bishiyun dake kadawa Samar kefurta
"Man fresh air yayi kaikaji wani dadi dana keji"
Sameer murmushi yay don wnn weather din tana kawomasa wani irin dadi da shauqi wanda yake matuqar qauna,
motoci suka hango qofar katafaran asibitin IMPERIAL din wanda basuganiba ahanyarsu taxuwaba don batanan suka biyo ba gurin hasken fitila ya haskakashi duk da har lokacin gari begama washewaba,
Samar yace
"wow Sam kaga wasu xafafan motoci wnn mutum daya nasan yana hawan irinsu"
yafada yana tunkarar gurin dasauri Sameer yariqoshi yana furta
" inaxaka kadaisan xamu shiga gym center kafin mukoma ko"
yace
"man motocinnan natabbata na AJ ne toh meyake yi asibiti awannan lokaci" berufe bakiba yahango escorts dinsa sunfito daga hospital din sun xagaye gurin daga qarshe saiga shinan rungume yake dawata yarirriqo tadora kanta aqirjinsa kmr wata jinjira aka bude murfin motar cikin axama Samar yanufo inda suke ,
Alh AJ yacewa driver yasauke glasses din motar don fresh air dimple kebuqata awannan lokacin yasata amotar,
Sam yana tadaya bangaren yana kallon kyakkyawan dattijon wanda yay masa matuqar kwarjini baya iya hango fuskar yarinyar sbd gashinta dayarufe fuskar ruf kmr alh AJ yasan meyake tinani kuwa yay baya da gashin nata mematuqar tsayi da santsi yana shafa fuskarta, mamaki ne fal cikin xuciyar Sameer toh meyasameta Samar neyake furta
"Good morning Sir "
yana sunkuyar dakai fitowa yay batareda yarufe murfin motarba yace
"Morning Samar "
Yace
"Sir dafatan dai lapia ko,naga kamar dimple........uhm meyasameta"
yatambaya cike da kulawa da diriricewa sbd tsananin kwarjinin da alh AJ kemasa
Yace
" don't worry she's OK now "
yana shigewa motar sbd bashida lokacin tsayawa amsa tambayoyi awannan sa'in Allah Allah kawai yake suje gida tasamu ta kwanta tahuta,
itakuma dimple dake jin duk abinda ke faruwa ahankali tabude idonta tana lumshewa ta daya bangaren lokacinda AJ yashigo motar yajawota jikinshi yakwantar Sameer take iya kalla kadai agurin shima itan yake kalla cike da son jin meyasameta domin jiya lafiyarta klau har aka tashi.
Tashin qurar motocinsu yasaka shi dawowa hayyacinsa lokacinda Samar yadan tabashi da alama ma besan yaqaraso ba, yace
" man muje ko,"
Dogon numfashi yaja tareda furta
' is she OK"ni fatima nace my two aminene's kuji gulma irin na S fulani
Yace
"she'll be fine karka damu indai Aysha ce she's always sick"
Kalmar qarshe dayafada yadaure masa kai taya xa'ace mutum kullum cikin rashin lapia yanason yaji qarin bayani amma ganin Samar yayi gaba yasaka kawai yaja bakinsa yay shiru suka wuce.
Lilly,meemee and meenah ne on video call suna tambayar juna yasuke,meenah kefurta
"kunga gurl dinnan tanacan tana mayan baccin nnan nata ko daga kiran bataiba ko,"
Lilly tace
" dimpy dabarci nima tunsafe nake nemanta awaya bata dagawa,"
meemee tace
"anya kwa lapia muka jita shiru"
Lilly kefurta
"inkun gama ku wuce school kawai nixan biya ta Villa din nasu intasota gaba" dariya sukai kafin su kashe kiran duka da na'am da shawarar Lilly data kawo.
Ahankali take bude idanuwanta suka sauka akan popsy wanda kekan sofa yana duba wasu takardu yaya muhsin ne agefenshi yayi tsuru irin na marasa gaskiyar nan yaudin xatace tamanta rabon da taga dan uwannata sbd basa haduwa kwata kwata shidin dabanne akaf yayan gidansu bedamu da kwana agida ba sannan baruwanshi da harkar qannenshi suma baruwansu dashi,
ahankali tatashi xaune tanafurta
Popsy"
Dagowa yay cike da jindadi yamiqe yaqaraso inda takeyana furta
"my child kinfarka yajikin naki meyake miki ciwo lemme call doc sahara,"
riqo hannun satai lokacinda yaqaraso inda take ta qaqalo murmushi tana furta "popsy banaso ,tsayawa yay yana kallonta" tace
" banason inringa ganin kuna fada kaida ummin muhsin"
rungumeta yay tsam ajikinshi yana jin wani dadi har cikin ransa muhsin kuwa galala yatsaya yana kallonsa don xe'iya cewa abu daya ne aduniya ke rikita nutsuwar alh AJ, Aysha, shidin mutumne jajirtacce akan komai banda Aysha his very weak indai maganar yarinyar ce"
Cikin kulawa AJ yace
"I promise baxamu qara fada ba kema kiyi min alqawari you'll never be this weak again,'
dagowa daga jikinshi tai tana murmushi hannunta cikin nasa take furta
"popsy kamanta sunane a super hero party I'm a thunder woman "
tafada tana daga masa kwanjinta daya wai yaga muscle dinta dariya yay yana kallon dan qaramin damtsen nata yay peck din forehead dinta,muhsin ganin su ahaka yasa yatabe baki yanajin kishin soyayyar dayakema dimple har qasan ransa yamiqe yana furta
"sannu ko dimple Allah yasa kafarane,"
Tadago tana furta
" Ameen yaya"
Cikin jin dadin kulawar da muhsin yanuna gareta yake furta
"xansaka PA yaturo maka kudin karka damu"
Smiling muhsin yay yana furta
" OK Sir"
yafice adakin,
yana meraya rashin lapiar yarinyar nan yatemaka masa inda badan hakaba aiyasha tambayoyi kafin yasamu kudinnan yaxama dolene shiyasa yadawo gida don yasamu yadawo da motarsa da flat din dayake xaune ciki da yarasa a gambling, sashen mahaifiyarsa yanufa yana dan yamutse fuska don yay kalar tausayi tayajja xatai saurin bashi kudin dayake buqata, a living room yaxauna me aiki taje tasanar da ita xuwan Mr muhsin cikin farinciki suka fito tareda hudallah don tana tareda ita a kitchen suna girki,
Cikin kulawa take furta
"oyoyo ga babban yaya yadawo,"
Beyi mamakin ganeshi dame aikitai ba hartaje tafada musu duk da tsananin kamannin dasukeyi da tagwaininsa MUHASSIN,hada muhsin da muhassin kmr sama daqasa ne MUHASSIN mutum ne kamili wanda yake kiyaye komai nacikin rayuwa da addininsa wanda yake mahimman ta family dinsa sama dakomai sabanin muhsin wanda tun tasowarsa yake biyewa yaran masu kudi muhsin baya cikakken wata aqasar naija tunda yagama karatun sa baya aikin fari bare baqi bakamar muhassin ba wanda keda matsayin CEO nadaya daga cikin manyan matatun manfetur mallakin mahaifinsa AJ, yana aiki tuquru don ganin ya temakama mahaifinsa yasamu nakansa shikwa muhsin kam dakyar yakammala degree dinsa sbd shashancin da yasaka agaba na shaye shaye da gambling, kullum yana casino da friends dinsa abunda babu ruwansa dashi guda dayane mata impact yace sunan mace yaji anfurta amai yakeji sbd bayason su kwata kwata sakamakon irin axabtuwar dayay narashin kulawar mahaifiya lokacin da yafi kowa buqatarta tajefar dasu takama gabanta sanadin wnn damuwa abokansa a boarding school suka fara koya masa shaye shaye hakan yajawo qara tabarbarewar lamarin muhsin wanda ada Alh ke kaffa kaffa da rayuwarsa yana qaunar muhsin matuqa wanda ko sauran yayansa sunsan dahaka haihuwar dimple yasa Alh yinnisa da muhsin sbd kulawar da take buqata muhsin ya xamana bayada wanda xeyi sharing problem dashi domin shida MUHASSIN ko maganar kirki bayi sukeba sbd yana ganin cewa muhsin yay nisa baya jinkira.
"Barka da xuwa son", doctor bint tafada tana murmushi kafin tace
"lapia kuwa naganka dasassafe karkacemin AJ ne yatasoka don yar lelensa tasuma jiya"
Yace
"ah'a badaya ummi naxone gurinki dama kuma sena tarar da cewar dimple ba lafiya,"
Tace
" OK mekakeso"
tambayar datai masa kenan yana mamakin halin ko inkula irin na mahaifiyarsu memakon ta tambayeshi ya yake koya jikin dimple wanda Yatabbatar har xuwa yanxun bataje tadubata take cewa meyake so
Dogon numafashi yaja kafin yace
"daman inason kibani wasu yan kudadene xanfara harka a new York tareda doc Arsal Noor kuma banida jari shine nace koxaki bani in ya so innafara akasamu alheri saina ciremiki kudinki nabaki,"
murmushi tai kafin tace
"muhsin kenan wancan karanma haka kamin dadin baki nakwashe duk yan kuda dena nabaka katafi ka asarantar dasu a gambling,narantse da Allah sisina bakaci yaudinnan sbd haka xaka iya komawa inda kafito shi ubannaka dayakeji yayansa sunfiye masa kowa aduniya yabaka nasa kudin badai niba, nima yar marainiya ta nake tarawa tasamu rayuwa mekyau nangaba kobana numafashi"
tafada tana kallon hudallah wacca tai qasa dakanta kafin tadago tana furta "don Allah ummi kidena cewa haka nidasu duk fa yayankine kibashi mana dan Allah tafada cike da marairaicewa' tace
"saidai fa kiyi sbd muhsin baxe maidani bankin cirar kudinsa akoda yaushe kuma in kyaleshi baxe yiwu ba".
Muhsin dagowa yay yana kallon hudallah wacca kaf cikin yan uwansa bawanda yake qauna yake bawa kulawa tamusamman kmr ta sbd hudallah ke damuwa da damuwarsa,hudallah yarinya ce mehankali wacca tasan yakamata bakamar waccan shedaniyar yarinyar ba mekama da aljanu haka yake ambaton dimple dashi yawancin lokuta,
duk qarshen wata kowana da dake cikin gidan Alh AJ najin alert me nauyi a account dinsa bayan haka sukansamu allowance sati sati idan company yasamu riba kasancewar kowa yanada hannun jari harda hudallah a AJ group of companies.
Wannan kudin kowa kanyi buqatun kansa dashi harma inya qare kana iya neman qari amma da sharadin se kafadi mexakai dashi,account dinkowa dai masha Allah yana isarsa banda muhsin wanda ko sati baya rufawa yake caca danasa kudin a casino don yatattara rayuwarsa kacokam yakoma NYC dasunan xeriqe babban kamfanin alh na sarrafa na'ura mai kwakwalwa amma in anga muhsin gun aiki toh lalitarsa ce taqare yake buqatar wani.
Fitowa yayi, hudallah tabiyo shi abaya tana furta
"ya muhsin nawa kake buqata inada kudi a account dina kuma balefi dayawa xan iya bakasu"
yajiyo yawatsa mata shanyayyun idanunsa da dama kalarsu ce haka sakamakon kamanni da mahaifinsa dayake mugunyi,
yace
"hudallah kibarshi kawai nayi convincing popsy, kuma natabbata xesaka min kawai dama xanhada biyu ne kuma tun ahanya naji araina ummi baxata bani kudinta ba sbd susu kadaine abinda take qauna aduniya,"
riqe masa hannu hudallah tai ahankali tana furta
"ya muhsin kadena fadar haka,ummi nasonka sosai bata taba qinka dede darana dayaba kawai dai batason gambling din dakakeyi,"
yace
" hudallah kina qoqarin karetane kawai bakisan meyafaru ba yarinyar can dimple bakisan ahalin dana tarar da ita ba,naji xafi sosai danaga popsy ne agurinta"
dasauri hudallah takatse shi tana furta meyasamu dimple din cikin damuwa yace
"oh kema bakisaniba kenan,"
yace
"duk da cewa yarinyar bata da kunya but kaso hamsin na gurbatar tarbiyyarta lefin ummi ne bata damu da itaba shikuma popsy gani yake yajja batasonta muma bama sonta hudallah inasonku yan uwana i want the best for you guy's,"
Murmushi hudallah taitana son sanja magana tace
"toh yaushe xaka koma yace daxarar natattara kudade na wnn karan bama xankoma new York city ba Cuba xan wuce"
tace
"yah muhsin cuba kuma"
cike da mamaki yace
" yah"
Tace
" toh Allah yatsare" kadaibi ahankali.
AJ ne yafito daga bangaren Aysha dede Lilly tana parking qofar flat din,cikin girmama wa tarusunar dakai tana furta "good morning popsy,'
yace
"morning Lilly,"
hudallah da muhsin ne suka qaraso gurin,
Lilly Ina makarantar?"
Alh yatambaya cikeda mamakin ganinta
dan sunkuyar dakai tai don dama Allah tasan indai tahadu dashi sai yamata fada sbd ya hanasu kashe makaranta sbd rashin lafiyar dimple don ada kan yafarga indai bata da lafiya xuwa suke su tare agidan wai sunxo jiya ba'arabi bare boko sukashe makarantar su duka,
tace
"ahm popsy daman dimple ne tunjiya ina kiranta awaya bata picking shine nace bari nabiyo naji ko lafiya"
Murmushi yay yana jinjina qaunar da Lilly dasauran yaran kewa dimple shiyasa shima yake matuqar jidasu kamar nasa don duk meson dimple shima masoyin sane, wanda yake qintakuwa gani yakeyi shima maqiyinsa ne,
Cikin farinciki yace
" karki damu Lilly jiyane kawai tashiga mild shock"
cikin tashin hankali Lilly take furta
"is she OK"
yajikin nata yanxun duk tabi tarude,yace "calm down Lilly, she's alright doctor tabata bed rest na kwana daya in sha Allah gobe xatai resuming school kinga karki rasa karatun ki kijuya kikoma,"
Tace
"popsy don Allah xanshiga inga halin datake ciki inaso naganta"
tafada cikeda marairaicewa,hudallah da muhsin suka kallo juna ganin tsagwaran damuwar dake tattare da Lilly yasa yace "toh kishiga kiganta amma karki dade don sekinje makaranta"
tagyada kai tana me masa godia tashige ciki hudallah ne taiwa Alh yame jiki kafinta shige don duba dimple din muhsin da alh kuma suka wuce bangarensa suna tattaunawa irinta da da uban da suka dade basu haduba.
Fitowar ta awanka kenan tajiyo sallamar Lilly Miss Gabby ce tafito daga closet's dinta tareda wata doguwar riga mai dan nauyi sbd yanayin xaxxabi da taji tareda dimple din juyawa tai tana kallon Lilly,dagudu taqarasa tai hugging dinta tana furta
'gurl ykk,yajikin naki you scared me kinqi daga wayan kowa,"
Miss Gabby smiling tai tana kallonsu dimple ture Lilly daga jikinta tai tana furta
"yarinyarnan naga alama karyani kikesonyi"
hawayen idanuwanta Lilly tagoge tana furta
"sannu kinji"
tace
"Lilly am fine stop crying haba babban yaya bakece kullum kike cewa kingirmeni ba yakuma kike kuka kmr baby,"
Tace
"gurl kinma dau abinwasa ko nabuge ki" tana turo baki
Itama kwatanta sad face din Lilly tai tana furta
"toh nima nabugeki"
suka qara hugging each other.
Kwankwasa qofar da akeyine yasa suka dago
Miss Gabby tatambaya
" waye?"
"Hudallah"
ce amsar da akabayar kenan wacca tasa dimple hade girar sama da taqasa kafin Miss Gabby tace
"shigo"
ahankali cikin nutsuwa hudallah tashigo tana kallon straight inda dimple take xaune daure da towel ajikinta,cikeda kulawa take furta
"sis daman naji ance bakida lafiya ne shine naxo naduba ki naga yajikin naki"
Wani irin kallo dimple take mata kafin tace
"saikuma kikaga banmutu ba inanan daraina ko'
tafada cikin daka tsawa,smiling hudallah tai tana mamakin baqar qiyayyar da yarinyarnan kemata toh maitama ta kotace meta taba mata arayu data cancanci wnn cin mutuncin daga gurinta
Tace
" i can see you are OK'
sai anjima
Tajuya tafice adakin tanajan dogon numfashi sanda tafito kafin tasaki murmushi mai ma'anoni kala kala tai wucewarta.
Tana fita dimple taja tsaki tana kallon Miss Gabby tace
"pls kar asake bari kowa yashigomun bangare har cikin master bedroom without my permission"
Kmr yajja Lilly tai alqawari kuwa saigata tashigo makaranta qarfe11 tana xuwa tatarar yan class dinsu sun shiga lab.
Aji takoma tadauki jakar meenah taduba notes din da ba'aiba tana kwafa,lap court dinshi yamanta cikin jaka hakan yasa yadawo ajin daniyar dauka,idonsa yakai kan Lilly daketa aikin kwafar note aranshi yace taxo kenan toh ina dayar dauka yay batareda da yace mata komaiba yafice warsa.
Yau ajinnasu gaba daya tsit kakeji bayan Lilly tasanarda class teacher dinsu xataiwa dimple attendance da submitting assignment yau baxata shigoba bata jin dadi hakannan Sameer yaji yanason yasan yatake don halin da yaganta daxu da asuba yatsaya masa arai sosai da irin kallon datake masa.
a ajin malamai sunfara gane baiwar da Allah yaywa Sameer ta iya lissafi da sarrafa computer hakan yasa akafara yawo dashi amakaranta ko ina malami yaje inxe basu musali sai yakwatanta da irin maida hankalin da Sameer keyi da kwakwalwarshi don ayan kwanakin nan da yagabata aji ajine ma suke xuwa kawai don anuna musu waye Sameer s fulani.
Hakan kwa yadaga hankalin dimple da squad dinta musamman dasuka samu labarin irin yajja Sameer ya iya basket ball wanda gabadaya shine center of sport na makarantar sosai abin yafara takura mata domin ko maganar kirki bata hadasu dasu,
a aji idan malami ya tambayeshi yakan tashi yabada answer wanda dalibai suka camfa s Fulani baya taba missing yayi ba dede ba har akafara kiransa dasunan Mr ITK ma'ana (I too knows) shikomai yasani shida dimple kam wani mugun competition sukeyi a aji indai daya yayi BBB answering question dayama seyayi amma tini dimple tagane cewa shayi ruwa ne sbd tana da mugun rauni kan lissafi hardarsa take kowana irine gudun karta fadi shikam Sameer indan yana lissafi cewa sukeyi kmr damacam dashi aka haifeshi ba aduniya yakoyaba,
Duk wani sunan banxan da click din dimple kefada masa yana sani sbd agabansa suke yi ba tsoransa sukejiba balle suyi bayan idonsa saidai kwarjini dayake musu dayane cewar ba yarinyar da ta isa tashiga sabgarsa wanda inkinganshi yana mgn dawani toh Samar ne mugun miskilancin shi naqara masa wani aji cikin daliban yan matan grade12th takanas suke xuwa wai sunaso yakoya musu assignment don kawai suganshi suji muryarshi me mugun xaki ahankali yake magana cikin nutsuwarda yataso da ita tun quruciya baya daga murya idan xemagana kaikace cajarsa xa'ai cikin qanqanin lokaci laika muzaffar diyar minister of finance tai proposing wa Sameer a grade 12 take tanuna niyarta nason dating dinsa agaban kowa atsakiyar makaranta abin yafaru wanda dimple tai witnessing da idonta Sameer yay rejecting dinta yace
"he's sorry shi ba soyayya yaxo yiba".
Laika yarinya ce me nutsuwa wacca takasance topper din year dinsu bata damu ba tacigaba da courting dinsa wanda hakan yasa dimple da squad dinta niyar daukar mataki sbd kmr tana xubarwa da mata aji ne agurin wanda bekaiba cewar dimple.kuji fa akace qarfin hali barawo da sallama subasa sansa basa qaunar wani yasoshi aminoni anan nakawo qarshen chapter dinnan taku wacca nayita metsayin gaske sbd nuna godiya ta abisa comments dinku akwai wadanda suma nan gaba kadan zasuji sunayensu ciki,so don't worry kowa turn dinsa zezo accept wanda suke kurame awannan group din.😂🙄,don't forget to
Comment,share
&vote.
YOU ARE READING
AYSAM
RomanceLabari akan wasu masoya biyu masa mabambamta rayuwa Aysha takasance diya daya tilo ga shahararran attijiri kuma dan boko Alh Alhassan abu jandal(AJ),tana rayuwa yajja takeso tataka uban wanda takeso sameer yakasance dan talakawa wanda yasamu scholar...