Next Life

1 0 0
                                    

AYSAM

Its Fatoums Passion's

   Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's.

    Chapter 49

(Next life)

Arsal ne yakalli driver din lilly dake tsaye gabanshi yacilla masa raf din dubu guda biyar yadauka yana yashe baki yace 

"nagode doctor,

Allah yaqara budi,"

daga masa hannu kawai yay yana masa alamar xe iya tafiya,juyawa yay yafice.


Ahankali yasaki wani murmushi yana jujjuya xoben hannunsa tinawa da yajja jikinshi yadau electricity lokacin daya riqeta yake da irin tsoron dayagani a idonta,

tabbas yafi kowa sanin irin qaunar datakewa xobennan don haka xe ajje mata shi harse lokacin daya aureta ya koyamata sansa xefito dawannan xoben amatsayin yasa anqeramata wanine baxe taba bari taseda xobennan dan taiwa maqiyinsa amfani dashiba.

wayarsace tahau ringing,

yadaga ganin sunan wacca takira yasa yaja tsaki kafin yadaga cikin wani salo yake fadin 

"rabin rai ya akayine theatre fa xanshiga,"

tace 

"daman cemaka xanyi haqarmu tacimma ruwa wadannan kudaden dakace nasamoma gurin ummi tace xata bayar amma da sharadi,"

yace 

"inajinki"

tace 

"tace duk shekara xa'aringa biyanta instead of monthly aringa hadamata ribarta guri guda gabaki daya,"

yace 

"hudallah kenan bakida matsala akan hakan kinsan bana wasa da kudi koh,"

tace 

"nasan hakan shiyasa ma nayarda dakai ka iya maida thousand million,million to billion my man,"

smiling yay yana fadin 

"albishirinki,"

tace goro yace 

"your VISA Is ready,"

tace 

"really"

yace 

"yah kasan cewar kinjima bakijeba shiyasa yadanyi wiya buh ansamu,kuma saura qiris auren aysha yaballe yanxun haka tana gidanmu,"

tace 

"gidanku kai dan Allah me yafaru kodai naxo,"

yace 

"kixo kimata me kinsan sarai lilly hates you and that gurl is smart kiringa lura da steps dinki akusa da ita,"

tace 

"ainafi kowa sanin qinda sister dinka takemin kuma haka xanxo naxama in law dinta kotaqi kotaso ba"

 hhhhhh!

 suka sheqe da dariya suduka cikin xuciyar arsal yake fadin 

"not even in your widest dream,Arsal abdulfatah mijin aysha Alhassan ne ita daya."

      Qarfe tara daidai yaqaraso imperial,

aqofar estate dinsu yatsaya yakira wayar lilly tare suka fito,

bayan aysha tasaka taimata alqawarin baxata taba gayama sameer abinda yafaru dasu ayaudin ba,

tundaga nesa ya hangota tana tafiya ahankali kmr tana qirga takunta karya yaqare,

AYSAMWhere stories live. Discover now