AYSAM
Its Fatoums Passion's
Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's.
Chapter 45
(Married couple)
Moon ce keta kici kicin jera breakfast din baffa data gama hadawa a dan madaidaicin tray din silver,
ammi tashigo kitchen din tana tambayar ta kota gama ta ansa da eh yanxun xata kawo tace mata ta ajje xatakai masa daki taje tacewa sameer yafito yaja musu ruwa arijiya tun kafin rana tagama kwallewa,
da toh kawai ta ansa mata batareda ta motsa daga inda takeba,tace
"baxaki wuce ba koh ninaje da kaina"
dan jim tai tana tsoron kada ammin tagane sameer din baya dakinsa ahankali tanufi dakin tana waiwayan ammi har tatura qofar tashige haka kawai ammi taji bata yarda da zuru zurun da idon Moon yay ba,
aranta tace
"badai yarinyar nan ce takwana adaki tareda shiba"
dasauri tadire tray din data dauka tafito afusace tanufi dakin sameer tabanka qofar amma ga mamakin ta moon tagani taxuba tagumi tana kallon qofa tadan firgita ganin ammin,
kallon dakin tai tsaf kafin tace
"ina sameer yake?
qasa Moon tai dakanta tana girgixa kai tace
"ina yaje da sassafennan ina tambayar ki kinmin shiru"
dan girgixa kai tai alamun bata saniba takasa hada ido da ammin,
ammi cikeda takaici take fadin
"ina waccan yarinyar"
wacca tasan aysha take nufi badai daukarta yay suka fice da sassafennan ba,
fita tai takoma parlor tana dauko wayarta no din sameer tasoma dialing can tajiyota tana ringing daga can dakin Moon cikin mamaki ammi tabi sautin wayar ahankali tatura qofar dakin Moon din suna tsakiyar qatifar manne jikin juna barci sukeyi hankalinsu kwance ya maqalqaleta sekace yaro meqiwa da akarabashi da mamarsa akadawo dashi.
suman tsaye tai tana kallonsu kafin tajuya tafita da dan sauri,
moon dake parlor yarfar da hannunta kawai take tsabar tsoran fadan ammi tana fitowa suka hada ido tabata wani dirty look kafin tace
" xanyi maganin ki tunda hardake ake hada baki a munafunceni algunguma kawai,"
dif tai don tasan ammi xata iya kwarfeta anan idan tatanka mata koda uffan,
cikin fada take fadin
"wllh sena yi maganinki daga kehar shi sameer din kun rainani ban isa nafadi mgn agidannan kubita ba ko sbd ga sa'arku kuma wllh nadawo naganshi adakinnan daga kehar shi sena gyarawa xama"
taqarasa tana ficewa a parlor dakanta tasoma jan ruwa arijiya tanayi tana masifa ita kadai,
moon kam da gudu taqarasa dakin badai tashiga cikiba daga bayan labule take fadin
"hamma,hamma,hamma katashi ammi ce taxo"
cikin barci sameer yajiyo muryar moon din ahankali yabude idonsa kallonsa yasauka akan kyakkyarwar babu face din aysha hannunta saqale jikinshi barci takeyi da alama yay mata dadi dan jim yay kafin yaqarajin sautin moon din tana fadin
"Hamma dagaske nake wllh, ammi taxo"
adan firgice yamiqe duk da haka seda yasamu nutsuwar janye hannunta daga bayanshi ahankali gudun kada yatasheta don yalura tanada nauyin barci miqewa yay yana kallon agogo it's almost 10 in the morning.
YOU ARE READING
AYSAM
RomanceLabari akan wasu masoya biyu masa mabambamta rayuwa Aysha takasance diya daya tilo ga shahararran attijiri kuma dan boko Alh Alhassan abu jandal(AJ),tana rayuwa yajja takeso tataka uban wanda takeso sameer yakasance dan talakawa wanda yasamu scholar...