*🫧 ZAMANIN MU A YAU🫧*
NA
JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO___________
*003*
*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️
GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA
GUDA BIYAR 1500.GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jeeddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
Halima ce ta kyara kallon
ƙawarta ta zuciyarta cike da baƙin ciki a wasu lokuta wani abu idan Maryama ta yi shi kamar ba musulma ba, haka taso takaita ta baro a shekarun baya, in banda ALLAH ya bata hankali da hangen nesa da tuni tayi sanadiyar da maigidanta ya sake ta. Wani sa'in har mamakin ƙawancensu take yi dan maryama sam ba ƙawar arziki bace ba.
"Kinga Halima idan zaki tashi tsaye ki tashi tsaye ki kakkaɓe 'yar banza yarinya daga gidanki, shine magana amma kinsani a gaba kina wani banzan tunani da inda zai kai ki, ke ga ki ba ki taɓa haifar ɗan namiji ba domin shi ne magaji uba sai tarin tulin 'ya'ya mata ga shi nan garin sakarcinki kin tsaya wata banza wacce aka haifa a tafin hannunki sai saƙin kwai-kwaye 'ya'ya maza take yi da dattijon mijinki da baya gudun abun kunya.
Mamaki ne ya ƙara kama Halima hakan yasata saurin tarar numfashin Maryama tana faɗin "A'ah Maryama 'ya'ya mata ba abin yarwa bane domin ke kanki da ki ke wannan zance mace ce kuma uwar da ta kawo ki duniya mace ce, ni ban rena ni'imar da ALLAH subhanahu wata'ala ya yi min ba. Wani yana can yana nema amma ALLAH bai bashi ba ni ya bani sai na rena ko kin taɓa gani bolar 'ya'ya mata ki kai ni na ƙara ɗebo wa na haɗa da nawa domin na fahimci duk da kasantuwar ki ta 'ya mace ba ki san girman darajar da ALLAH subhanahu wata'ala ya yi miki ba.
"Mtsssss! Babbar matsala ta dake kenan Halima da zarar an yi miki maganar so kanki sai dinga yiwa mutum guntun wa'azi ki, idan mutum bai yi hattara ba nan take za ki kafirta shi.
"Ai Maryama ba kowacce mace bace ba irinki wacce bata san inda yake mata ciwo ba, ko an gayamiki nima boko ta haukatani ne? Ke wai dan ALLAH bakya duba gidanku Malam Kabiru mahaifinki yara nawa ya haifa? "Miƙewa Maryama tayi tana dallah mata harara sannan ta ɗauki hand bag ɗinta tayi hanyar fita ba tare da ta ƙara tofa komai ba, don a duniya mahaifinta shine mutumin da bata ƙaunar a danganta ta dashi, yayi mata taɓon da ba zata iya mantawa da shi ba, shiyasa duk ƙaunarta da wuri indai aka ambaceshi dole tabar wajen. Saurin riƙo hannunta Halima tayi tana mai marairaice murya gami da faɗin "Ki yi haƙuri Maryama ba abunda kike tunani bani ba kawai dai ina ƙoƙarin tunatar dake abinda kika manta.
"Dallah Malama saƙarni kome k ikace ai ba zanyi mamaki ba, Tunda nice na taƙo har cikin gidanki, gaba idan kika ƙara ganina kiyi min abunda yafi wannan ta faɗa tana mai nufar kofar fita, Halima ta biyo ta a baya duk magiyar da take mata bata sa ta tsaya ba, a mugun fusace ta shiga motarta, da ƙarfi ta ja motar sai lokaci tunaninta ya dawo jikinta ta yaya zata ƙarbi wannan uban kuɗin a gurin Abah, Dogon murmushi kawai tayi sannan ta danna horn alamun ta ƙaraso cikin gidan, mai gadi ne yazo aguje ya buɗe mata gate, mamakin ganin uban securities a harabar gidan tayi, ta ko'ina sune wannan ya ƙara tabbatar mata da Alhaji Shema ya dawo kenan? Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, First time da Abah bai gayamata dawowar alhaji ba wannan ya ƙara tabbatar mata dacewa yayi fushi sosai da ita, murmushi tayi don tasan kome za tayi masa ba zai taɓa iya fushi da ita ba, hakan ya sata fitowa daga cikin mota cikin takonta na isa da nuna ita ce matar Abah, ta nufo entrance ɗin part ɗin su tana ƙaraso wa securities kowanne ya shiga sara mata, hakan yayi mata daɗi matuƙa dan haka taji kanta ya ƙara girma. Directly sai tayi part ɗinta don bata shirya magana da tsohon nan yanzu ba.
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romancewannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...