*ZAMANIN MU A YAU*
NAJEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO*PAID BOOk*
_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________*011*
Hank'alin Hamida ne yayi mugun tashi nan ta durkushe kasan ɗaƙin tashiga magiya " DanAllah ranki yadade kiyi hakuri wallahi bandade ba sabida son rai na, alhaji Abah ne yabada umarnin mu hadawa maleek kayan fruit yakusa isowa. Madam maryama dake zaune aƙan kujera sai faman ƙada kafa daya ƙan daya takeyi, minti ƙadan taja tsaki takara ƙallon hamida tace " Bana magana biyu kinsani ko? kamar yadda nazabarwa kaina rayuwa da ɗa daya to ƙomai nawa yanaƙan guda ne! Dan haka na sallameki babu abunda yayimin zafi da yawan shekarun mu tare ko ladabinki kokuma makamancin haka, dan haka ki hada ƙayanki kiyi hanzarin nufar gidan gyatumanki." Tana gama faɗa ta nufi daƙinta ta banƙo ƙofar. Hamida dake durkushe agurin tafashe da kuka tashiga faɗin " YaaAllah kaine mai azurtawa yaAllah kabani yadda zanyi tafada tana k'uka tare da barin gurin, tunda tafita bata tsaya ko'ina ba sai sassasar su ta masu aiki tana kuka ko data isa daƙin nasu bata tarar da kowa ba sai baba larai tanajin radio kallonta tayi cike da firgici tace " Ke hamidatu menene kika shigo kina kuka ina cikin firgici ƙada kikaramin wani." "Wallahi baabah babu abunda nayi mata kawai dan ban kawo mata lemo da wuri ba kuma umarnin abah nabi ak'an a hadawa maleek kayan tabawa kafin yaƙaraso." Shiru baabah tabawa tayi batare da tace ƙomai ba tana ƙallon hamida sai daga baya tace " To ai sai kiyi hakuri kinsan dai ni bani zuwa in tunƙareta da maganar bada hakurinki dan banda wannan matsayin." " DanAllah danAnnabi babah kitaimaka kibata hakuri kinfi kowa sanin da wannan aikin nake dawainiya da iyayena danAllah." " Hamidatu kiyi hakuri Allah yazaba miki mafi alkhairi." Kuka sosai hamida tashiga. Babah larai kuwa miƙewa tayi ta nufi bangaren hajiya fulany dan tabbas bata iya riƙe maganar nan batare da tasanar da itaba. Tana shiga shashin tafara tarar da hajara ƙanwar abah tare da Hajiya cik'in girmamawa tagaidasu sannan tasamu guri ta zauna sanin halin hajiya fulany idan kanada saqo tanan zata gane." " larai naji kinyi shiru akwai magana kenan abakinki?" Murmushi larai tayi tace tabbas hajiya." " To ai hajaru ke gurin nan tunda diyata take ai babu damuwa sanar dani." " Ranki yadade hajiya wallahi dazu abah yazomin da wani batu hankalina yatashi sanin tazarar dake tsakani da nisa." " Hajara ce tagyara zama dan ita indai akan abah ne to tabbas tafi kowa maraba da zancensa. " tazara kamar yaya larai wani abun kikayi ne?" " ko daya ranki yadade magana yayimin aƙan aure dayakeso yakara." " Nima munyi maganar dashi." " Ranki yadade ba lallai irin maganar da yayimin baceba yazomin aƙan maganar hamida cewa itace wacce yagani yakeso." Cikin ɓacin rai hajiya tajiyo tace hamida? Wacce hamidan?" Dariya hajaru tayi tace " banda abunki hajiya akwai wata hamida ce bayan mai aikin gidan nan?" " kigafarceni ranki yadade nima na nuna masa tazarar dake tsakani amma kwatakwata yaki saurarata." Hajaru ce takara dariya tace " Tunda aka karbe wannan kamfanin Ahmadun yazama wani iri gaskiya hajiya ki bincikeshi, duk da dai ba laifi baniba dan yace yanason ƴar aiki, kadan daga masifun dasukafara sauƙar masa kenan to Allah ya sawake." Hajiya ce tayi dariya tace " Banda abunki hajaru ai masifa bataga abah ba albarkacin fiyayyen halitta arzukinsa sai yafi nada ma." " dakamar wuya hajiyarmu." Tafada ranta na sosawa amma wannan hanyar kadai ce zatasa tacimma abunda ke cik'in ranta tabbas zatayi amfani da hamida domin wulakanta abah aduniya" larai zaki iya tafiya Allah yazaba mafi alkhairi koda hamidan ce." Babah larai ta amsa da amin sannan tafita daga shashin nasu tana zuwa tatarar da hamida tana hada ƙayanta zaunar daita, hamida magana ce akan Ahmadu wato Abah wannan wani kyauta ce da Allah yakeso yabaki sai ki gode masa ki kuma tattala kyautar, babah larai duk ta kwashe tagayamata yadda sukayi, lokaci daya wani farin ciki ya saukar mata." Babah kina nufin dakansa yace miki?" " wallahi hamida zuwa karshen sati zasuje suga iyayenki." Wata muguwar dariya tayi hade da faɗin " Nagode Allah." Sallamar da akayi yasasu daga kansu hajiya hajara ce. " larai ko zaki bani guri zanwa ɗan uwana kamfen." " hajiya hajara me zai hana bari nafita." Wannan itace babbar damar dazaki samu arayuwarki hamida nasan kinsan Abah kinsan wanene shi babu maccen dazataganshi tace baidace da'ita ba sai dai ma tace yafi karfinta, wannan lokacine da zakiyi amfani dashi gurin samun ciƙar burinki, lokacine dazaki rama abunda ballagazar maccen cen tayimiki lok'acine da zaki Gina labarin zuciyarki, abu nafarko danakeso dake zamu hada hannu zankuma taimakamiki maganar kayan biki da daƙinki na dauki ragamar komai, kuma kisa aranki inada zafaffun malamai, zan maidake tauraruwa acikin zuciyar Abah zamu ƙore maryama zamu dasaki, wani farin cikine yakama hamida tare da godiya da kuma amincewa da dukkan bukatun hajaru."
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romancewannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...