12

125 5 0
                                    

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

012

"innalillahi wa'inna illahim raji'un! Wannan wacce irin masifa ce? Umma Habiba ta faɗa gami da yi kan Mummy tana girgiza ta, gami da kiran sunanta gani bata motsi yasa hankali Umma mugun tashi ta ruga part ɗin Baba ta kira shi hali da ta tadda shi ciki yafi wanda ta baro Mummy ciki muni duk yadda ake shiga tashin hankali yau Umma Habiba ta shige shi gaba ɗaya ta fice daga hankali gashi Abdulkarim baya gida idan ta ce ta kira shi a waya Kafin ya zo komai zai iya faruwa, saboda haka ta nufi bakin gate cikin sa'a ta tarar da mai gadi da direban gidan su na fira suna gani yadda take haƙi su kasan babu lafiya shiyasa tun kafin ta kai ga yi musu magana suka tashi tsaye cikin matuƙar ruɗewa da fita hayyaci take magana koda Umma Habiba ta dawo guri Mummy masu kawo lefe sun yi tsaye jigu-jigu ba su da niyar komawa idan suka fito, wani mugun kallo Umma watsa musu kafin a mugun fusace ta ce "Wai ku me ku ke jira ne hakan? Ko ku na jira har sai na ba ku umarni ku tattara wannan ƙazantar taku ku barna gida?
Wata tsohuwa ce mai ƙarfin hali daga cikin ayari ta ce "ke kuwa Hajiya me ya yi zafi shi ba wuta ba. Ai mu 'yan araka yarima ne a sha ƙida. Mai gadi da direba suka cicciɓe Mummy suka sa mota. Umma Habiba ta kalli tsohuwar da tai magana cikin rauni murya gami da karaya zuciya ta ce "Baaba ki ɗauki kanki ki kai matsayin mu ke ce ki ke da 'ya sai ta bijere miki akan saurayi kuma saurayi nan ba nagari bane a matsayin ki na uwa ba ki da buri da ya wuce wannan 'yar taki tai aure gidan mutunci da nagarta kwatsam! Sai a zo miki da labari ta daura aure ba tare da sani ku iyayenta ba. Shin a wannan lokaci da labarin ya riske ki shin ya za ki yi?"
"Subhanalillah! Ba a fata 'yar nan amma da matuƙar wahala zuciyata bata buga ba.
"To kin gani ita ma mahaifiyar Salma hali da ta shiga kenan saboda haka Dan ALLAH ku tattara akwatuna nan ku mayar musu da abinsu yadda ta iya bijere mana ta zaɓi tai aure ko ba da amincewar iyayenta ba, shi ma lefen za ta iya zuwa ta karɓo abinta da kanta.
Daga haka Umma Habiba ta nufi gun mota domin sa'ili da take magana har maigadi da direba su ɗauko Alhaji Umaru Sadauki sun sa mota, tana shiga mota kafin direba ya ja motar ta ƙara jadadda wa maigadi ya tabbatar da waɗancan mutane sun bar musu gida.
Suna zuwa asibiti aka wuce dasu emergency room likitoci suka duƙufa ceto rayuka su, a wannan karo jini Baba yai bala'i hawa Mummy ma jini ta ya hau ga kuma zuciyarta da ke bugawa tana daff da kamuwa da ciwon zuciya.
Ta ɓangaren gimbiyar taku Salma suna baro guri da aka ɗaura musu suka nufi hotel buri Yazeed Talba ya dandani zumar ta sai dai kashhh! Tana period hakan ba ƙaramin ƙona masa rai ya yi ba nan take ya rufe ta da faɗa "Wannan wane irin iskanci ne Salma kin san yadda na kwallafa raina akanki babban burina yau ɗinan na sauke duk wani kwaɗayi ki da nake ji shi ne dan kuturun wulaƙanci za ki bar wannan abin ya zo miki, idan har ina da muhimmanci a wurinki kamata ya yi ki sha magani ki hana masa zuwa.
Ya ƙarashe magana yana mai saukowa daga kan gado tunbur! jikinshi ba kaya da sauri ta taso daga kwance da take yadda yake tsirara ita ma haka take babu kunya balle tsoron ALLAH ta tsaya a gabanshi ta wani narke murya tana faɗin "Dear ka yi haƙuri nima nayi mamaki zuwansa yau da safe saboda ba shi bane actual time ɗin da yake zuwa ba. Amma na danganta hakan da stress ɗin da nake ciki.
"Mtsssss! Ba dole ki shiga stress ba tun da ALLAH ya haɗa ki da tsinannu Iyaye da ba sa son farin ciki.
Ya ƙarashe magana gami da yi wani tsaki ya nufi bathroom yana mai ci-gaba da zagin iyayenta.
Idan ta ce ba ta ji zafi zagi da ya yiwa iyayenta tayi ƙarya sai dai zazzafar soyayya da take masa ba za ta barta taga laifinsa saboda tsanani gudun ɓacin ransa da take yi yasa ta bishi cikin bathroom ɗin ta ci-gaba da rarrashinsa sai da ta kai ga yi masa kuka sannan ya haƙura kafin ya mannata ga bango bathroom ya ci-gaba da jagwalwala ta sai da tai masa sucking ya yi realising sannan hankalinsa ya ɗan kwata amma babba burinsa ya ratsa cinyoyinta, kuma ya kudurta a ransa duk ranar da ya sami damar yi hakan ba zai mata da wasa ba.
Sai dare suka baro hotel ɗin ya ajiye ta a kofar gidansu da suna sai ya ƙarasa gyara musu gidan da za su zauna duk iskanci nan da suke tattawa ko gini sa bai kammala ba.
"Mtsssss! wallahi Umma mutumin nan ya gama rena muku hankali haka kawai zai ɗora mana sharri sata.
Cewar Rufaida wacce take ji Kamar ta bi bayan mahaifinta ta rufe shi da mugun duka.
Kallon mamaki Hauwa ta bita dashi duk da ba yau ne ranar farko da ta fara jin iri-iri waɗannan kalamai daga bakin yaransu. Kafin tai magana ta tsikaya muryar Zakiyya tana faɗin "Wallahi Umma maganar Yaya Rufaida gaskiya ce ban da reni wayau irin na Abba ina ruwan mu da dukiyarsa, dukiyar da kullum da kalar buri da yake ci akanta...
"Ke Zakiyya!
Hauwa ta faɗa cikin tsawa kana ta ci-gaba da faɗin "ahir! Ɗinku karka na sake ji kun faɗi maganar rashin ɗa'a akan mahaifinku duk lalacewrsa mahaifinku ne matuƙar ba za ku yi masa addu'a da fatan shiriya ba to ku kame bakinku ku yi shiru.
"Umma ki yi haƙuri amma gaskiya a wannan karo Abba bai yi mana adalci ba duk rashin adalci halinsa ne duk abinda yake yi ni baya damuna amma yau da ya kira mu da suna ɓarayi kalmar nan ba ƙaramin ciwo tai min ba.
Hafsah ta faɗa cikin sanyi murya Rabi'ah ta ce koma menene haƙuri za mu yi domin kowanne ɗan adam da tashi ƙaddara mu ta mu ƙaddara ce ta zo da haka, kuma duk haƙuri da shanye wulaƙancinsa saboda ku muke yi da ace ba mu da 'ya'ya da shi da tuni zaman mu ya zama tarihi a gidanan, saboda haka ku ci-gaba da haƙuri da kauda ido akan duk wani cin kashi da zai mana. Hauwa da Rabi'ah haka suka ci-gaba gaba da lurar da 'ya'yansu akan mahaifinsu jin su kawai suke yi musanman Rufaida da take ji babu ko burbushi ƙaunarsa a zuciyarta ita fa bata ƙi yana fita tirela ta bi ta kanshi ta nanuke namansa.
Lokaci da labari abinda Salma ta aikata ya riski Ya Bashir da Ya Abdulhakim sun shiga ƙunci da baƙi ciki kasa jurewa ya Bashir ya yi a hasale ya nufo gida koda ya zo Salma bata dawo daga gantalinta ba ya share wuri ya zauna yana jiran dawowarta sallah kaɗai ke fitar dashi daga gida yana zaune a main parlour sai ga ta ta dawo ko kallonshi bata yi ba nufi ɗakinta tana wata irin tafiya tana hura hanci, tana daff da kai wa ƙofar shiga ɗakinta a kufule Ya Bashir ya kira sunanta "Salma!
Ta juyo tana yatsine fuska cike da fitsari gami da zallar rashin kunya ta ce "Malam ya aka yi ne?"
Sosai ta ƙara harzuƙa Ya Bashir ya taso a mugun fusace ya nufo a maimakon ta arci na kare sai kawai tai tsayin ta tana wani girgiza ƙafa duk tsiyarsa bai wuce ya dake ta ba kuma a yau tasha alwashi duk uban da ya kai hannu jikinta sai ta rama don ita ba jaka bace. Ya Bashir yana zuwa ya ɗauke ta da kafiri mari sai da ta wuntsila baya ta dafa bango tana ɗagowa ta kai hannunta da nufi ramawa kafin hannunta ya kai ga fuskarsa ya damƙe shi yasa dukkan ƙarfi da ALLAH subhanahu wata'ala ya albarka ce dashi ya murɗe hannunta ya bada wani irin sauti mai ƙarar gaske "ƙasssssss! Ta zubduma wani irin ihu wanda ya karade ciki da wajen gidan, duk da haka bai sa zuciyar Ya Bashir tai sanyi ba sai kawai ya rufe ta da mugun duka ta ko'ina naushi yake kai mata irin dukan nan da ake kira da dukan akawo wuƙa.
A can asibiti kuma Umma Habiba tana hankalce da fitar Ya Bashir ta kuma ga a fusace ya fita shiru-shiru bai dawo ba nan take jikinta ya bata babu lafiya domin duk sanda mahaifinsu ya kwanta jinya nan da can ba zai gusa ba a takaice ma shi yake kwana guri Baban nasu amma yanzu ya fita fiye da awanni uku bai dawo ba shiyasa Umma ta zargi gida ya tafi guri Salma ta Kuma san ba za su kwashe ta da kyau ba domin duk cikin yaran gidan yafi kowa Zuciya, saboda haka Umma ta miƙe ta umarce Ya Abdulkarim ya zo ya Kaita gida za ta yi wanka. Tun a bakin gate suka fara jiyo ihu da neman taimako da Salma take yi Ya Abdulkarim yana kammala parking Umma ta ɓalle murfi mota ta nufi entrance da gudu, yadda ta hango Ya Bashir ya haye ruwan cikin Salma sai tumurmusa ta yake yi yai bala'i ɗaga mata hankali "Kai Bashir! Kanka ɗaya kuwa kashe ta za ka yi ne?
Ya Bashir da bai ji bai gani sai dunƙule hannu yake yi yana kai mata naushi tuni ya gama farfasa mata baki da hanci fuskata gaba ɗaya ta haye tayi suntun! Kamar an kwaɓa fulawa da east, yayin da hankali Ya Abdulkarim kwance sai kawai ya nemi kujera ya harɗe abinsa bai ƙi Ya Bashir ya aikata barzahu ba. Saboda bai ga amfani barinta a raye ba.
Duk yadda Umma taso ta ɓamɓare Ya Bashir daga cikin Salma ta kasa Saboda majiyi ƙarfi ne jikinsa a murmurde yake kamar ɗan wrestling, a fusace umma Habiba ta kai ganinta akan Ya Abdulkarim rai ɓace ta ce "Zaman me ka ke yi Abdulkarim da ba za ka taso ka taimaka min mu ceto ta ko so ka ke yi sai kashe ta?"
Tasowa Abdulkarim ya yi yana faɗar "Ai wallahi Umma gara ya kashe ta mu huta miye amfani rayuwarta mutuwar ta yafi mana alkhairi.
"Banaso shasshamci Abdulkarim kana tsammani idan ya kashe ta hukumar za ta zuba mishi ido ne?
"Umma iyakaci ya yi fursuna amma wallahi barinta a raye ba ƙaramar masifa bace.
Abdulkarim ya ƙarashe magana yana mai nufar ɗan uwansa tsabar takaici Umma Habiba kasa magana tayi sai kawai ta ci-gaba da ture Ya Bashir kajaran-majaran! Suka cire shi daga jikin Salma wacce zuwa lokaci nan ta daina motsi gawa ce kawai yake duka. Yadda Umma Habiba taga fuskar Salma ta kwaɓe kamar wacce tayi car accident, yasa ta kaɗuwa tana taɓa ƙofufin hancinta ta ji bata numfashi umma batasan lokaci da ta ɗora hannu akai ta ratsa kuka "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Shikenan Bashir ka kasheta Bashir ka kasheta kai Abdulkarim zo ka taɓa jikinta ka ji wallahi bata numfashi.
Ba dan ran Abdulkarim yaso ba ya tattaɓa jikin Salma yayin da Ya Bashir yana gefe yana sauke zazzafan numfashi kuma babu nadama a tattare dashi.
"Umma suma ne tayi ki yayyafa mata ruwa mai sanyi za ta farfaɗo.
Da gudu Umma Habiba ta nufi guri fridge ta buɗe ta dauko ruwan roba wanda ya fara ƙanƙara ta sheƙawa Salma nan take ta ja dogon numfashi kafin kuma ta kurma ihu gami da faɗin "wayyo Umma Ya Bashir ya ƙarya min hannu ya ƙarya min ƙugu.
Umma ta juyo a kufule ta rufe Ya Bashir da faɗa kasa jure faɗa Umma ya yi ya fita a fusace.
Da taimakon Umma Salma ta kai gun mota asibiti suka nufa sai aka yi ma Salma gyaran hannunta domin ta sami kariya kwana su Baba biyar asibiti sannan aka sallame su har suka dawo Salma tana karkashin kulawar Umma..

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now