ZAMANIN MU AYAU 2

183 10 0
                                    

*🫧 ZAMANIN MU A YAU🫧*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

_________

*002*




Murmushin jin daɗi Hajiya Nafisa tayi a cikin ranta domin tabbas burinta yana gaf da cika akan ƙawartata, sautin muryar Hajiya Maryama ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, cikin makirci irin nata tace "Ƙawata ai na gayamiki kina da cikakken ƴanci, ki ci-gaba daga inda kika tsaya, ko kaɗan kada ki sa sanya domin nan da ɗan wani lokaci sai mulkin gidan Shema's ya dawo hannunki, wannan mahaifiyar tasa kuwa gwara da kika canza mata taku hakan ba ƙaramin kasa gane gabanki da bayanki zata yi ba.
Murmushin nan nata tayi mai cike da izza da nuna isa, sannan tace "zan fita yanzu ƙawata za mu yi magana later.
Takaici ne ya cika Hajiya Nafisa dan ita kanta ta kasa fahimtar halin aminiyar tata duk kuwa da irin dabara da wayonta "hmm! kawai ta ambata sannan ta ajiye wayar hannunta.

Hamida! Hamida! Hamida!Kusan sau uku tana ambatar sunan ƴar aikin nata, cikin tsoro da firgici Hamida ta ƙaraso tana mai tsugunnawa tare da fad'in "dan ALLAH ki gafarceni Hajiya na dan fitane." Wani mugun kallo ta wulla mata sannan tace "ki tattara tarkace ne ki mayar kitchen na fasa ci orange juice kawai za ki kawo min kuma mai sanyi sosai nake so.
"To Hajiya.
Hamida ta faɗa tare da miƙewa da sauri ta nufi kitchen jim kaɗan sai ga ta ta dawo ɗauke da juice a glass jug haɗe da handle cup ta ɗora akan tray, ƙaramin centre table ta jawo ta kawo gaban Hajiya Maryama ta ajiye kana ta tsiyaya mata juice ɗin a cup, kusan rabin jug ɗin ta shanye kafin tayi gyatsa ta ɗago daga latsar wayarta da take yi ta dubi Hamida a ɗage ta ce "ki je ki samu idi kice masa zan fita ni ɗaya a fitar min da mota wajen gate.
"To ranki yadade
Hamida ta faɗa tana mai barin sashin. Miƙewa maryama tayi ta shiga wanka again ta jima sosai kafin tafito, kai tsaye bedside drawer ta nufa ta buɗe tare da ɗauko wata robar magani wasu ƙwayoyi ta ɗauka tasha kusan kala 3 sannan ta shafa mai tare da zura wata baƙar abaya, white bag da takalmi fari ta saka sannan ta rufe kwayar idanuwanta da glass tare da kulle ɗakin sannan ta sauka ƙasa, Hamida dake tsugunne gefe ta daga idanuwanta ta kalleta cikin ranta ta tsinci kanta da faɗin Ma-sha-Allah uwar ɗakina ba dai kyau da gayuwa ba. Cikin isa irinta ta ta kalli h
Hamida sannan ta kau da kanta tana yatsine fuska ta ce "Turarenki ya ƙare ne?"
Ta wurga mata tambaya tare da dallah mata harara sunkuyar da kai Hamida tayi cikin rawar murya tace "Dama Abah ne yace kada nasake sakawa."Tsaki maryama ta ƙara ja "mtsssss! sannan tace mata "Abah ne ya siya miki? Nace abah ne ki zaune dake? Ko so ku ke yi ku kasheni da wari? Wannan ne maganata ta ƙarshe akan gyaran gashinki da kuma gyaran jikinki Hamida idan na ƙara maimaita miki to tabbas sallamarki zanyi."
Ta faɗa tana mai fita daga part ɗin nata.

Tun daga lokaci da ya isa office gaba ɗaya ya kasa aiki, saktariyarsa sau uku tana kawo masa file amma ya kasa dubawa, da alama fever ce ke ƙoƙarin rufeshi, knocking ɗin da aka yi ne yasas hi gyara zamanshi da yabi ƙofar da kallo a hankali kafin yace "Yes! come in."
Wata matashiya mace ce da ba zata wuce shekara 28 ce t ashigo cikin office ɗin, sanye take da wasu matsatsun kaya, fuskarta tasha makeup ga kuma bakinta da yayi raɗau da janbaki, take tsigar jikin Abah ta soma tashi, wata azababbar sha'awa ta taso masa yai sauri rufe idanuwansa, baisan lokacin da yaja numfashi ba daga sama ya ji tana gaisheshi "Barka da rana sir daman angama design na flask ɗinan ne, idan ALLAH yasa muka yi shi za a samu alkhairi sosai.
Duk maganganunta ba wanda ya ji ya dai yaji ta ambaci kalmar design amma bayan wannan kalma baya tunanin yaji komai, murmushi tayi har cikin ranta ta ji daɗi yanayi da taga ya shiga domin ta tabbatar hankalin oga Ahmad ya fara karkata kanta, aduniyar nan bata da wani muradi sama da ta kusanci oganta, dan yadda take kishinsa bata tunanin madam Maryama nayi, ɗago rinannun idanuwansa yayi Yace "Hadiza!" Cikin yanga da jan hankali tace "uhm sir! tana ƙoƙarin kara banƙaro ƙirjinta, mutane nawa kike da burin halaƙarwa a company nan bayan ni Kina mantawa da ke musulma ce Ko kuma kin manta kina da igiyoyin aure akanki? Hadiza wannan shine last time da zan yi miki faɗa dan nan gaba sai dai na sallameki daga wannan Company, ya faɗa yana mai gyara zamanshi Dan ALLAH kalli shigarki kalli tsayuwarki, ko kina tunanin na canza ne ko kuma zan canza?" Cikin duburbur cewa Hadiza tace "Dan ALLAH kayi hakuri Sir baka fahimce ni bane ba.
"Okay fita! yace yana mai nuna mata hanyar barin office ɗin. Wani wawan bugawa kansa ya yi cikin sanyin murya yace "Yaa hayyu yaa ƙayyum ka tsare ni daga dukkan tarko na shaiɗanu mutane da aljan sannan. ya ɗauki wayarsa wasu numbobi ya ɗanna, kana ya furta "can we meet today?" Banji mai na can bangaren yace masa ba sai Abah sake cewa "Okay thank you."
File ɗin gabansa ya jawo ya fara bubbuɗewa, jin jikinsa na daukar zafi da kuma wasu sauyi yasa shi miƙewa ya ɗauki key ɗin motarsa, ya fita ya tarar da securities ɗinsa ko ina sannan driver ɗinsa yayi saurin miƙewa yana mai nuna girmama warsa ya isa gareshi, "Malam ado airport zamu je Alhaji yana tafe.
"Tohm ranka yadade ya fada yana mai ƙarbar mukullin.

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now