ZAMANIN MU AYAU 7

132 6 0
                                    

*🫧ZAMANIN MU A YAU🫧*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

*007*

Murmushi Abah ya yi dan tabbas wannan shawarar ta abokinsa tayi masa ɗari bisa ɗari dama yasan halin gimbiyar tasa da shegen girman kai tsiya da fi'ili ta hanyar aure 'yar aikinta kawai zai koya mata hankali haɗe da nuna mata ita ɗin ba kowa-kowa bace ba domin duk abinda ta zama da bazarsa take taka rawa, wannan shawarar ba ƙaramin daɗi tai masa ba dan duk ƴan aikin gidan bai taɓa ganin mai ƙoƙarin Hamida ba duk da abunda Maryama take yi mata ta shanye komai tana zaune da ita. Cike da gamsuwa da shawarar aminin nasa ya ce "To abokina ina godiya sosai da wannan gudummawar taka ALLAH yabar zumunci ALLAH yasa hakan yaz ame mana alkhairi. "Amin ya ALLAH abokina Amma kuma ina da wani complain dan ALLAH kayi nazari akai gami da tunani.
Gyara zama Abah ya yi fuskar nan tashi ɗauke da fara'a wacce ta bayyana farin haƙorin makkahn sa yace "ALLAH yasa ba wani laifin nayi ba kuma?"
"A'a babu laifin da kayi magana ce ta gaskiya zan yi kuma dan ALLAH a duba maganata Alhaji Ahmad, nasan ka yiwa Gwamnatin hidima kuma har gobe gwamnatin mai mulki yanzu tana alfahari da kai saboda gaskiya da riƙon amanarka yasa har yanzu kujerar ka da ka baro ba a maye gurbin ta da kowa ba. Domin koda yaushe suna dako dawowarka wannan dama ce da za ka koma bakin aikinka ka ci-gaba daga inda ka tsaya Dan ALLAH abokina kada min a'ah!
Ƙarfaffiyar ajiyar zuciya Abah ya yi domin gaba ɗaya Alhaji Sadik ya ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa, tsawon mintuna ya kasa cewa komai sai shafar lallausar sajensa yake yi Alhaji Sadik ya ce "Ya naji ka yi shiru abokina kodai buƙata ta ce bata sami karɓuwa ba?"
"Hmmm! Ba haka bane Alhaji Sadik kawai dai ina tuna girman al'amari nan da ka zo dashi, duk babu abinda zai gaggara a tsakanimu ka bani ɗan lokaci zan yi nazari da tunani.
"Ba wani nazari da tunani da za ka yi Shema duk nazari da za ka yi ba zai ka wanda na kwana ina yi maka ba Dan ALLAH ka amince ka tuna irin gudunmawar da mu ka ba wa jam'iyyar, da gimin jikinmu da na aljihun mu ka tuna irin faɗi tashi da mu dinga yi har ALLAH yasa muka yi nasarar kafa gwamnati mai adalci, sai da lokaci da za mu ci moriyarta ya zo za ka guje mu. Shi kanshi Mr President yana yawan zance ka sai dai nasan yanda ka ke ɗaukar duk wani al'amari da ya shafi dattijo da matuƙar muhimmanci da wuya ka dawo shiyasa a duk lokaci da yai min zance ka sai kawai na basa haƙuri gami da bashi tabbacin wata rana za ka dawo.
"Shikenan abokina na amince ALLAH ya shige mana gaba yasa hakan ya zame min alkhairi.
"Amin thumma Amin abokina lallai yau zan fesa wa 'yan jam'iyya labari mai matuƙar daɗi dole ma mu haɗa maka kwarya-kwarya liyafar murnar dawowarka.
Dariya kawai Abah ya yi daga nan suka ci-gaba da fira suna tuna irin hidima da suka dinga yiwa jam'iyya, bayan wani lokaci Alhaji Sadik ya yi masa sallama har wajen motarsa Abah ya raka sa bayan ya dawo kaitsaye ɓangaren sa ya nufa a master bedroom ɗin sa ya yada zango ya nufi safe ɗin da yake ajiye muhimman abubuwan sa ya yi pressing code wanda date of birth ɗin Maleek ne ya tattaro duk wasu documents na Company ɗin dattijo yau jin kan shi yake yi sakayau! Tamkar an ɗora masa ƙaton dutse an sauke domin wani ƙaton nauyi ne zai saukewa kanshi.
__________
*"BARRISTER SULEIMAN GARKUWA MANSION"*

Cike da tashin hankali Surayya ta nufi Master bedroom ɗin Barrister Suleiman, cikin tashin hankali ta tura ƙofa yana zaune da laptop a gabanshi yai sauri ɗagowa a dalili yanda ta bango ƙofar kafin ya kai da tambayar ta ba'asi shigowar ta babu sallama tai sauri cewa "Man gidanmu babu lafiya yanzu nan Abdulkarim ya kira ni a waya yana faɗa min jiya da dare saura ƙiris! Baba ya kashe Salma yanzu haka tana asibiti har wayewar safiya yau batasan wanda yake kanta ba.
Yadda ta ƙarashe magana tana rushewa da kuka yai masifar ɗagawa Barrister hankali yai sauri ture laptop ɗin gabanshi ya taso da sauri, sai da ya zaunar da ita akan resting chair kafin ya durƙusa ya riƙo hannuwanta duka biyu ya jinƙe su cikin tafin hannunshi ya kwantar da murya cikin sigar rarrashi ya ce "Sweetheart please calm down kinsan hali da ki ke ciki abu ƙanƙani zai iya haifar miki da matsala.
Cikin muryar kuka ta ce "Man har yaushe farin ciki da kwanciyar hankalin gidanmu zai dawo kullum da kalar tashin hankali da zai faru Salma so take ta kashe mana iyaye da baƙin cikin da koda yaushe take ƙunsa musu akan ɗan iska yaronan Yazeed Talba wanda duk gari an shaida rashin tarbiyyarsa.
"Duk da haka Surayya ki yi duba da situation ɗin da ki ke ciki banaso wani abu ya sami Babynmu wallahi Surayya na kwallafa raina akan cikin nan naki fiye da cikin Rusulum.
Sai da Surayya ta goge hawaye fuskarta kafin ta ce "Man tashi ka kaini gida naga hali da Babanmu yake ciki domin Abdulkarim ya gayamin bai taɓa gani Baba yana kuka da hawaye ba sai jiya, da alama laifin da Salma ta sake yi ya girmama sosai.
"Hmmm! Ai Surayya halin irin na Salma sai dai addu'a gaba ɗaya ta gama lalacewa ta fandare wallahi da ba ki kama da ita da nace ba ku haɗa jini ba. Tashi mu je na kai ki gun Baba ɗin saboda ko kaɗan banaso zance kangararriya yarinya nan.
A babban falo gidan suka tarar da Mummy da su Abdulkarim Mummy tayi kuka har ta gode ALLAH idanuwanta sun yi luhu-luhu, kallo ɗaya za ka yi mata ka gano tana cikin tsantsan damuwa. Hankali tashe Surayya ta zauna kusa da ita cikin muryar so yi kuka ta ce "subhanalillah... Mummy ya naganku jigu-jigu gida ya dawo tamkar gidan makoki kowanne ku na kalli fuskarshi ina iya hango ɗibin damuwa da yake ciki meke faruwa ne me Salma ta aikata har haka ne?
Kasa cewa komai Mummy tayi sai kawai ta shiga sharar hawaye domin ita kanta har yanzu bata san me Salma tayi ba iyakaci Baba ya faɗa musu abinda tayi muninsa ya yi yawa har ya koma ga Ubangiji bakinsa ba zai iya faɗarsa ba. Tun daga lokaci Mummy take cikin ƙunci da baƙi ciki tun da Baba ya kasa faɗawa kowa ta tabbata da ƙazantar tayi yawa.
"Ki yi haƙuri Mummy ki daina ɗaga hankalinki domin kowa ya shaida irin kyakkyawar tarbiyya da yaran gidanan suke da ita. Salma ce kaɗai ta fita dabam saboda haka Mummy ki ɗauki wannan a matsayin jarabawa kawai dai mu ci-gaba da addu'a ALLAH ya ba mu ikon cinye wannan jarabawa.
Cewar Barrister Suleiman wanda ya ƙarashe magana cikin sigar son kwantar wa da Mummy hankali.
"Bari kawai Suleiman ni na tabbatar baƙin ciki Salma zai yi ajalina a dalili abinda ta aikata ga mahaifinta kwance magashiyan hawan jininsa ya tashi wanda ita ce silar kamuwar sa dashi.
Da sauri Surayya ta tashi hankalinta yai mugun tashi ta nufi ɓangaren Baba gani haka yasa Barrister Suleiman fasa maganar da ya yi niyar faɗa ya bi bayanta, shi dai damuwarsa ɗaya cikin jikinta. A kwance suka tarar da Baba hannunshi manne da drip Ya Bashir da Ya Abdulhakim su na zaune kusa da shi kowanne su tamkar yana kirga numfashi da yake fitar wa, hankali Surayya ya ƙara tashi a dalili yadda taga Baba ya zabge ya yi wata muguwar rama tamkar wanda ya shekara yana jinya, kasa jure ci-gaba da kallonshi tayi ta juya cikin kuka ta fito daga ɗakin yayin da Barrister ya bita da kallo ya sauke numfashi kana ya dawo da ganinshi akan su Ya Bashir ya tambaye su jikin Baba, ya ɗauki tsawon mintuna goma a ɗakin kafin ya fito ya dawo falo har lokaci Surayya tana sharar hawaye duk sai ya ji tsanar da yake wa Salma ta ƙara linkawa fiye da farko.
________________

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now