Paid book N400
_Team tagwaye_.
ZAMANIN MU A YAU
NA
JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISOGA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA
GUDA BIYAR 1500.GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salisKATIN WAYA
+234 706 528 3730*FREE PAGE*
*004*
"Ki ji tsoron mahaliccin ki Maryama duk mutumin da ya bawa shekaru 40 baya ai ba zai danganta kanshi da yarinta ba...
"Dallah dakata Abah! Kada ka sake ka gayyan magana ko munafiki ya kalle ni ba zai ce nayi shekaru 40 a duniya ba domin yadda nake gyaran jikina ko yarinya mai shekaru 18 ba za ta gwada min komai ba sai ni ɗinan da ka rena na nuna mata.
Murmushi ƙarfin hali ya yi domin ba ƙaramin mamaki take bashi ba yadda ya ga ta taƙarƙare cikin ɓaci rai sai kwararo zance take yi, shi da ya zo da buƙatarsa shine za ta wani buge da yi masa wani zance na dabam.
"ALLAH ya ba ki haƙuri habibty ni dai dan ALLAH ki taimaka mun wallahi idan ban rage mara ta ba komai zai iya faru dani.
"Humm!
Ta faɗa tana wani taɓe baki dan ba ƙaramin haushinsa take ji ba da ya kira ta da tsohuwa, gyara zama tayi ta fuskanci shi da kyau kana shiga kwararowa masa nata buƙata, dama ita lamarin ta ban gishiri na ba ka manda ne. Lokaci da ya ji ta ambaci Ten million naira sai da ya girgiza domin bai yi tsammanin haukarta ya girmama har haka ba.
"Habibty me za ki da Ten million iya sani dake ba kasuwanci ki ke yi ba ballantana nayi tunani ko za ki ƙara ƙarfi jarinki ne?"
Yai magana cikin kwantar da murya kamar wani yaronta, duk wannan kwantar da kai yana yi ne domin ya sami biyar buƙatarsa. Kuma ta fahimce sarai shiyasa ita ma ta shigo da nata buƙata. Harara ta fara watsa masa kafin ta hayyaƙo masa tana faɗin "million goma har wata kayan gabas ce da za ka titse ni sai na faɗa maka abinda zan yi da ita.
Sosai ta ƙara jefa shi a mamaki yanzu banda reni wayau irin na Maryama million goma ce za ta ɗauke ta ba a baki komai ba. Sai kawai ya murmusa gami da cewa "Maida wuƙa rabin raina na tambaya ne kawai kinsan banaso almubbazaranci..
"Dallah isa! Iya sani kai dani bana caca balle ka danganta ni da kalmar almubbazaranci, idan za ka bani ka bani kawai kai kuma ka sami biyan taka buƙata idan ba za ka bani ba Please ga ƙofa nan kafita ka bani guri dama can ba gayyatar ka nayi ba kaine ka kawo kanka, saboda haka ba za ka zo ka haifar min da ciwo kai ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Ya shiga maimaita wa kusan sau uku ya faɗa kafin ya ɗago rinani idanuwanshi ya sauke su akan fuskar ta da take yatsina wa karo na farko na rayuwarsa da ya ji yana danasani aurenta, wai matarsa ta sunnah ba zai kusance ta har sai ya biya ta makudan kudade irin wannan ko karuwa ya dauko ai ba zai biya ta wannan manyan kudade ba. Nan take ya ji duk wata sha'awarta da yake ji ta kau, a mugun fusace ya ce "Daga yau Maryama ki rubuta ki ajiye muddin sai na biya ki za ki bani hakkina ki riƙe abinki in-sha-Allahu ba zan mutu ba da sannu Ubangiji sammai bakwai zai kawo mafita.
Kafin tayi magana yai miƙe ranshi a ɓace ya buɗe ƙofa ya fita tsanani ɓaci rai ko gabansa baya gani, a daddafe ya iso bedroom ɗinsa.
"Mtsssss! Ta ja dogon tsaki gami da faɗin "aikin banza kawai dama can jarabar taka ce bata motsa maka da kyau ba da ba million goma ba ko Hajiya nace ka yanka min da gudu za ka yanka ta ina nan ina jiran ka za ka dawo ka sami kuma wallahi ka jawo wa kanka don kuwa double changes zan maka.
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romancewannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...