*ZAMANIN MU A YAU*
NAJEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO*PAID BOOk*
_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________*014*
Tsawon lokaci Yazeed Talba ya dauka yana tsotsar bakin Salma sai kace zai cinye baki dukka, boobs ɗinta sai matsar su yake yi yana luguiguita su kamar zai tsinka mata su kwata-kwata babu wani daɗi da take ji sai azaba ta kasa dakatar dashi gudun kada ta ɓata mishi sai da ya gaji dan kanshi sannan ya sake ta tare da buɗe mata ƙofar mota ta shiga ya zagaye ya zauna a driving seat ya firzge motar da mugun speed dama gate a buɗe yake maigadi bai rufe ba. Kaitsaye gidansu ya nufa da ita a main parlour suka tarar da Yusrah da Yaseera kowacce tana sabgar gabanta Yaseera tana waya da wani abokin aikinta Yusrah kuma tana kallon movie a laptop ɗin ta shiyasa duk sallamar da gaisuwr da Salma take musu basu amsa ba. Sai da Yazeed Talba ya daka masu tsawa "wannan wane irin iskanci ne Salma tana muku magana ba 'yar iska da ta amsa a cikinku.
Da sauri Yusrah ta tsayar da movie ɗin da take kallo kafin ta yada ganinta akan fuskarshi cikin fusata ta ce "Mun ƙi mu amsa gaisuwar Salma ita da gaisuwar ta ta sun ci uwarsu! akan wane dalili za ka zo ka taƙura mana saboda wata ballagaza yarinya wacce kwata-kwata bata dace da ajinka ba.
Sosai kalaman Yusrah suka ɓatawa Yazeed rai ya yi kanta zai doke ta Yaseera tai sauri datse wayar da take yi ta taso ta shiga tsakani Yazeed da Yusrah domin ita ma Yusrah ta miƙe tana jira ya doke ta ita ma ta rama dan ba yau suka saba faɗa a tsakanin su ko kaɗan basa shan inuwa ɗaya tun farko ganinta da Salma taji tayi mugun tsanarta kasancewar best friend ɗin ta ya fara dating da ita dukkan su ita suka so ya aura yana haɗuwa da Salma ya rabuda ita tayi binshi har tagaji yaƙi ya dawo mata har yau Farha ta kasa daina sonshi.
Nan take suka dinga zagi junansu kamar 'ya'yan maguzawa Mom tana upstairs bedroom ɗinta ta ji faɗa ya kaure a tsakaninsu ta sauko da sauri tana faɗin "Kai Yazeed miye haka kai duk lokaci da za ka shigo gidanan sai ayi faɗa da kai?"
"Mom! Ba Wannan banzar bace ta zagi Salma kin Kuma sani duk mutumin da zai zagi Salma idan bani bane sai naci mutunci sa saboda haka ki ja wa 'yayanki kunne ba ruwansu da matata domin daga yau ta dawo gidanan da zama har sai na kammala gini na.
"Jar ubanan! Wallahi ba za mu zauna gida ɗaya da wannan kucakar ba. Ka je ka nema mata hotel ku ci-gaba da watsewar ku a can.
"Mom kina ji abinda Yusrah take faɗa ko na rantse zan ɓarar mata da haƙora gaba.
"Kai ya isa dallah! Gaba ɗaya kun cika mana kunne Yazeed ka sani nan gida na ne ba zan lamunci ka fiffita bare akan 'yayana ba, matuƙar kana so Salma ta zauna lafiya a gidanan dole ka koya mata girmama na gaba da ita dan ni ba zan ɗauki rashin tarbiyya a gidana ba.
A tunani Salma Yazeed Talba zai hayyaƙo wa Mom Kamar yadda take wa nata Iyaye sai taga saɓani haka ɗan kuwa Yazeed amsawa ya yi da "Mom ki yi haƙuri haƙuri in-sha-Allahu Salma za ta yi duk abunda ku ke so ba za ta taɓa saɓawa umarnin ku ba.
"Da yafi mata dan mu gidanan ba za mu lamunci rashin tarbiyya da ta saba yi a gidansu ba.
Yusrah ta faɗa gami da gallawa Salma harara wacce tai mutuwar tsaye wai har ita waɗannan gantalallu 'ya'yan mace ke kira da marar tarbiyya su da an yi ittafaƙi a unguwa sun fi kowa lalacewa tsabar rashin tarbiyyar su har kwantatce ake dasu.
Yau su ne ke mata goron tarbiyya duk sai jikinta ya yi wani irin sanyi a wulaƙancce Mom ta kare mata kallo sama da ƙasa ta taɓe baki kafin cike da izza ta zauna akan two sitter ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya, shaye da toka ta ce "ke Salma zo nan ki zauna na karanto miki sharudɗan zaman gidanan.
Mom ta ƙarashe magana gami da nuna mata ƙasa kusa da ƙafafuwan ta
Jikin Salma a sanyayye ta zo ta zauna tare da sadda kanta ƙasa cikin kakkausar murya Mom ta shiga faɗin "ya zame miki dole ki girmama yarana sannan kuma duk abinda Zeed zai miki kada ki kuskure ki kawo min complain daga ke har shi ba wanda aka yiwa dole saboda haka duk abunda zai miki ku je can ku ƙarata, abu na gaba banaso ƙazanta idan ma ba ki da tsafta ki yi gaggauta koya kuma banaso sa'ido duk abunda ki ka gani ki ja bakinki ki yi shiru.
"in-sha-Allahu Mom Zan yi ƙoƙari na kiyaye duk wasu sharudɗan ki
Salma ta faɗan cikin ƙaramar murya.
"Wannan kuma ya zame miki dole.
Yusrah ta faɗa tana galla mata harara domin Mom bata da lokaci sake tanka ta shiyasa Yusrah ta bata amsa.
Ɗayan bayan Ɗayan suka bar mata falo tana ɗago ga mamakinta sai taga Yazeed Talba yana chat a wayarshi sai zabga murmushi yake yi ko tantama bata yi da mace ce yake chat, ranta yai mugun ɓaci domin da ita ce iyayenta da 'yan uwanta suka nemi su ci zarafin shi da tuni tayi wanka tsalki ta kwashewa musu mutunci amma shi ko a jikinsa asalima nishaɗi yake yi abinsa a kufule ta taso ta iso gaban shi shaye da toka ta ce dashi "Malam ka nuna mfin inda zan shigar da kayana ko a gidan naku banida ɗaki ne?"
A tsanake ya ɗago ya ƙare mata kafin ya taɓe baki ya ce "Naga ai ɗakinki ba baƙo ki bane sau nawa kina shiga cikinsa kwana ne kawai ba ki yi a cikinsa ba in banda neman magana miye na wani tambaya.
Ya ƙarashe magana tare da maida ganinsa akan wayarsa ya ci-gaba da chat ɗinsa tsabar takaicinsa da ya kama Salma bata ƙara furta uffan ba ta wuce fuuu! Ɗakinsa dake upstairs tana zuwa ta kwanta akan gado ta shiga tunani irin zaman da za ta yi a gidanan dan gaskiya da matuƙar wahala tabi waɗannan sharudɗan da Mom ta gindaya mata.
____________
*"Alhaji Ado Hukuma Mansion"*
Yau kwanaki da ya ba wa Iyalin nasa ya cika kuma har kawo yanzu basu dawo masa da kuɗinsa ba saboda haka ya fito da rubber chair ya aza a tsakar gida, ya shiga ta ta musu rashin mutunci "Wallahi idan ba ku fito min da kuɗina ba duk abunda ya faru daku to ku sani ku ne ku ka jawo wa kanku wannan shine gargaɗi na ƙarshe da zan muku idan ba ku bani kuɗina ba na rantse da ALLAH guri malam Tsalha za je yai min yassi duk wanda ya ɗauki kuɗina zai haukace ko cikinsa ya kumbura ya mutu dan haka ɓarawon kuɗina ya rufawa kansa asiri ya dawo min da kuɗina cikin sauƙi da sauƙaƙawa kansa shiga bala'i.
Tun kafin ya ƙarashe magana jikin Rabi'ah ya ɗauki rawa tamkar mai jin sanyi cikin sauri Hauwa ta riƙo hannunta ta matse cikin nata, domin ta fahimci gargaɗinsa ba ƙaramin tasiri ya yi akan Rabi'ah. Cikin kwantar da murya ta ce "Alhaji idan kana gani zuwa wajen Malam Tsalha shi ne maslaha ka je kawai ALLAH yasa kuɗi nan rabonka ne domin ni dai na tabbata gidanan ba mu ɗauki kuɗi ba. amma ba zan hana ka yin yassi ba domin dukiyar kace watakila ma yassi ɗin ta zame mana alkhairi. Sai dai ina so ka sani ita yassi yawo take yi idan har ta je bata sami wanda ya ɗauki kuɗinka ba to kuwa kanka za ta dawo fargaba ta ɗaya kada ka mayar da 'ya'yanka marayu duk dai ba wani amfana suke da kai ba.
Hauwa tana dasa aya a zancen ta Rufaida ta shiga ƙunshe dariya har ga ALLAH maganar mahaifiyarta ba ƙaramin daɗi tai mata ba. Tun farko haka take so su dinga yiwa mahaifin nasu amma tsoronshi ya hana su.
Jikin Alhaji Ado Hukuma ya yi sanyi kasancewar barazana ce kawai yake yi musu saboda maƙonsa ba zai bari ya iya ba wa malaman tsibo ko bokaye kuɗinsa. Jin abunda Hauwa ta faɗa yasa ya shiga muzurai yana faɗin "Shikenan ku tashi ku bani guri amma Inaso ku sani daga ku har 'ya'yanku ba wanda zai ƙara jin daɗin zaman gidanan wahala zan dinga ba ku har na fanshe dubu sittin ɗina.
Ba wanda yace dashi uffan suka tashi gami da shigewa ɓangaren su. Sai da suka ji fitarsa sannan suka shiga mayar da zance Rabi'ah ce ta kalli Hauwa tana faɗin "Lallai yaya Hauwa ALLAH ya yi miki basira da iya tsara zance cikin hikima dan ni wallahi ina shirin miƙa wuya sai kawai na ji kin fara kwararo zance, kamar abunda aka tsara miki.
Hauwa da taji Rabi'ah ta koɗa ta sai wani murmushi take yi tana kaɗa kai gami da faɗin "Rabi'ah kenan ba ki ji masu iya magana suna cewa shege shi yasan makwacin shege wallahi ko da can ina ɗagawa Alhaji ƙafa ne a dalili 'ya'ya dake tsakaninmu amma ba dan haka ba da tuni nayi fito na fito da ɓakar aƙidarsa.
"Hmmm! Ko yanzu kin yi namiji ƙoƙari yaya Hauwa gobe ki ba wa Rufaida dubu arba'in ta je ta biya musu kuɗi makaranta raguwar ashirin kuma a turawa su Lukman sai su yi maneji kafin mu samu 'yan basusukan mu dake hannu mutane.
"Madallah! Rabi'ah nagode sosai da irin ƙoƙari da ki ke yi akan 'ya'yana shiyasa a koda yaushe cikin godewa ALLAH nake da ya haɗa ni da kishiya tagari.
"Lah! Yaya Hauwa ki daina gode min ban taɓa kallo su Lukman ba a matsayin 'yayan da na haifa da cikina ba. Fatana ALLAH Ubangiji ya ba mu tsawon rai cin moriyar karatunsu.
"Amin Rabi'ah ALLAH ya ƙara haɗa kanmu ya kore duk wata fitina a tsakanimu.
"Amin thumma Amin! Yaya.
Daga haka suka ci-gaba da firar su ta yau da kullum kamar ba kishiyoyi ba.
______________
Tun Salma tana zuba idanuwa taga gogan naku ya biyo ta ɗaki har bacci ya yi awon gaba da ita sai daff da magariba ta falka ta shiga bathroom tayi wanka, trolleys ɗin ta ta shiga nema lugun da saƙo na ɗakin bata gansu ba dole ɗaya daga cikin jallabiya's ɗin sa ta saka tayi sallah bayan ta kammala sallah ta cire jallabiya ɗin ta mayar da kayan da ta cire ta sauko ƙasa nemansa kowa babu a main parlour tsitt! Take ji a gidan kamar babu masu rai ga wata shegiyar yunwa da take ji kamar za ta ci babu ta fita compound bata ga motarsa ba alamar dake nuni da baya gidan ta gaji da tsayuwa ta juya tana shiga main parlour Yusrah tana saukowa daga bene taci uwar kwalliya cikin matsatsun english wears wando da riga yadda Yusrah ta kalle ta ta watsar kamar taga kashi yai masifar ƙonawa Salma rai.
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romansawannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...