ZAMANIN MU AYAU 06

124 6 0
                                    

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
--------------------
*006*

(Waiyazubillahi) saurin ture shi tayi daga jikinta tana sauke zazzafan numfashi. Wata muguwar harara Yazeed Talba ya saƙarwa Salma cikin fusata ya ce "Miyasa k ike min haka ne Salma?" Wai ke har sai yaushe za ki waye ne? Menene bambancin abunda muke yi yanzu da real one Eheee ba magana nake miki ba? Kin yi kunne uwar shegu dani.
"Kome za ka ce Yazeed sai dai kace amma duk lallacewata ba zan yi zina ba na gayamaka kuma zan ƙara gayamaka, ka barni da guntun zunubaina na romancing mana! Wai kai ba ka feeling rashin jin daɗi idan kana irin abubuwan?"
Gyara zaman towel ɗin da ke jikinsa ya yi sannan ya ƙara zama akan bed ɗin yana mai da wani mugun numfashi tabbas yarinyar nan ta mugun rainashi? Oh really!
Ya faɗa yana mata kallon kin ma rena min da hankali, kana ya ɗora da cewa "Kawai dai dan kin ga ina sonki ne Salma that's why ki ke min wannan wulaƙancin da ci wa soyayya ta mutuncin, watakila kina tunanin ke kadai ke sona ko? Is fine nagode.
Gaba ɗaya zuciyarta ta ji babu daɗi hakan ya sata saurin ɗago idanuwanta tana kallonsa cikin murya dake nuni da gajiya ko kasala tace "Yazeed why not mu je wasu iyaye su ɗaura mana aure tunda iyayena sun ƙi amincewa da kai?" Murmushi ya yi don dama wannan ita ce damar da yake jira ya ji ta ambata gashi kuwa ta ambata din. Domin ya ƙara gasganta kalaman nata sai ya ce " Are you sure?
"Very sure my Love muyi maganin tsofaffin nan nawa kawai sai dai suji an kaini gidanka.
"Ohhh my Baby!
Ya faɗa yana mai ƙara rungumo ta. Cike da zallar farin ciki yake shafa kumatunta yana faɗin "Tashi mu je akwai wani tsoho dana sani aikinsa kenan." Murmushin farin ciki tayi tace really? But yanzu I have to go back home saboda Baba kadai san halin wannan tsohon da rashin m. Dariya ya yi sosai yana cewa "Okay ki zama ready cikin satinnan komai zai ƙare zan mallaki abinda ake hana min a saukakke.
Ya ƙarashe magana yana kanne idonshi guda.
Harara ta balla masa kafin ta kada kanta sannan tayi hanyar ƙofar fita daga ɗakin har ta isa ƙofar ya kira sunanta gami da cewa "Zo karɓi wannan wayar hide it please kada wani ya gani ya ƙarbe da safe zan kiraki.
Murmushin tayi ta ƙara hugging ɗinsa tare da sumbatar kumatunsa hagu da dama sannan ta sauka ta fita daga gidan.

Mommy ce zaune tana kuka sosai gaba ɗaya ranta babu daɗi wannan ɗabi'a ta ɗiyarta ta rasa yadda za ta yi da ita. Umma Habiba ce ta ƙaraso inda take ta zauna kusa da ita cikin kwatar da murya ta shiga faɗin "Ɗan ALLAH Mummyn Salma ki daina yiwa yarinyar nan kuka ki ajiye maganar kishi da ke tsakaninmu amma wallahi ko ni a duk lokaci da nayi sallah sai na roƙawa Salma shiriyar Ubangiji, lamarinta ya huce tunanin duk wani mai hankali addu'a za ki ci-gaba da yi mata.
"Habiba na rasa yadda zan yi da Salma dama ALLAH zai kashemin ita na huta, ina tsoron yarinyar nan ta je ta yi abun kunya ki dubi mahaifinta kullum lafiyarsa cikin farmaki take saboda baƙin ciki abunda yarinyar nan ta ke yi, yanzu ma musa almajiri ya ce min ya ganta ta ta shiga gidan su gantalalle yaro nan Yazeed wallahi da ace mutumin kirki ne ba zan taɓa adawa da aurenta dashi ba tunda nima rufin asirina ne Amma umma Tabawa mai aiki tace min tayi aiki gidansu Yazeed yaya da ƙanwa ya haɗe ya yiwa ciki fa kuma ta tabbatar min ɗabi'arsa kenan yanzu idan ya yiwa salm....ya Abdulkarim yai sauri katse ta ta hanyar furta "Mummy Dan ALLAH kar ki yi mata baki ki yi shiru Dan ALLAH karki manta hakan ma jarabawa ce indai muna mata addu'a wata rana za ta shiryu kuma in-shaa-ALLAHU ALLAH ba zai ba wa Yazeed Ikon lallata Salma ba zan ƙara zuba idanuwana akanta. Umma Habiba da jikinta ya ƙara sanyi dan lamarin Salmar ita ma ya fara fin ƙarfinta dan haka sai ta rufe maganganun da cewa "ALLAH ka shiga lamarin yarinyar nan ka shirya mana ita.
"Ameen! suka faɗa a lokaci ɗaya sannan suka bar gurin kowanne zuciyarsa ba daɗi.

*WASHEGARI*

Wajajen la'asar Salma tana zaune a ɗakinta tana tunanin ta inda zata fara shirya kayanta dan tasan Yazeed Talba da gaggawa bata tunanin ƙarshen satinnan zai ƙare ba tare da su je an ɗaura musu aurennan ba, akwatinta ta ɗauko sannan ta buɗe closet ɗinta ta shiga fiddo da kayanta tana jerawa cikin akwati sai murmushi take yi burinta yana daff da cika dan ita gani take yi duk duniya babu mai ƙaunarta sama da Yazeed iyayenta kuwa maƙauniyar soyayya da take masa yasa mata jin sune maƙiyanta. Sallama mummy tayi tashigo tana faɗin "Ke sallama ubanki ne zai gyara miki kitchen ɗin?" Idanuwanta ta sauke akan kayan da Salma take haɗawa take ƙirjinta ya buga batasan lokaci ta shiga furta "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! me ki ke yi haka Ummul-Salma kayan menene wannan ina za ki tafi da wannan tuli kaya?" Cikin gunguni ƙasa-ƙasa tace "Ba kayan komai bani ba kawai dai nayi sha'awar haɗa kayana ne a akwati ko akwai matsala ne?"
Ta ƙarashe magana tana turo baki gaba.
Wani wawan mari Mummy ta kai mata cikin tuƙuƙi baƙi ciki tace "Ba dai guduwa za ki yi ba Salma da ɗan iskan yaro nan ba?" Wani mugun takaicine ya zo wa Salma cikin ɗaga murya ta hayyaƙo wa Mummy tana cewa"Na ce ku auramin shi kun ƙi wallahi akan Yazeed Talba babu abunda ba zan iya aikatawa ba, tunda ba za ku auramin...
Bata ƙarasa magana ba Mummy ta jawota ta shiga dukanta tana faɗin "Wallahi nayi nadamar haihuwarki Salma Salma kin zame min fitina me za a yi da haihuwar irinki? Duk wahalar da nayi dake wannan ce sakayyar da za ki yi min? Wani mugun duka da Mummy ke mata yasa sauran yaran gidan dasu umma shigowa ana kwatar salma yayin da Mummy cikin kuka take faɗin "Salma duk abunda ki ka yi mana mu iyayenki ALLAH ya yi miki linkinsa kin cuceni kinsa na zama uwar nunawa a duk inda na shiga ana faɗin na kasa ba ki nagartattaciyar tarbiyya.
Ta ƙarashe magana gami da sake rushewa da kuka mai ƙarfin gaske. Ya Abdulkarim shi ma kuka ya saka gani haka yasa gaba ɗaya yaran gida suma suka sa kuka da sauri Ya Abdulkarim ya juya ya fita dan wallahi zai iya kashe yarinyar nan idan ya ci-gaba da tsayuwa a ɗakin.
"Haba mummyn Salma Dan ALLAH ki bar maganganun nan akan yarinyar nan kada ki manta tasirin addu'ar mahaifiya akan 'ya'yanta Dan ALLAH ki dinga kai zuciyarki nesa nace mu bi abinan a hankali, ke Salma tashi mu je ɗakina Umma Habiba ta ƙarashe magana gami da ta ja hannunta suka tafi zuwa nata ɗakin. Gaba ɗaya haka gidan ya kasance shiru har dare mutane gidan suna cikin rashin walwala gashi Alhaji Umaru Sadauki ya yi tafiya sai dare ya dawo shiyasa ba wanda ya gayamasa abinda ya faru sun bari ne sai da safe su faɗa masa.
Kowannen su yayi bacci Salma kuma tana ɗakin Umma Habiba jira daman take yi tayi bacci ta salallabo tafita zuwa dakinta, da yake dare ya ja kuma a cikin duhu ake har ta shige ɗakin nata bata lura da Babanta na gefen ɗakinta ba yana ta sallolinsa dan nan yafi masa daɗin ibada da daddare wayartace tayi ringing babu shiri ta ɗauka tana faɗin "My love sai yanzu za ka kirani ko? Ba muji mai yace mata ba sai tasa dariya tace "my Yazeed kenan duk duniya ba wanda ya kai Salma ƙaunarka, ai in gayamaka tsohuwa ɗazu ta kusa kasheni don ta kamani ina faman haɗa kayana kai da ace Umma Habiba bata nan da shikenan wallahi kashe ni za ta yi nifa akanka naci uwar biyayya gare su wallahi Zeed a shirye nake Mummy ta kwashe min albarka akanka.
Ta ƙarashe magana tana dariya sai kace wani abin arziki ne ta faɗa.
Babane ya sallame sallarsa cikin tashin hankali dan ya tabbatar da cewa bai bawa Salma waya ba kuma bata amfani da ta iyayenta a ina ta samu waya a tsohon dare nan?" Magangun da ta keyi ne yasa shi ƙara shiga damuwa ƙara kasa kunnensa ya yi ya ci-gaba da sauraron abinda take faɗa Yazeed ya yi ƙasa da murya cikin kwarewa da yaudara ya ce "Babyn ki ciro breast ɗinki ki ɗaukar min shi hoto ki turomin ta whatsapp please baby kinsan dai ina sonki kuma ina mugun ƙaunar nonuwanki fiye da duk wata halitta ta jikinta na rantse da ALLAH My Salma duk ranar da na mallake ki sai na kwana ina shanye miki nonuwa.
Dariya ta ƙara kwashe da ita cikin muryar shaƙiya ci ta ce "Wai kana nufin nonuwana zan turo maka ta WhatsApp?
"Eh! Baby please don't say no har pant ɗinki ma ki cire ki dauƙar min kinsan bana gani kowacce mace a gabana bayan ke hatta da Mom bata gabana ke kaɗai nake gani My Salma, ki taimaka min kinga zan rage zafi kafin muyi aure.
Cikin jin daɗi furuncin shi tace "To Baby bari na ɗauka na turo maka, Baba baisan sanda ya shiga ɗakin ba tana ƙoƙari cire rigar jikinta Baba yana faɗuwa yana zuwa ya fizgo ta gami da sheƙe mata wuya
kwal ya bugata da bango wata mahaukaciyar ƙara tayi da yasa kowanne babba da yaro na gidan farkawa kafin su umma su ƙaraso tuni jini ya fara fita ta kan salma har ma ta suma. Mugun kukan da Baba yake yi ne kamar ƙaramin yaro ya ƙara ɗaga musu hankali Abdulkarim ne ya zo ya sunkuceta akayi asibiti da ita..

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now