*🫧 ZAMANIN MU A YAU🫧*
NA
JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO*PAID BOOk*
_Team Tagwaye Biyar Novel_
005
Yau gaba ɗaya hankalinta ya ƙarkata akan abunda malamin ajin yake koyarwa ɗaliban kalmar da taji na stop shine yasata kara zura kai tana sauraronsa yana faɗin "idan akace stop Aisha ana nufi ki tsaya A'isha, kunga kenan kalmar stop tsayawa ake nufi ko? Kungane?
Gaba ɗaya ɗaliban da zasu kai adadin hamsin zuwa sittin a cikin ajin suka ce "mun gane malam. Yar uwar Rahee ce ta kallota wato Ladi harara ta shiga zabgawa Rahee tana kada kanta alamun za ki sani, Tabbas tasan sharrin ladi yau in suka koma gida tashiga uku, amma zata san duk yadda za tayi tasiyar da awarar nan tanan ne kadai tasan zata samu sassauci murmushi ta kuma yi Tunda Rahee taji kalmar take fama maimaitawa tana faɗin "top top yau na ƙoyo kalmar turaci ta faɗa tare da saurin daukar awararta ta koma bakin inda masu tallah suke tsayawa dan taga alamun ana daf da tashi. Gefen mai sayar da masara ta samu ta zauna tana mai faɗin gaskiya turanci da daɗi. Mai masara ce ta dallah mata harara tana faɗin "Wai ke Rahee ba za ki daina laiƙasu ba ko? Wata rana in suka yi miki duka ke ki kaso in banda ba ki da hankali me za kiyi da wata boko ko? Malama mu nemi ƙudi muyi auren mu ta faɗa tana kara toro da ɗan ƙwalinta waje." Takaicin mai masara ne yasa Rahee saurin faɗin "Hefe ba ki da hankali karatun ne bakyaso? Yanzu ke Kinfi son yawan tallah da jahilci? Ni gaskiya inason karatun he baba ya samu kuɗi tukunna. "Ke Rahee kyaleni da maganar karatunnan he ki damu mutum da batun karatu ina dalili? Ni maganar da zanyi miki ma kina ƙaiwa Sha'aibu kayanki kuwa? In gayamiki jiyannan he da ya bani dubu ɗaya ya siye kayana.
Rahee ce ta zaro idanuwa tare da mamakin kuɗin da abokiyar sana'ar ta ta ambata sannan ta ƙara wangale baki tana faɗin. "In ce aiki ki kayi masa ya baki kuɗi masu yawa har haka?"
Dariya mai masara tayi tace "ke wallahi na daina wahalar tallah daga makarantar nan gurinsa nake zuwa ba ki ga ina zuwa zai siyarmin da masara ta duka
"Dan ALLAH ki kaini nima ya dinga siyarmin. "Ai ba za ki yarda da abunda zai yi miki ba. "Kamar yaya?"
Rahee ta faɗa tana mai neman ƙarin bayani gami da zazzaro idanuwa. "Dallah ce he ki yi ta ƙauyanci ke Rahee, zai ɗan tattaɓaki tuƙunna wannan ɗakin nasa shi zai kai ki fa, nasan ke har dubu biyu zai baki tunda kinga ke kina da diri ga ki da nonuwa masu girma kawai dai ƙazantarki ce matsala ba kowa zai iya taɓa ƙazamin jikinki ba. Rahee ce ta ja tsaki "mtsssss! tare da faɗin "ALLAH ya shiryeki, ALLAH kuma ya tsareni da iskanci komai talaucin mu ba zan iya bari ƙato wofi ya taɓa min jiki ba, ko aka gayamiki dan banyi makaranta ba bana tsoron ALLAH?
Shi kuma ɗan Sha'aibu in shaa ALLAHU sai asirinsa ya tonu.
"Dallah yimun shiru Rahee ni za ki gayawa magana sai kace ke bakyayi ko kina so ki wanke kanki ne?."Mtsssss! Rahee ta ja guntun tsaki tare da dauƙar awarar ta ta dora akanta, ta bar wuri tafiya ce take yi tana tafe tana waƙarta duk da irin yunwar da take ji haka ta ɗaure tana zagawa dan yau kam bata tsayawa a makaranta mai masara ta ɓata mata tarbiyar ta salan Babanta ya daina kulata, samun guri tayi ta shiga ƴar carafke jikin nan nata yayi datti sosai ga uban wari dake tashi a jikinta amma saboda yanayi na sabo ba taji komai ba, bayan wasu mintuna bacci ya kwasheta, tsawan mintuna 30 tana shan baccinta, "ke Raheenatu ke Raheenatu wacce kalar kwanciya ce haka cikin ƙasa sai kace ba mace ba dubi kayan jikinki zanin ma ya yayyage, duk maganganun da wata mata take yi Rahee tayi nisa a baccinta dan bata san ma tana yi ba. Matar ce tasa ka hannuwanta ta ɗaƙawa Rahee duka cikin firgita da tsoro tayi maza ta tashi har tana rungumar bokitin awararta.
"Ke Rahee uban me ki ke yi a haka dubeki fa kamar mahaukaciya kina macce kin fara zama budurwa ki ke saka kayan nan? Dubi uban dattin da ki kayi?.
"Lahh inna A'i yaushe ki ka zo Ƙauyen?"
"Ƙaniyarki tashi mu je gidan naku kamin na ɓata miki kin zama wata ballagaza dake.
Kunkuni Rahee ta fara yi sannan tabi inna A'i abaya har suka isa cikin gidansu da mata sunfi goma tsaye kowannen su sai uban surutu sukeyi anata zabgawa inna cinikin maganin matanta, inna A'i ce ta jiyo bata ga Rahee ba hakan ya sata komawa soro nan ta ganta rakuɓe a jikin ƙyauren ƙofar tana rarraba idanuwa.
"Ke Rahee sai yaushe za kiyi hankali ne? Dan ubanki ba haka nace ki shige mu je ba zaman menene kikeyi anan?"
"Inna A'i ban fa siyarwa da inna awarar ta ba yau ko sisi banyi ba so ki keyi ta kasheni.
Baki inna A'i ta saki tana sauraron Rahee kafin tace "Dallah shige mu je in taga dama ta ɗaurawa Shatu mana tallan sai ke marainiyar ALLAH.
Cikin tsoro Rahee tace "Dan ALLAH ki barni naje nayi tallah ko rabi nasiyar mata kada ta zaneni wallahi yanzu idan aka dakeni jikina he ya yi ta ciwo yana fidda jini. Ƙokarin fizgota inna A'i take yi amma ina tuni Rahee ta falfala da mugun gudu abunka da mai ƙaramin jiki tuni tabar bakin ƙyauren tayi cikin kasuwa, cikin sa'a kuwa tayi naira ashirin a hanya, barau dan gidan mai unguwa dake sonta ne yazo bakin bishiyar da take zaune da zuwansa yace "Yan matana! ya faɗa yana mai washe haƙora.
Turo baki da duk ya bushe tayi tace "he ka dinga tsoratani ko?"
"Kiyi haƙuri me yafaru yau baki siyar da awarar ba? Ko dai munyi ƙwantai ne?"
"ALLAH ya tsareni kwantai.
"To yanzu ta nawa ce wannan?"
Murmushi tayi da ya bayyana haƙoranta jajir dasu fusƙar nan duk tayi furu-furu
"Naira ɗari biyu.
"To yau dai banida kuɗi abani ta naira 50. Murmushi tayi gami da faɗin "Nagode sosai! sannan ta zuba masa daga nan kuma ta ɗauki bokitinta tayi gaba dan harga Allah tasan barau ba ajinta bani ba ko kalaman soyayyar da yake gayamata tasan yaudararta kawai ya keyi dan gidan mai unguwa fa "tabdijan! ta faɗa.
Cikin hukunci Ubangiji kamin azahar tayi ta yi cinikin naira 180 sauranta ta naira talatin dan haka sai kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Babanta inda yake faskare, tafiyace mai ɗan nisa tayi dan bata isa ba sai kusan bayan azahar, wani dattijo ne tunda ta hangoshi fara'ar fuskarta ta ƙara bayyana, rigar jikinsa takallah duk yadda take ganin mutuwar kayan jiķinta amma ina, yadin dake jikin mahaifin nata ya gaji da koɗewa ga shi duk ya yayyage, da ɗan saurinta ta ƙarasa tana isa kusa dashi, ALLAH sarki bacci wahala yake yi da alama faskaran itacen yake yi. Zamanta kusa dashi yasa ta sakin kuka dan tana tausayin mahaifin nata, shi kansa itacen ba jarinsa bane ba acikin na dubu ɗaya idan yayi dari biyu zuwa uku ake bashi, duk da ƙankantar shekarunta tasan mahaifinta yana cikin matsala da damuwa duk yadda zai fahimtar da inna yasan ba zata taɓa ganewa ba."Babana dan ALLAH kabar aikin itacen nan dubi hannunka yadda yayi.
ta faɗa tana mai share hawayenta.
Murmushi ya yi gami da faɗin "ƴar gidan Baba menene na kukan bana hanaki ba? Wata rana sai labari yanzu idan ban yi faskaren ba ta yaya zamu ci abinci kina ganin innarki bata ganin ƙoƙarina, so na keyi ma nasamu kudi kema nasa ki makaranta kamar yadda innarki ta saka Shatu, yau ma ba kiyi wanka ba ko Raheenatu ? Kin ji wani irin wari da ki ke yi kuwa?"
"ALLAH sarki Babana ALLAH ya ba ka kuɗin dan wallahi ina son makaranta yau ma top top aka koyawa ƴan makarantar.
Shiru ya yi zuciyarsa tana masa zafi, amma da yake dattijon kirki ne shi sai cewa ya yi in shaa ALLAHU sai kin gaji da bo koko yar gidan Babanta."
"Yanzu dai Baba kabar maganar wanka ga wannan awarar kaci nasan ba kaci abinci ba, In yaso sai nacewa inna kai ka siya za ka bata kuɗin daga baya.
Ba dan yaso ba ya ƙarbi awarar ya shiga ci, kai "Malam Audi! malam Audi! ina kuɗina ne naira ɗari da hamsin ace kusan satinka uku? Shiyasa kowa ya haƙura da ba ka rance wallahi. Babane yayi hanzarin tashi yana tarar abokin nasa dan baya son Rahee ta fahimta "Dan ALLAH ɗan birni kayi haƙuri zan ba ka dazarar na haɗa. Ƙokarin caƙumo wuyansa ɗan birni ya shiga yi yana mai faɗin "Ai wallahi-tallahi ka daina yaudarata tsohon banza.
Wani sabon hawaye ne ya zubowa Rahee kullin zaninta ta ƙwance naira ɗari da hamsin ta ɗauka sannan ta ɗaure naira talatin ɗin, cikin girmamawa tace "Baba ɗan birni gashi yanzun nan ya bani yace in kawo maka daman." Murmushi dan birni ya saki sannan yace "shine a
ka ke zolayata? Har kana so in nuna maka baƙin halina.?"
Wasu sabbin hawaye ke ƙoƙarin wankewa Baba fuska amma yayi saurin haɗiye su yana jin ƙaunar ɗiyar tashi har cikin jinin jikinsa. Gaban Rahee kawai ke duka dan tasan yau sai dai wata ba ita ba a gurin inna.
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romancewannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...