15

155 6 0
                                    

015

*LAST FREE PAGE*

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

*LAST FREE PAGE*

Sosai ƙalaman hajiya nafisa yabawa maryama mamaki? Cike da wani mamakin da yabayyana afusƙarta tace " Taɓewar tawa bataƙai nan ba wato ke rashin tsoron Allahn naki haryaƙai haka?" Saurin miƙewa tayi tsaye tana faɗin " Allah yatsareni taɓewa, ko dan ƙinga nayi zurfi a boko shine kike tunanin banda ilimin addini? Menene haɗin shawarar ƙara aure da wannan banzar maganar taki? Ke daga yau bakya kara ganina agidanki ƙada wataran akifa dani ƙekuma Allah yaganar dake." Saurin riƙo hannunta hajiya nafisa tayi tace " ke kawata wasafa nake miki, amma kin ɗauki abun da zafi." Fizge hannunta maryama tayi tare da nufar hanyar waje, batare da taƙara sauraron hajiya nafisa daketa magana ba. Ko da hajiya nafisa taga tashiga motarta wayarta ta lalubo takira wata numba tana faɗin " Hajiya, maryama fa duk yadda muke tunanin ta wallahi bahaka take ba, kinga maganar boka ma haka tayimin tas wai data ɓata ƙudinta gurin ƙato gwara ta siya supplement, yanzu ma bakiga abunda tayimin ba." Daga cik'in wayar ce akace ƙada kidamu nafisa kinsan tahaka ne ƙawai zan iya ɓata mata suna agurin mijinta,dole kikara janta jikinki dan bazamu iya yimata illah ba sai ta hanyarki ke kadai tunda daƙe ƙadai tayarda." " in shaa Allahu gobe zan taka naje gidan nata.

Tunda maryama ta ɗakko hanya zuciyarta ke ƙara mata wani radadi da zafi, samun gurin parking tayi taci kukanta sosai, bata taba tunanin tanayiwa mijinta irin wannan jarabben soyayyar ba.

Kyakyawan matashi da bazai gaza shekara Ashirin da daya ko biyu ba, yanayin girman jik'insa sai kayi tunanin cikakken namijine, sauƙarsa kenan daga airport tunda yafito yake fara'a yana hangen wanda sukazo ɗaukansa, mahaifinda yagano daga can gefe yana amsa waya, saurin karasawa yayi kusa dashi sai Abah yaji anrugumeshi ana dariya. Cikin sanyin rai irin nasa da nuna tsantsan farinciki yaƙara rungume tilon dan nasa, " MashaaAllah maleek haka kakara komawa." Runsunawa yayi yana murmushi " Nakoma sak dadyna ba, amma dady baƙace Dr maleek ba." Dariya Abah yayi yana ƙama hannunsa har suka nufi motarsu, farincikin da abah yakeyi bazai taba misaltuwa ba dan gabadaya hannun maleek yana cikin nasa jiyakeyi kamar zai ƙara komawa." Suna nufar gida basu tsaya ko'ina ba sai bangaren dattijo, sallamar da maleek yayi itace tasaka zuciyar mama motsi tare da fargaba, daga idonta da zatayi sukayi ido biyu da maleek, ƙallonta yakarayi yanason tuna wacece ita, Abah ne yayi saurin fad'in " maleek ga maman ismaila and ga dattijo." Dattijo ne yasaki baki yana ƙallon maleek dake ƙarasowa kusa dashi." Babana wannan yaron ai photo copy dinka ne." Mamace tayi caraf tace " Amma girman jikin nasa yayi ai alhaji sai kace wani dan shekara 30 yaron da baifi 20 ba." " MashaaAllahu dan balaraben jikana yagigita amaryata to badai auren zamuyi dake ba." Wani baƙin ciki ne yataso mata acikin ranta, maleek na ƙarasawa ya rungume dattijo da hausarsa wacce bata fita yashiga gaisheshi." " Kaje kayi zamanka maleek sai kace bakada dangi anan, yanzu jibi B hausarka idan mutum ba nautsuwa yayi ya saurareka ba to tabbas bai gane me kake cewa." Wani kallo maleek yayiwa mama baicemata komai ba. Haushi d takaici ne yaƙara kamata, dattijo ne suka gaisasanna yace masa yashiga ciki yhuta tuƙunna. Sauyin dayagani acik'in gidan shiyasa bin ƙoina na gidan da ƙallo, part dinsa yaga anata gyra dan haka bai nufi can ba sai yayi shigewarsa bangaren mahaifiyarsa, tunda yashiga part dinsa masu aiki ne ke kai kawo, Nan suka shiga gaisheshi cik'in girmammawa da hannu yadinga binsu a hanƙali ya ajiye jaƙarsa yahaura hasa, directly dak'in maryama ya tsaya, knocking yashiga yi amma babu wanda ya amsa masa dan haka ya tura ƙofar a hank'ali gabansa ne ya wadi ganin mahaifiyarsa tana ta faman kuka, da dan sauri yaƙarasa ya zauna kusa da'ita hannunta ya riko yace " mom? Menene? Daga dawowata ? Innalilahi wainna illahirrajiun." Rungumeshi tayi tacigaba da kuka, gabadaya hankalinsa tashi yayi ganinta ahaka. Cik'in da shashiyar muryarta tace " maleek Abah bayasona Abah wulakantani zaiyi, Anrabani da mijina maleek ansaka abah yaƙaro aure." Yasan hakan sai faru daman ɓata ransa yayi yace " Haba mom daga dawowata ace a yanayin da zanganki kenan kinaso zuciyata ta buga ne? Menene cik'in auren? Kinmanta shekarunki nawa da aure kuma kowaccce dadyna zai aura ai bazata taba ƙaiki ba. " Hannunsa yasaka ya share mata hawayen sannan yace " Kidaina kuka danAllah." " To naji zan daina kaje kayi masa magana yafasa auren dan nasan yafi kowa jin maganarka kuma akanka babu abunda bazai fasa ba." " is okay, zan masa magana kema kidaina kuka."

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now