*ZAMANIN MU A YAU*
NAJEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO*PAID BOOk*
_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________*008*
Alhaji Ado Hukuma yana kammala sallar isha'i wacce shi kaɗai ya sallaci abarsa, ga masallaci a unguwar amma baya fita sallah balle ya sami ladar jam'i. Wannan mummunar ɗabi'a tashi tana ɗaya daga cikin abinda yake baƙantawa iyalinsa rai, sai dai basu da yanda za su yi. Tsakar gida ya fito fuskarsa a haɗe cikin masifa da bala'i ya dinga kwaɗa wa matan gidan kira, hatta da maƙota su na jiyo sautin muryarsa gashi da ƙatuwar murya tubarakallah! Kamar yana amfani da microphone "Hauwa! Rabi'ah! Hauwa! Rabi'ah wai kuna ina ne shegun mata sai zaman ɗaki sai kace muminai alhali ƙattan munafukai ne ku fito yanzu nan ko na shigo da kaina anan za a tantance wanda yafi rashin mutunci tsakani ni da ku.
Da sauri kowacce ta fito nesa dashi suka tsaya da ka kalli fuskokin su za ka ga irin tsoratar da suka yi, yayin da 'ya'yan su suka rakuɓe a jikin ƙofa su na kallonshi. 'Yan matan gidan kuma ta window suka leƙo kowane ranshi ba daɗi, domin sun sa idan ya fara tijara har maƙota sai sun jiyo shi.
"Ke Hauwa zo nan tsohuwar munafukar wato ke ce babbar banza mai kawo shawara Rabi'ah ta tunƙare ni da zance kuɗin makarantar 'ya'yanku ko?
"Alhaji ba sharawa ta ce ni kaɗai ba mu duka muka ga dacewar ka taimaka wa yara nan kasancewar Rabi'ah ce da girki shiyasa ta ce za ta faɗa maka, Alhaji yara nan hakkinsu a wuyanka ya rataya ba ga na mu ba amma a haka muke ƙoƙari gani mun inganta rayuwarsu. Alhaji kana dashi ba wai don ba ka da ba balle mu yi maka uzuri rashi gaba ɗaya ka danne mana hakki babu ci babu sutura kirki yanzu duk wanda ya ganmu a cikin wannan ƙaton zai zaci duk duniya tana nan mun tara alhali baƙar wahala da muke sha bata faɗuwa sai dai kawai abarwa ALLAH.
Yanda Hauwa take magana cikin tausasa kalamai sai za ka yi zato karatu ne take bita, domin cike da ladabi da biyayya take masa magana. Amma duk da haka gani yake yi tayi mugun rena shi.
Saboda haka dui maganganu da take faɗa tsaye kawai ya yi yana kallonta gami da murza gashin bakinsa, nazari yake yi ɗaya bayan ɗaya akan duk wata kalma da ta fito bakin Hauwa, domin yana zargin waɗannan maganganu da suke fitowa daga bakinta ba su yi kama da na fatar bakinta ba. Akwai wata tsohuwar munafuka dake shigo masa gida tana hurewa matansa kunne, lallai dole ya yi sauri yiwa tufka hanci tun da suka fara da haka baisan abinda gaba za ta haifar ba.
"Hauwa yaushe reni ya shiga tsakaninmu har da za ki tsaya a gabana kina kallona ido cikin ido kina zaro min maganganu iya son ranki wato kin ga na daina duka ko? To ku sani har gobe ba ku wuce duka a wurina ba idan har haka ta sake faruwa wallahi dukkan ku sai jikinku ya gayamuku, ina nan Ado Hukuma ban canza ba duk wacce ta gaji da zama dani ga hanya nan ta tafi gidan ubanta cikinku ba wacce na yiwa dabaibaye ballantana ta kasa tafiya, gida dai mallaki na ne ba da kuɗi uban mutum na gina sa ba.
Haka ya ci-gaba da ƙare musu zagin ƙare dangi tun abin ƙarfe 8 sai ƙarfe 10 ya juya ya koma ɓangaren sa yana mita dama ALLAH ya yi shi mutum mai azababben faɗa da mita tsiya, in dinga mita kamar zai ci babu.
"Mtsssss! Na rasa wacce tsiya ce a gidanan da Abba idan ya tashi faɗa sa yake tinƙaho da abar masa gidansa?"
"Hmmm! Kema dai kya faɗa Zakiyya ni wallahi duk ranar da haukar sa ya motsa ya ce na bar masa gida ko second ɗaya ba zan ƙara a gidanan ba. Da zama wannan gidan nashi ba gara zama gidan karuwai ko ba komai kana da 'yanci.
Rufaida ta ƙarashe magana gami da yi ƙwafa kuma har ga ALLAH abinda ta faɗa har cikin zuciyata haka yake.
"Haba! Yaya Rufaida ya za ki dinga danganta gidan mahaifinki da gidan karuwai?"
Hafsah ta faɗa cikin sanyi muryarta domin ita mutum ce da ALLAH ya yiwa sanyi hali bata da hayaniya ko kaɗan idan ma ka ji Hafsah tana magana tana cikin 'yan uwanta ne.
Cikin masifa Rufaida ta hayyaƙo mata tana faɗin "Na faɗa gara gidan karuwai sau dubu da wannan gidan da babu komai a cikinsa sai tarin baƙin ciki da takaici.
"Amma Hafsah komai Abba ya zama mahaifinmu ne fa?"
"To sai me dan yana mahaifinmu duk cikinmu akwai wanda yasan daɗin sa ko amfaninsa wallahi gara a haife ka shege da a ce Ado Hukuma ne ya haifeka.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Yaya Zakiyya hadda ke gaskiya ku daina ba daidai bane ku dinga faɗar mummunan maganganu akan Abba...
"Ke dallah! Rufe mana baki.
Rufaida ce ta daka mata tsawa kafin ta ɗora da cewa "Halan kowa irin ki ne marar zuciya mutumin nan kina kallo yadda yake zaluntar mu da iyayen mu sannan ki hana mu faɗar zalunci da yake mana so kike idan ba mu faɗa ba bakin cikinsa ya kashe mu kou?
"Amma Yaya Rufaida...
"Wallahi-azim Hafsah idan ba ki yi mana shiru ba duk abinda nai miki ke ki ka janyo.
Cewar Rufaida tana zazzare wa Hafsah idanuwa dole Hafsah tai shiru ta zubawa sarautar ALLAH idanu.
______________
Kaitsaye Abah ɓangaren dattijo ya nufa cike da ladabi ya yi sallama, dattijo dake kishigiɗe ya amsa masa yana mai tashi zaune wata irin fara'a da annashuwar gani Ahmad Shema ta bayyana ƙarara akan fuskar Dattijo duk a cikin 'ya'yanshi Abah shi ne mafi soyuwa a zuciyarsa, domin yana gudun zuciyarsa tun shi na yaro bai taɓa saɓawa umarnin sa ba wannan yana cikin kwarara dalillai da yasa ƙaunar da yake masa ta fita dabam.
"Barka da hutawa Alhaji!
"Barka! Ahmadu na ashe kana gida ba ka fita ba?"
"En! Alhaji ban fita ba na tsaya haɗa documents ɗin dukiyar ka da take guri na.
Wannan magana ta Abah ba ƙaramin haifar wa da dattijo faɗuwar gaba tayi ba domin yasan watan lalacewar dukiyarsa ne ya tsaya, sai dai ba shi da yarda zai yi bayaso a wannan karo ya taƙurawa Abah kamar yadda yai masa a shekaru baya, yasa shi karɓa ragamar dukiyarsa sai gashi kwatsam! Wannan al'amari ya kunno kai yana da yakinin da cewa 'yan uwan Abah sun shigo da wannan maganar ne don baƙin ciki da hassadar ci-gaban da ya kawo masa cikin dukiyar sa.
"Alhaji ka yi shiru ba ka ce komai ba?
Abah ya faɗa gami da katse wa dattijo duniyar tunani da ya lula.
"Hmmm! Ba komai Ahmadu kawai ina tunani a kira dukka 'yan uwanka ayi komai a gabansu, domin su shaida ka dawo min da takardun duka dukiya ta da ke gurinka. Saboda yanayi na rayuwa gara su shaida.
"Tohm! Alhaji bara na kira su.
Abah ya yi magana tare da fiddo wayarshi ya shiga kiransu sai gashi sun bayyana a falon cikin abinda bai fi mintuna biyar ba. Dama su na gidan ba wanda ya fita muradinsu su ga sun karɓe ragamar dukiyar ta dawo gunsu, kowanne su ya nemi guri ya zauna fuskokinsu ɗauke da fara'a, sai da Abah ya ƙare musu kallo kafin ya shiga fito da documents ɗin ɗaya bayan ɗaya yana bayani akai. Har ya kammala kana ya sake mayar da kowanne cikin file sannan ya miƙawa dattijo lokaci da dattijo ya miƙa hannunshi ya ƙarbi takardun wani irin ƙunci da takaici ne suka lulluɓe shi har sai yaushe kan iyalinsa zai haɗu duk iya ƙoƙarinsa na gani sun zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya abin ya ci tura, dukka burinsa na cimma manufar shi ya ta'allaka ta ne akan Abah shi ma ya kasa shiyasa a yau ya fitar da cikar buri nan nashi, abu ɗaya ya rage masa ya zuba musu ido ya ga yadda za ta kaya a tsakaninsu dama masu iya magana sun ce ƙarshen alawa ƙasa.
Abah ya miƙe haɗe da yiwa dattijo sallama ya fito zuwa ɓangaren Hajiya Fulani saboda yasan ita ma tana can hankalinta tashe.
Yanda su Isma'il suka ga Abah ya fita da walwala akan fuskar sa babu wani alamar yana cikin ƙunci ko damuwa, hakan ba ƙaramin ƙona musu rai ya yi ba. Su fa a halin yanzu babu abinda suke buƙata irin su ga sun kawo ƙarshen Abah, wato karɓi dukiyar ubansu da suka yi bai sa shi ya girgiza ba to tabbas akwai abinda ya taka, saboda haka dole su sake sabon shiri, rai ɓace suka baro ɓangaren Dattijo suka yo na Mama amarya wacce ke ɗora su akan mummunar turba.
"Assalamu alaikum!
Abah ya faɗa sa'ili da ya shigo ƙaramin falon Hajiya wanda ta fi zama a cikinsa "Wa'alaikum Salaam Abah barka da shigowa!
Batoul ce ta amsa mishi wacce take zaune gaban Hajiya tana mata massage ɗin ƙafafuwanta, a kwanaki nan sun matsa mata da ciwo ɗaurewa kawai take yi a dalili halin damuwar da take ciki domin gani take yi shikenan kariyar arziki ta zo wa Abah.
"Yawwa Batoul sannu da ƙoƙari. Hajiya ya kamata gobe ki shirya mu tafi asibiti a duba ki, zama da ciwo a gida babu daɗi.
Ya ƙarashe magana tare da zaunawa kusa da ita Hajiya ta kalli Batoul fuskar nan ta ta babu walwala ko kaɗan ta ce "Fati shiga ciki zan yi magana da yayanki.
"Tohm!
Batoul ta faɗa haɗe da bari falo Hajiya ta dawo da natsuwata guri Abah cikin sanyi murya ta ce "Abah ina cikin matuƙar damuwa dangane da hali da za ka shiga banso ka yi sauri amincewa da buƙatar 'yan uwanka ba yanzu idan ka fita daga dukiyar mahaifinki ta ya za ka ci-gaba da gudanar da naka kasuwanci?
"Hajiya ki kwantar da hankali ki ci-gaba da yi min addu'a in-sha-Allahu wannan al'amari alkhairi zai zame min.
Ajiyar zuciya Hajiya tayi kafin ta ce "shikenan ALLAH ya yi jagoranci na alkhairi.
"Amin thumma Amin!
Sai kuma magana ta gaba dangane da shaiɗaniya matarka tana daff da ta kaini bango kodai ka ɗauki mataki ko kuma domin ni wanda zan ɗauka daga da kai har ita ba zai muku daɗi ba.
"Hajiya in-sha-ALLAHU komai zai daidaita domin na yanke shawara nan ba da daɗewa ba zan ƙara aure.
Wani irin murmushi Hajiya ta saki ranta fari tass! Kafin ta ce "A ina ka sami mata ne domin banaso ka sake zaɓen tumun dare?"
"Hajiya ban fara nema ba ina dai duddubawa ne banaso nasa gaggawa gudun kada na koma gidan jiya.
"Haka ne gaskiya nima na fiso ka tsaya ka tantance saboda matan nan na zamani ba kirki ya wadace su ba.
Murmushi Abah ya yi domin yasan abinda Hajiya ta faɗa gaskiya ne dan ga Maryama nan ta nuna masa hali yau.
Lokaci da labari ya riske madam Maryama Abah ya mayarwa da dattijo takardun dukiyarshi, ba ƙaramin tashin hankali ta shiga gaba ɗaya ta tayar da hankalinta har dasu koke-koke kasa tanka mata Abah ya yi sai kawai ya tashi yai tafiyarsa gani haka ta rarumi jakka da makulli mota sai gidan Hajiya Nafisa.*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️
GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA
GUDA BIYAR 1500.GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA ƊAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
YOU ARE READING
ZAMANIN MU A YAU
Romansawannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa...