💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 9
Hannun ta da ta ke miqo min na bi da kallo, da sauri na riqe plate din da ta miqo min,idanun ta na qare min kallo fuskar ta d'auke da murmushi, nima murmushin na mayar mata ta ce,
"Ina kwana amarya?"
"Lafiya qlou alhamdulillah,"
"Masha Allahu, ga wannan ba yawa ku tab'a,"
"Thank you so much, this is more than enough, thank you"
"Ba komai,"
Juyawa ta yi zata koma d'akin ta, na bi bayan ta da kallo, Maimuna mace me mai jiki mai kyau masha Allah, bata da tsayi sannan bata da qiba, mazaunan da take da shi ne suka qarawa surar ta kyau, d'aki na na koma riqe da plate d'in a hannu na, bud'e wa na yi sai na ga indomie ce da kwai da dankalin turawa a gefe.
Ajiye wa na yi a qasa na masa bismillah akan ya sakko mu ci dan ni bana wasa da ciki na musamman in na ga abinda nake so, halin da nake ciki be sani jin ba zan ci abincin ba, kallon plate d'in Yah Maheer ya yi sannan ya ce,
"Ki ci kawai zan ci cincin da dubulan kar ki damu,"
Qoqarin tilasta masa nake ya ci sai ya kalle ni ya ce,
"Kar ki damu young lady i am not hungry, zan fita anjima sai in kawo maki kayan miya ki yi mana girkin rana, tinda kin ga ko mutanen kano ma basu tafi ba zasu sake dawowa, be kamata ace su zo ba abinci ba ko?"
"Hakane, Allah ya kaimu,"
Loma d'aya na kai baki na ina taunawa, dad'in abincin ya sanya ni lumshe ido, a duniya ina masifar son duk.wani abinci da aka sanya wa farin maggi shine dalilin da ya sa yana wahala in ci abincin da aka sanya wa farin maggi ban gane ba,mu gidan mu ba a cin farin maggi,dan haka nake matuqar qaunar cin shi, lokuta da dama abinci ko ba dad'i indai an saka farin maggi bana jin haushin cin shi ko waye ya dafa kuwa.
Hamdala na yi a qasan raina da Yah Maheer be ci ba, haka kawai na zo na yi girki ya ji be kai wannan dad'i ba?
Ina gama ci na miqe na tattare komai na gyara na share, sannan na kai masa ruwa a buta waje saboda zai yi sallar dhuha (walaha) ya na fita na dakko bedsheet d'ina da ya yaye a jiyan na bud'e qofa kamar mara gaskiya ina leqe, na shige kitchen d'ina na kama inda duk na ga be min ba na wanke, na yi masa muguwar matsa na yarfe, sannan na koma cikin d'akin da sauri na sake maida zanin gadon, ko da ya shigo ya ga zanin gadon har zai yi magana sai ya yi shiru ya na ta kallon shi, ni kuma na juya ina gyaran wardrobe na qarya dan komai a gyare yake, ban juyo ba se da na ji ya tada sallah sannan na yi wufff na bar d'akin na koma parlour na kwanta a kujera ta man rest da nake mugun son irin ta, se gashi an yi min ba tare da an san ma zab'i na ba,wannan karon se na ji bata burge ni ba wanda da a da ne na gan ta aka ce wannan taki ce ba qaramin tsallen murna zan yi ba da farin ciki.
Numfashi nake ta fitarwa saboda sabon zazzab'in da ya ke son sake rufe ni, ina kwance na ji sallamar Yah Maheer ya fito cikin shirin fita, ya ce min bari ya je ya dawo, in 'yan kano sun zo na sanar da shi ya dawo su yi sallama zai je ya samu Yaya Babba a samo motar da za su koma har kano a cikin ta, na ce masa to.
Qasan raina kuwa har na gama yanke hukuncin binsu in koma gidan mu na fasa zaman anan ni,bani da lafiya ba zan zauna ba, ni dai kawai kome za a yi sai an koma da ni a wannan ranar.
Ko minti biyar be yi ba da fita sai ga 'yan uwa na sun zo inda daga nan ba inda za suje za a wuce da su kano, cikin murna na je na tarbe su ina ta farin ciki, na shiga d'aki kamar wadda zata d'akko wani abu, na d'auki akwati na madaidaici da aka d'ora a saman wardrobe na zuba kaya na a ciki sannan na zuge, na ajiye a gefe, na dauki ledar kazar da ban ci ba jiya da sauran lemo na fita da shi,sannan na koma na deb'i kayan gara da yawa na sake fita da shi, Goggonaye na ne wato qannen babana ne su uku suka zo daga baya kowaccen su ta ci kwalliya, Goggo Bilki, Aunty Jummai, Aunty Ameenah (matar qanin babana)da Aunty Iyannan, can kitchen d'ina kuma Yayar mu ce da sauran qannen babana su Shafa, ina zaune wajen su Yayar mu ta ce,
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....